Share this page
2 / 5
dan iskan mutum ne kana duba agogon ka kuwa?kasan ynxu tara da rabi kai fa kace tara daidai ba African tym shine ynxu dan iya shege daga dauko mota sai miji ka shiru kama kashe wayoyi,to ka samemu a wajen dinner domin har Amarya tana gun,yayanmu yace ni ake jira kenan yace eh mana kai kadai muke jira Amarya bata shiga gurin ba gata nan a mota sai ka iso ku shiga tare,gani nan yace sannan ya kashe ya ja mota muka tafi,ya dubeni kece mutum ta farko da ta soma shiga motar nan, naso Mimi ta soma shiga sai gashi kin mata shigar sauri kin shige mata mota sannan hotonki shine na farkon zama ajiya cikin aljihun motar kinsan ko a kannena kina da babban matsayin da kannena basu taka ba, nayi murmushi sannan nace nagode,muka isa gurin ya ajiye motar ya fito yana neman Nasir a waya can ya sameshi Nas na iso kuna daidai ina ne,yace gamu na bayanka kai baka ganmu ba,ya dubeni to fito Hajiya,na fito daidai sanda Anty mimi ta fito daga motar Nasir muka dubi juna ni da ita, shadda galila tasa dark green shima yaynmu ita yasa ankon kenan sukayi tayi kyau na fitar hankali ta sa sarka kirar dubai ga ashoben da aka sa mata a kanta ya dauru gashi har kan kafada duk sai naji na raina kaina,ganin ta daure fuska kuma tayi fushi hatta Nasir na kula yayi mamakin ganinmu tare,shi kam gogan ko a jikinshi ya isa gurinta madam kin jirani ko?sorry zo muje ana jiranmu ya kama hannunta muka bisu ni da Nasir sauran abokan ango sun taryi Amarya da Ango,wuri yayi wuri kowanne teburi mutum hudu mata biyu maza biyu,Amarya da Ango su biyu ne a gunsu mu kuma mu uku ne ni sai Mami sai Nasir,can an soma ciye ciye sai ga Adams bansan ta inda ya fito ba sai ganinshi nayi ya dubeni,yar kyakkyawa ina kika shiga ne yau duk banganki ba?kafin nayi magana ya juyo gun Nasir Assalamu alaikum abokina ai min afuwa 'yar kyakkyawa ta tsone min ido bana ganin kowa sai ita yace to ai shi kenan tunda ka ganta ynxu sai mu gaisa waalaikassalam,mu kayi dariya sannan ya zauna bakici komai ba yar gidana ya miko min cinyar kaza saitin bakina ci wannan mana na kauda kaina sannan nace a'a Adam bana cin komai juice zansha,yace sha mana ko na danji sanyi kinga Nasir yasa yar gidanshi a gaba sai ciyar da ita yake ba ruwanshi dake,Mami tayi dariya tace to tunda ynxu kaxo ai sai ka bata yace to ba gashi taki ci ba na fa dade ina kallonki naga shigowarki tare da Maska da Amarya na dubi gun yayanmu ga mamakina duk hankalinshi na gurin mu ya cika yayi fam tamkar ya fashe Adams ma ya dubeshi yace yar gidana kin ga yanda Maska ke faman hararata?nace to ya maka kashedi kaki ji ba?Adam kana son bata ma kanka lokaci ne kawai yardar yayanmu shine tawa,Adams ya dubi Nasir yace Nasir yi mana sharia,Nasir yace ina jinku,naga yar kyakkyawa ina so ina ruwan yaynsu,Nasir ya nuna mami yace baga yar gidana ba da muka shirya kanmu dole ya barmu,Adams yace to shi ne ta kasa ganewa tabbas in kin yarda na san halin Maska in har yace yes baya yarda yace no kin gane?so in har da gaske kike sona zan aureki kuma zakiji dadi sosai yanda nake jinki a raina, ko! na dubeshi,yace ba sai kin sha wahala wajen zuwa gurin malami ba zaki mallakeni son ranki,Allah sai yanda kikayi dani na rantse miki,na soma dariya shima yana dariya mami suna ta hirar su suma yace a makaranta wane matsayi kike son ki taka? Masters ko Degree ko Professor kikeson zama?zan barki da karfina da Aljihuna burina dai ki aureni ki haifamani yara masu kama da ke har da wannan dan dimple din naki, ya kai hannu zai taba min kumatu na goce ina dariya,sai yaynmu na gani akaina sai huci yake yace tashi a kaiki gida sha daya yayi ,nace yaynmu ka bari a tashi mana mama tasan wannan kuma zan kula da kaina......,ya katse ni tashi ko na mareki,tsoro ya kamani na soma kyarma adams yace Maska ya zaka ruda tane haba.....shima ya katse shi please Malam yi min shiru kajiko,na nuna Mami ga Mami ma nan yace ni na kawota?wanda ya kawo ta shi zai maidata na mike ya dafo min baya har gurin motoci,shiga nan ki jirani tunda ke bakya jin magana,kin je kin saki baki kina faman yi ma Adams dariya zanyi purnish dinki,ya rufe motar da karfi ya tafi.haka na zauna shiru can da na gaji ga wuri yayi shiru sai sautin kidan can gurin dinner kawai sai na kira wayar mami nace wai yayanmu fa?tace gashi can wurin Amaryar shi suna zaune suna hira nace to na kashe wayar duk haushi ya isheni nace wato shi yana can yana hira da matarshi ni kuma ya hana ni neman miji ba wani jiranshi da zanyi tfy ta zanyi abuna wato ga mai gadi! na soma kici kicin bude kofa abin haushi sai na kasa hala kulleni da key ne in ba haka ba na jijjiga murfin ko motsi baiyi ba na kari masifa ta nakoma na zauna na hada kai da cinya na matse nayi shiru,har misalin sha biyu da rabi ni lokacin ma barci ya soma dauka,ta ban ankara ba naji an bude motar an shigo dan ma baccin nawa a dar dar na keyinshi kun sanni da shegen tsoro sai na kware baki zan tsala ihu sai naji an rufe min baki gami da cewa shishit!,ya kunna wutar motar duk da naga yaynmu ne har ynxu jikina bai daina bari ba kin cika tsoro Iman saidai kin fi burgeni in kina cikin tsoro idanuwanki su kan birgeni ya kai yatsansa saman idona na lumshe ido jikina yana wani irin tsuma saboda yanda yake sosa min saman idona ya janye yatsansa sannan ya daure fuska ya dubeni yauwa dazu me Adams ya ce miki kike dariya?nace ba komai yace karya kike yi zan gaya maki abinda ba ki sani ba shi kike so ba kuma ba zaki aure shi ba,kafin ya rufe baki wayata ta soma ringin shi ya rigani daukan wayar yana duban sunan sai yaga ashe mama ce sai ya bani na karba gabana yana faduwa,Iman yayi maki kyau kinji ko,nace dan Allah mama ki yi hakuri yanxu zamu dawo yanzun nan fa aka tashi tace bana ga mami ta shigo ba ynxu nace to ai ni yaynmu ne yace tunda shi ya kawo ni zai maidoni ya min magana a hankali yace kice mata kuma na tsaya sallama da mutane ne,tace to kiyi sauri sha biyu ta wuce banda ma bana dakin kika fita da babu inda zakije ta kashe wayar,na dube shi yayanmu ka kaini gida ni mama ke jira dan na san itace da girki zata sashen Alhj shi yasa yayi wata yar dariya to bari mu tafi kar Alhj na yayi ta jiran mamanki gashi kuma na tsare ki anan yana magana da wata fassara ne na kula sai na kauda kaina gefe,ya tada mota yace yauma gidanku zan kwana ance wai sai gobe zanje gidana suna son yi mata budan kai gsky sun bani haushi menene kuma budan kai?nace nima ban sani ba a raina nace me ya dameni da zaka dameni dube shi kawai, wayarshi ta soma ringin daidai sanda muka tsaya a harabar gidanmu zan bude na fita naji ya jawoni ba tare da ya min magana ba ya dauki wayar na ji yace Alhj Iman gata nan na kawo ta kome Alhj yace mashi sai yace to ynzu zata shigo,ki shiga Alhj na jiran matarshi nima zan shiga daki ne na kira tawa a waya dan kece kika hana na maidata gida sai dai Nasir ne ya kaita,cikin mamaki nace ni?da yaushe nace?yace au baki ma san san da kikace ba ko?to shi kenan sai da safe ya bude min na fita ina dubanshi koda yaushe na ce kar ya kai matarshi oho?yazo ya min sharri kawai. Washegari budar kai da safe nice nayi musu abincin breakfast musa dryva ya kai musu gidan Nasir,da rana ana tafiya gidan Amarya ni kam ban fara ba don nasan magana zai zama kai na gurin Amarya ko ince tamkar naje neman fada,da daddare muna zaune a dakin Amira ni da mami,nan mami ta sameni gidansu Amirar mami na bamu lbr tsaruwar gidan,nace dama shi yaynmu ai dan gayu ne sannan ya saba da rayuwar turawa kinga kuma dole ne ya tsara gida na yan gayu,mami tace gashi kuma da kudin ba,Amira ta dubi mami dama akwai zancen da zamuyi dake,nan ta kwashe maganar son yaynmu da halin da nake ciki ta gaya ma mami,mami ta cigaba da mamaki dama yaynmu kike so Iman?gabana na faduwa hawaye na zubo min wllh mami kinji halin da nake ciki kenan,tayi shiru dan lokacin sannan tace to sai dai muyi ta addu'a amma Haj Yaya da Haj Laure basu da kyau in ma kin shiga gidan ba zasu bari ki samu kwanciyar hankali ba sannan shi kanshi yaynmu a irin ra'ayinshi baya son karamar yarinya yafi son babba nace na sani Amira ta ce ni kam sai naga kamr sonta yake yi nace ke ba wani so jiya kinji yadda yake min zancen matar shi dan haushi ni ko kula shi banyi ba. Mun tsaida shawara akan cewa zamu tsananta addu'a kawai Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 Amira ta rakomu har gida dan zata karbi littafinta a hannuna dai dai dakin yayanmu abokanshi ne sun sha kwalliya sai kamshi sukeyi mami ta dubeni yau za'a kai angonki gidan amarya na dubi wajen sannan nace to ni ina ruwana ,dai dai nan Adams ya fito shima sanye da waganbari blue ammy sky yace Iman na juyo ina duban shi amma gurin na tsaya,yazo yau duk bangankiba yar gidana ina kika shiga ne?ina nan banje ko ina ba na fada, su mami suka gaisheshi yace mami ko?mami tace eh yace kefa?ya nuna Amira mami tace Amira yace nice name,suna ta surutunsu ni ko hankalina na can gurin ganin ango ya fito sai ko gashi yasha kwalliya da wani farin yadi mai shara shara fari tas komai fari yasa har glass ban taba ganin yasa glass ba sai yau yayi kyau har ya gaji,takaici da kishi ne ya kamani raina ya sosu sosai na zuba mishi ido duban shi kawai nakeyi ba mamaki ganin karshe ne nake mishi dan yanzu ba gidan mu daya ba bani zan dinga dafa mishi abincin ba ba zan dinga dafa mishi lipton da daddare ba ba zai aikeni ba bare na mishi gyaran daki sai dai anty mimi bayan kwana kadan kuma su tafi England shi kenan nayi rashin yayanmu,nayi zurfi cikin tunani ban san su mami na min magana ba sai da suka dafani nayi ajiyar zuciya na dubesu yayane? Adams yace don Allah ki daina irin wannan tunanin wai ma tunanin me kikeyi?ban ma saurareshi ba na juya ina duban yaynmu ya shiga gaban motar Nasir,Nasir ya iso gunmu Adams zo muje mu kai angon can tun kafin ya kai kanshi,sai masifa yake mana wai in ba zamu je ba ya tafi abunshi,hankalina ya kuma tashi na juya nayi gida na barsu a nan mami da Amira suka shigo, kuka riris suka sameni ina yi dukkansu sun tausaya min tare da bani hakuri sunce na ringa danne kishina a gaban mutane dan kar suni,cikin kuka nace ba zan iya ba dan wani zazzafan so nake mishi ga mugun kishin shi dana ke fama dashi ku tava kirjina kuji ji nake kamar zai bude dan azaba kun san Allah Amira ko mimi bata kaini son yaynmu ba,sai dai tabi bayana,sun zubo min ido suna mamakina daga baya suka koma bani baki gami da kwantar min da hankali suka ce nayi shiru kar mama taji,nayi tsaki sannan nace ynxu bana shakkar kowa ya sani yanda nakeji ni kadai na sani nan dai suka dan lallasheni suka tafi.. So masifa ne yanda naga rana haka naga dare sai bayan nayi sallar Asuba sannan barci ya daukeni nannauyan barci mai cike da mafarkai kala-kala,mama ta tasheni karfe bakwai tayi lokacin da ciwon kirji mai karfi na tashi hankalin mama ya tashi sosai ta yiwa Alhj waya yana dakinshi sai gashi yazo,yace shirya ku je Rimi Clinic zan sameku ina yin wanka mama tace kodai a siyo mata magani a chemist?Alhj yace a'a ku daije in ciwonta ne fa kinsan da kirji yake farawa sannan ta suma ku dai tashi kafin suman yazo,ko wanka banyi ba muka tafi bayan mun ga likita ne sai ya bani gado raina baiso ba amma dole na kwanta an min allurai na samu bacci ya daukeni da sauri ba ni na farka ba sai wurin Azahar mama ta rike min hannu tana min sannu,na yunkura na tashi har yanxu saitin zuciyata bai daina zugi ba,da taimakon mama na samu naje bayi bayan na dawo ne na samu likita ya shigo zai dubani daidai lokacin yaynmu ya shigo shima suka gaisa da mama ya tambayeta jikina tacemashi da sauki,sannan ta fita likitan yace na kwanta sannan yace ya nake jin saitin zuciyata?nace da sauki sosai saidai yana min zugi har ynzu na dubi yayanmu da ya kafa min ido na kauda kai dan ni ko ganin shi bana sonyi,Doctor ya juyo gurin yayanmu yace yallabai tun safe nake neman ka a waya ban sameka ba ko da dai kana Amarci don Allah kayi hakuri na taso ka ko?yaynmu yace no ba komai matsalar ntwk ne shi yasa baki sameni ba,ya cigaba da cewa sanda kika yi min waya ina kan hanyar zuwa nan don Alhj mu ya sanar dani da na kirashi,likitan yace ciwonta yana barazanar dawowa da karfinsa abinda ya haifar mata ada ciwon ta sa wani abu a ranta sosai ta matsa ma kanta da tunaninshi gabanta yana mugun faduwa inta ganshi,ya batun da kai wancan lokacin? kasan fa sai da lallashi sannan zaku san matsalar ta,ku san kuma maganinta sannan muma namu aikin yayi kyau,yayanmu ya dubeni sannan yace kamar yanda na sanar da kai na san matsalarta fiye da kowa a gidanmu ita dai ta cika zafafa abu ne,bata son bin komai a hankali shine matsalarta,yaja kujera ya zauna kusa da gadon Iman!ya kira sunana na dubeshi har ynxu mamakin maganarshi nakeyi yasan matsalata?ke nan ya san ina sonshi?dan ni dai a sanina bani da wata matsala da ta wuce wannan.Anty yagana na shigowa Adams da mami da Amira suka shigo ya rusuna ya gaida mama taja Anty yagana suka fita,Adams ya dubeni ke yar gidana ya haka ta faru?nayi murmuahi sannna nace ikon Allah kenan Adams ba abin mamaki bane ko da mutuwa aka ce nayi,ya tsare ni da ido kar ki ja mon yar gidana karki min fatan mutuwarki dan ban san halin da zan shiga ba a raina naji zan iya auran Adams gsky ba zan tabbatar ma da yaynmu zancenshi ba shi kuma maye ne yake in har zai zauna da mutum sai ya san halin da yake ciki,Adams ya dawo dani daga tunanina kinyi shiru yar gidana ko jikin ne?a'a kadan kadan kirjina ke min ciwo su mami suka min sannu yaynmu ne yayi sallama ya shigo ganin Adams ya bashi mamaki sai naga ya dauke fuska a daure,hannu yaba Adams suka gaisa sannan yace dama naso daga nan gidan Nasir zan sameka muje ku gaisa da Amarya sannan mukai ku airport,ina su john suke?sun fita da Nasir nima ynxu naje sallama da yar gidana shine na samu su mami sukayi min bayanin tana nan sai mukazo amma fa ina ganin ba zamu tafi tare da su john ba,because of what?yaynmu yayi saurin tare shi da tambaya,Adams yace kana son sani ne?to saboda sister dinka yaynmu yace yana da kyau ka san su ma ta lagos zasu tafi dan haka muje mu sallamesu,Adams ya dubeni zan dawo yar gidana kinji ko?gira na daga shiko yaynmu harara ya sakar min ya wuce abinshi,mun jima dasu mami sannan mukayi sallama,sukan su yaynmu suna fita sai gidan Nasir inda rigima ta sarke tsakanin yaynmu da Adams yaynmu ya nunashi kai Adams kana mantawa da halina kasan fa in har nace no ba mai canja min ra'ayi ko?kasan haka kafi kowa ma sanin hakan amma kana bata ma kanka llokaci ne a banza,Adams ya dafa yaynmu Maska na maka alkawarin barin kanwarka akan sharadi guda biu na farko in tace bata sona na biu kuma in ka gaya min hujja mai karfi da ba ka son na nemeta ka fahimta?yaynmu yace don so bata sonka maganar hijja kuma babu kasan baka isa in maka karya ba baya ga tana da wanda takeso da na tsaya maka ka aureta amma ynxu am sorry to say bazata aure ka ba in kuma ba zaka bata lokaci ne to shi kenan,Adams ya kule Maska na gama sanin cewa kaima son yarinyar nan kakeyi tun lokacin da nasamu lbr ba dadynka ya haifeta ba,yaynmu yayi wata dariya mai kama da yake sannan ya dubi su nasir wayanda sukayi cirko cirkk suna duban abokan juna mafi kusanci da juna a england suna rigima a kan yar yarinya kamar yanda maska ke kiranta,kunji shi da wani magana kai kanka ka san in ina sonta baka isa ka nemeta ba bayan haka ba ni da ra'ayin auran kananan yara don bana son raini so please and please kabar maganar nan ma dan zamu iya rabuwa da juna,Adams yace and so what idan mun rabu?na shirya,Nasir yace dan Allah ku saurara haka kai Maska kayi hakuri mana tunda ka san ko shi wane ne in yana da wata matsala ne sai ka mishi bayani ga matsalar ka shi yasa kaga in da gyara sai ya gyara,yaynmu yace Adams yace namiji ne,bashi da wata matsala sai dai ya nemi matarshi a gaba Adams yace ai na samu yanxu kai kuma baka isa ka hana ba,Ok! zamu gani kana proud din baka taba neman abu ka rasa ko?to zaka fara akan wannan inji Maska,su John dasu Nasir sune suka bada baki kafin sukayi sallama amma banda Adams yace sai ya kara kwana biu,sun kaisu airport sannan suka wuce gidan amarya wacce ta cika fam da fushi,yaynmu ya dubeta madam kimin afuwa kinsan ina tare da baki yau zasu tafi ko shiyasa ya fada lokacin da yake zaunawa kusa da ita su Nasir da Adams ma suka zauna,ta dan yatsina fuska sannan ta gaishe su yace yunwa fa mukeji fa,ta dube shi baku ci binciba?ayya gashi nayi bakin kawaye momina ne ta rako su shine suka cinye Dukda,ranshi ya sosu amma bai nuna ba sai yace shi kenan kawo masu wani dan abin sha mana,ta mike tana karairaya Nasir ya bita da kallo sannan ya dauke kai shima irin matan nan basa birgeshi sam bata son mutane yaci ace yanda suke abokan Maska ace sun saba amma ita sai girman kai kamar yar wani da wata gashi daga gani za tayi rowa kai shi kyanta ma bata birge shi mace a bushe haka?fari ne da hanci kawai shi kuma bai ma cika son dogon hanci ba,tunanin shi ya katse lokacin da taje musu da robar ruwan Cway da kofuna,kunya ta kama yayamu ya dubeta ke ba wani mai dan zaki ne?bana yiwa Kabir waya ya kawo drinks ba?ta dan yatsina fuska zata tashi Nasir yace no yi zamanki don ni dam nake sai dai ko Adams, Adams da ya zuba tagumi yana tunanin Iman ya ce am ok nima a koshe na ke,sun dan yi hira sam ita bata sa masu baki ba TV kawai take kallo ko da zasu tafi ba tayi musu magana ba sai Nasir ne yace mu mun wuce,to kawai tace suka fita yayi masu rakiya ya dawo su kuma su ka nufi gurinmu a Asibiti. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 Washegari aka sallame ni na dawo gida da kundurin cusa son Adams a zuciyata don haka duk sintirin da yaynmu yake yi bai burgeni ba duk da in har ina ganshi sai gabana ya fadi, kuma sonshi na nan daram a raina,daren ranar sai ga Adams ya zo mani sallama yana min bayanin dan dai zasu yi wani wasa ne a club dinsu kuma wasan yana da muhimmanci sosai da ba zai tafi ba gashi ba Maska bai kamata kuma shi ba ya nan ba,nace ba komai naji sauki kuma ga waya ai,ya ce to bani no naki in yaso in naje sai na dinga kiranki sannan ki bani tabbacin kina sona dan Maska ya gaya min kina da wanda kike so,haka ne?nace batun wanda nakeso dai bai taso ba dan babu sai dai game da kai,in mun waya zan sanar da kai ina jin kunya ne yanxu,yayi murmushi shi kenan yar gidana a zuciyata nace kunyar karyar da zan maka ne ya sa ba zan iya fadama baki da baki ba dan na san ba wani sonka nakeyi ba ne burgeni kawai kakeyi,kyautar wani kyakkyawan agogo da turare ya yi min nayi mishi godiya mukayi sallama sannan yace min idan ya sami sukuni zai zo ba da jimawa ba kuma jiya ya gabatar da kanshi a gurin Alhj,da sauri na dubeshi me yace maka?ya ce yace kar na damu gurin su manya ba matsala in dai sunyi bincike sun gano asalina a Ghana,nace yauwa Adams kana da yare ne?ya ce eh yace mu asalinmu fulanin yola ne yan Adamawa zama ne yakai kakaninmu suka haifi iyayenmu muma aka haifemu a Ghana,nayi karatuna duka zuwa Degree wasan kwallo kuwa ina primary nake zakara kuma ni ne babba a kaf gidanmu kanne na hudu maza da mata,matan babana biyu ne kuma har ynxu muna zuwa Adamawa kuma suna zuwa babana yana da sarautar matawalle dan haka duk salla familynmu a can muke yi ko ni in ina gida tare muke zuwa,kin fahimci takaitaccen tarihina? nace na gane yace to muna da yawa sai ki shirya in munyi aure duk sallah zamu zo daga England Adamawa zamu sauka haka nan in kin haihu a can zaki zauna ko in baby yayi kwari sai nazo na tafi da ku dariya nayi nace Adams kenan har ka tsara komai yace yes haka kullum nake mafarki nace to ba ka fadamin me kayi Degree a kai ba sannan cikakken sunan ka,yace nayi Degree akan,cikakken sunana shine Adamu Salisu Adamu, Abokaina su suka sa min Adams sai ya zama har JC na Adams suka samin kinji yanda abin yake,sai naji Adams ya kara bani sha'awa kuma zan iya kukutawa in aure shi,mun yi sallama dashi nayi mishi rakiya har wajen gate mukayi sallama akan sai naji shi a waya. Ni,Mami da Amira tafe muke kan hanyar mu ta zuwa kasuwar unguwar Rimi zamu raka Mami ne amsar dinki muna tafe muna hirar Adams,nace mami ni fa yanxu Adams kawai na tsaida ma zuciyata duk da na san cewa bashi ne zabin zuciyata ba zai fi min kwanciyar hankali,Amira tace na goyi bayanki Mami tace sam ba zata yiwu ba kina tunanin shi ba wata matsala daga dangin shi?sannan ba shi kike so ba in kika jure wani abu wani ba zaki jure ba musamman ma da yake ba shi kike so ba gara wanda kake so zaka hakura da wani abun albarkacin son nan shiko daban ne,nace Mami Haj Yaya da Haj Laure ba zasu bari na zauna lfy ba sannan da wanda na ke sonshi baya so na gara wanda nake ki yake sona zan lallaba da Adams,mun tsallaka daidai shagon Ubale zamu shiga cikin kasuwa sai ga wata mota ta tare mana gaba baka ce wuluk Mami tace motar nan tayi min kyau,kafin nayi magana har mai motar ya fito wani mummunan fduwar gaba naji yayin da muka hada ido da mai motar,shima ni ya tsura ma ido yana kallona mami ta ce kin sanshi ne?nayi karfin hali nace a'a naja hannun Amira jikina ba karfi sai mutumin yace uwata ni zaki gani ki wuce uwata?kin bani mamaki uwata zo kar ki tafi ina Habiba? Sai na soma kuka mai karfi mutane kallona sukeyi ya bar jikin motar ya nufo ni da gudu na tsallaka titi na nufi layinmu ina jiyo muryar shi yana fadin uwata kar ki kuma tfy ki barni zo mana mamana,ai sai gida ina tafe ina kuka kamar wadda aka ce uwarta ta mutu ban damu da kallon da mutane suke min ba jikin Mama na fada tana zaune a firgice ta tashi tana fadin lfy?menene? Ina sai kuka ruri nake Mami da Amira suka shigo a sukwane Mama tace Amira me ya faru? hankalinta a tashe ta ke magana Amira tace mama muna tfy zamu shiga kasuwa sai muka ga wata mota har muna cewa kai motar ta hadu kawai sai mai motar ya fito yana ganin Iman kawai sai mukaji ya hau cewa uwata dama kina nan uwata?zo nan kawai sai muka ga tana kuka ta rugo shine mutumin yace mun san gidansu? mukace eh shine ya dauko mu ynxu yana nan waje wai mu kiraki,mama tace baku da hankali daga ganin mutum sai ku nuna masa gidanku?dama ya tafi daku,ta daka masu tsawa me zakuje ku ce masa ba zan fito ba a ina ya sanni,Amira da Mami suka kada baki wllh mama yayi kama da Iman sosai mama tace ba shi bane nace kuje ku sallame shi mana,cikin kuka nace mama baba ne fa,mama tayi shiru dama nasan ta gane can sai tace Amira kije kuce mishi mijina baya nan dan haka ba zan iya ganinshi ba su Mami suka sameahi ya kifa kai jikin sitiyarin mota mami tace baba da sauri ya juyo yaushe rabon da yaji wannan kalmar yana kishin jin kalmar nan ga zatonsa Iman ce amma sai yaga yaran dazu,ya dubesu ina Habiban?suka ce tace mijinta baya nan shi yasa ba zata iya ganinka ba ba. Na idar da sallar magriba ina zaune a takure duk tausayin mahaifina ya cika ni Alhj ya shigo da sallamarsa ba sosai yake shiga dakin matanshi ba sai in bukatar hakan ta taso ya karaso gurina yaya dai Iman?lfy dai ko? nace lfy klau ka dawo lfy ya kasuwa?Amalhmdl Iman kuma lfy lau muka dawo ina Habiban fa?nace tana cikin dakinta,ya nufi dakin mama yana fadin Habiba sarkin hidima hala wani aikin takeyi,sun jima sannan suka fito naga fuskar mama murtuk babu alamar dariya ta zauna kan kujera shima ya zauna kan daya kujerar dake kusa dani yana fdin ban sanki da fushi ba ba halinki bane ruko,kuma ba kya gaba,uhm kuskure mutumin nan yayi ya kuma gane

Chapter 2 of 5