An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
https://whatsapp.com/channel/0029Vb5xdoy2975BcTM5m133
💗𝙎𝙄𝙍𝙍𝙄𝙉 𝙎𝙊💗
𝙎𝙩𝙤𝙧𝙮 & 𝙬𝙧𝙞𝙩𝙩𝙞𝙣𝙜 𝙗𝙮
𝙈𝘼𝙍𝙔𝘼𝙈 𝙎𝙏𝘼𝙍⭐ 𝙔𝘼𝙍 𝘽𝘼𝙄𝙒𝘼𝙍 𝙅𝘼𝙅𝙄𝙍𝙏𝘼𝙏𝙏𝙐💪✍🏻
𝙈𝙮 𝙜𝙧𝙤𝙪𝙥 𝙡𝙞𝙣𝙠
https://chat.whatsapp.com/JQlwOnhVAxnFwt1EU6AqU2?mode=gi_t
𝙏𝙞𝙠𝙏𝙤𝙠 𝙖𝙘𝙘𝙤𝙪𝙣𝙩
https://tiktok.com/@maryamumar8361
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
PAID BOOK.
BOOK ONE
FREE PAGE
1 & 2
A hankali cikin nutsuwa nike juya manyan idanuwa dana ɗan shanye kaɗan, kamar na mai jin barci a cikin nashi idanuwan waɗanda suka kaɗa zuwa launin jah, yayinda na kama ƙaƙƙarfan hannunshi cikin nawa ina murzawa a hankali, matsawa na yi da fuskata a saitin tashi fuskar da taimakon tuntuɗon da nayi ta hanyar tsayuwa akan yatsun ƙafafuwana, tattausar sumbata wacce ta sakashi lumshe ido tare da shaƙar lumfashi da ƙarfi, da hannunsa wanda ya zagaye ƙuguna yai amfani wajen janyoni na faɗa akan faffaɗan ƙirjinshi, ɗayan kuma ya ɗaurashi akan yalwatacciyar sumar kaina, bai tsaya anan ba sai da ya idasa kashe min jiki da hot kissis.
Da kyar bayan shulewar mintuna na kwaci kaina, sannan cikin sanyi da taushin murya nace da shi.
"Dear lokaci yana tafiya, zakayi leti, ka je zan kasance cikin jiran lokacin dawowarka, zaka tafi da rakiyar zuciyata, gangar jikina kuma zata jirayi dawowarka, kai ɗin na dabanne a rayuwata, ina tsananin ƙaunarka."
Nai maganar ina kallon tsakiyar cikin idanuwansa fuskata ƙayace da murmushi me sanya nutsuwa a ruhi da gangar jiki.
Da yaren da yafi kwarewa yai min magana, wato lumshe ido tare da jujjuyasu kamar yanda ya saba yimin a kullum, ban gushe daga wajen ina jero mashi kyawawan addu'o'i waɗanda mata nagari kan jerawa mazajensu a lokacin da zasu fita nema ko wani abu uzuri.
Sai da na tabbatar ya ɓace wa idanuwana sannan na tsugunna ƙasa tare da tallafar ƙafata da ke sanye da safa me launin kore, wasu zafafan hawaye na sauko min, cikin taƙa tsantsan na fara cire safar, fara tas ɗin ƙafata ce ta bayyana, daga sama wajen yatsun ƙafar kuma yayi wani irin jah ga kwanciyar jini nan gami da kumburi akan babbar yatsar ƙafar, zamewa na yi a ƙasan wajen tare da riƙe ƙafar ina kukan tsananin azabar da nike ji, a hankali na rarrafa zuwa ɗaki, ina isa na zube yaraf a ƙasa tare da ɗaura ƙafar tawa akan sofa cikin rashin abin yi, banyi mintuna biyu da kwanciya ba wani irin wahalallen barci yai awon gaba da ni.
Zaune suke su biyu a cikin ɗakin, ɗaya na wajen taga tana leƙen waje, lokaci zuwa lokaci tana riƙe haɓa tare da taɓe baki irinna gulma, sai bayan da waɗanda take leƙe suka wuce sannan ta saki labulen tare da gyara zamanta irinna gulma tana faɗin.
"Wallahi kallo yabarki a baya Adda, wai kinga salon sanabe da munafurci a wajen waccan matar me kama da jan ƙosai, jiya bana faɗa maki Yaya ranshi a ɓace ya dawo ba?." tai maganar ƙasa-ƙasa alamar bata so aji ta.
Wacce aka kira da Addace ta ajiye wayar hannunta tare da tattaro duka hankali da nutsuwarta ta maida wajen ƙanwarta, itama da ƙaramin sauti ta ce.
"Hummm aimu muna ganin sanabe a gidanan, nasan gulmar da zaki yi min bai wuce yanda ta je ya buɗe mashi gida cike da iyayiba, shi kuma kuturu uban zuciya irinta gado ya shigo da mashin a fusace harya taka ma ta ƙafa, amma dan tsabar sanabe kilbibi ta wayance bata nuna komi ba, inafa hango kyallin hawaye a idonta, amma matarnan sai ya fuske cike da salo ta ƙawata fuskarta da murmushi me kyau da birgewa, sannan ta wani narke gami da shagwaɓe fuska, ta taryeshi cikin kulawa, sam bata damu da yanda yake fuska ɗaure ba haka yaita janshi da maganganu, shiko yana tsaye ƙerere kamar kurtun soja, gaskiya na yarda wannan shine SIRRIN SO da matar yaya ta ke yiwa Yaya."
"Hummm wallahi Adda sautari nakan tausaya ma ta, tana ƙoƙari sosai, gashi kullum cikin ƙirƙirar sabon salon iyayi da sanabe wanda zata burge yaya ta ke, gaskiya sanin SIRRIN SO duniya ne."
Haka ƴan mata biyun suka ci gaba da tattaunawa akan batun, kafin daga bisani suka tsagaita da labarin, suka yanke shawarar rage ayyukan gidan.
Haɗuwa suka yi suka share gidan tas, sannan suka yi mopping, tsakar gida, toilet da sauran ɗakunan da ke gidan, bayan sun duba sunga babu wani wanke-wanke, domin matar gidan bata yarda da ajiye kwanuka babu wanki ba, komi aka ci bata jin ƙyuiwa wajen tattare kayan ta wanke bayan angama ci, komawa ɗakinsu suka yi suka ci gaba da harkokin gabansu, su na taɓa labari lokaci zuwa lokaci.
Kamar yanda al'adarsa ta ke, du lokacin da ya shiga kasu bayan ya gabatar da addu'a wacce haziƙar matarshi take yi mashi tuni adu lokacin da zai fita daga gida zuwa kasuwa, sai ya ajiye mashin ɗinshi a ma'ajiyarshi, fuskarshi ba yabo ba fallasa ya isa wajen abokan aikinshi suka gaisa a mutunce, sannan ya sauya kayan jikinshi zuwa masu rangwamen nauyi dan samu sauƙin aiki, babban shagone wanda ke cike taf da kayan provision, du wani abun buƙata akwaishi a shagon, daga gaban shagon kuma bahuna ne na kayan awo danginsu Alkama, Dawa, Gero, Masara dasauransu, bai fi mintuna biyu da buɗewa ba, mutane suka cika wajen anata siyayya, kasancewar du layin babu shagon da ke da sauƙin kaya kamar na shi, kuma dawahala aje neman abu ba'a samu ba, shiyasa shagon koda yaushe cikin hada- hadar siyayya ake, bai jima da zuwa ba, wasu matasan yara su biyu suka iso, nan suka kama mashi akaci gaba da sallamar customer.
A hankali na shiga buɗe lumsasun idanuwa gami da ƙoƙarin sauke ƙafata da naji ta riƙe, ji nai kaina na sarawa sama-sama, sannan jikina ta ko ina nayi min ciwo kamar wacce aka lakaɗawa shegen duka, kodayake anyi min abin da ya fi dukan, tunanin yanda tun jiya nike hidima har zuwa yau na shiga yi.
"Wash Allahnah, Baby nagaji dayawa wallahi." Kyakkyawan dogon farin matashi me cike da kamewa ya faɗi yana kaina zaune da dukkan ƙarfinshi a saman sofa, yana lumshe gajiyayun idanuwansa waɗanda nike iya hango tarin gajiya a cikinsu.
Cikin taushi da sanyin murya gami da tsantsar kulawa na ce.
"Ayya sannu Sadauki, ai kana ƙoƙari sosai wallahi, Allah yaci gaba da dafa maka." nai maganar lokacin da na gama tsiyaya ma shi sassanyan kunun aya wanda ke tashin ƙamshin citta da karamfani, miƙa ma shi na yi fuskata yalwace da murmushi, a maimakon ya amshi kofin sai ya watsamin birkitatun idanuwansa a cikin nawa, fuskarshi da alamar murmushi wanda bai bayyana ba.
Sanin mi ya ke nufi ya saka na ajiye cup ɗin, sannan na zare ƙaramin hijabin jikina na aje gefe, janye table ɗin gabanshi na yi zuwa gefe naiwa kaina masauki akan cinyoyinshi, sai de ban saki nauyi ba, ɗaukar cup ɗin nayi a hannuna nai basmala gami da kaiwa bakinshi ina jifarshi da kallon so mi kashe garkuwar jiki.
Yayinda sanyin kunun ke ratsa hanjinshi yana sake safkar mashi da kasala, haka mayen kallon da nike jifarshi da shi ke kassara zaman lafiyar gagar jikinshi, a taƙaice dai sanyi biyu ya haɗar ma shi lokaci guda, tas ya shanye kunun cikin cup ɗin tare da sauke nannauyar ajiyar zuciya, sai kuma ya sake jana dakyau zuwa jikinshi, lumshe ido ya yi lokacinda sassanyan ƙamshin turarena ya mamaye hancinsa, ɗaura kanshi yayi a kafaɗata yai shiru kamar me barci, ahankali na fara ƙoƙarin tashi daga kanshi, kallon miye haka ya jefeni da shi, cike da girmamawa na ce.
"Zan haɗa ma ka ruwan wanka ne, ko watsa ko zaka ji sanyi." Lumshe min idanuwansa kawai yai, na juya na shige bedroom, kai tsaye na nufi toilet ɗinmu ɗan madaidaici na haɗa ma shi ruwa masu ɗan gumi duda ana zafi, nasan baya son ruwa masu sanyi sosai, haɗaɗɗen turaren wanka wanda sam bana rabo da shi na zuba mashi a ruwan sannan na ɗauko wankakun fararen towel guda biyu, dan nasan dolene nima na sake yin wani wankan na rataye.
Lokacin dana koma falo a maimakon in tasheshi tai tsaye sai na koma gefe na ranƙwafa tare da balle botiran gaban rigarshi hakan ya saka ya buɗe ido, lallausan murmushi na sakar mashi gami da furta. "Sorry." a saman laɓɓana cikin salo, da karsashi ya miƙe tsaye dan in samu damar cire mashi rigar, kasancewar yafini tsayi sosai ya saka idan zan cire ma shi riga sai ya ranƙwafo sannan.
Cikin sassayan yanayi muka gabatar da wankan, yayinda ko wane motsi ke kasancewa cikin nunawa junanmu kulla da soyayya.
A gurguje muka shirya ciki kaya maras nauyi, na gabatar mana da abinci muka ci, nan muka zauna zaman fira duda rabi da kwata nice ke firar shi dai iyakarsa kasheni da salo-salo na ƙauna, me tsayawa a rai, ahaka barci ya ɗaukemu, wanda bamu farka ba sai ana kiran sallar magrib, a gurguje ya watsa ruwa sannan ga sake shiryawa dan daga massalaci zai wuce wajen duba aikin ginin sabuwar plaza da yake shirin buɗewa, lafiya lau muka yi sallama cikin farin ciki ya fice, bayan na gama sallah na tashi zuwa ɗakin ƙanensa mata da suka zo garin wajen wani biki, sai sukai rashin sa'a anɗaga bikin, shine na tsaidasu na hanasu komawa tunda badayawa aka ɗaga bikin ba, sati biyu kaɗai aka ƙara, Farida ita ce babba, sai Ummul autarsu gaba ɗaya, yaran basu da matsala sam, su na da daɗin zama sosai, sai de na lura kamar su na da saka ido, hakan ya saka nike taka tsantsan da su, tare da tsare mutuncina, taso su na yi a gurguje muka fara shirin yin girkin dare, muna yi muna fira cike da nishaɗi, yayinda Ummul ke bani labari wani saurayin Addarta Farida mai baƙin macin tsiya, Yayansu Farouk mijina Saraki yasha korarshi sau babu adadi amma ya nace ya liƙe, tun ana korarshi har suka gaji suka kyaleshi, bayan mungama aikin girkin cike da farin ciki muka jere komi, domin muna haɗuwa muci abincin safe dana dare a tare da su, na rana ne kawai bai amince min in haɗe manah ba shima kuma koda bai hana ni ba, nima bazanyi hakan ba domin nasan halin kayana, yana yawan son kusanci dani da rana idan ya taso daga shago, shiyasa nike tsananin kulawa da wannan lokacin.
Mungama komi sai tattare kitchen kawai saiga ƙarar horn ɗin mashin ɗinshi, du saida ya rikita mana kunnuwa da uban horn ɗin, da hanzari na gabana na dokawa da ƙarfi na gaɗa falo dan ɗauko key ɗin gidan, domin da zarar marice yayi nike kulle gidan saboda tsaro, unguwarce sam batada kyau ana yawan samun hatsaniya da matasa.
Ina ƙoƙarin zuwa zauren dan buɗe mashi ƙofar, ashe akwai key a wajenshi harya buɗe ya shigo, nayi ƙoƙarin janye ƙafata daga hanyarshi sai de ina, yanda ya afko da gudu sai da yai nasarar bi yakan yatsun ƙafana, wani irin zugin azaba gami da raɗaɗine ya ratsani tundaga kan ƴan yatsuna har tsakiyar kaina, dakyar nai nasarar mazewa ganin irin mumunan yanayin fushin da ya shigo da shi, ƙawata fuskata nai da sassanyan murmushi me kama da yaƙe, sannan cikin taushin murya na shiga kwantar ma shi da hankali ta hanyar yi mashi sannu da zuwa, bai kulani ba ya shige ɗaki, kallonsu Farida da ke tsaye fuskokinsu aɗan firgice nai, alamar ba komi nai musu sannan nabi bayanshi.
Wa ta iriyar damƙa yai min wacce ta saka ni kusan sakin zawayi dan tsoro, gabana in banda luguden duka babh abin da ya ke, zufar tashin hankali ta fara tsatstsafomin tako ina, amma sai na maze na dinga bashi haƙuri a tausashe, duda haka bai fasa yin abin da nike tsananin tsoronba, dan kanshi tsaye kuma a zafafe ya ɓarke rigar jikina tare da yin fatali da dukan suturar jikina, damƙa me zafi ya aikawa albarkatun ƙirjina, ban gushe wajen aika mashi da saƙonni masu zafi ba domin na rigada na karancin SIRRIN SO irinna Saraki, kuma wannan ita kaɗaice hanya mafi sauƙi da zai sauke fushinshi, hakan ya saka nai amana tare da sadaukar mashi da kaina ta hanyar tayashi yaƙin.
Tun inayi da armashi tare da dauriya, har na sare nai lakwas, daga ƙarshe dai sai da aka je matakinda nafara kuka da magiya, amma abanza, dan babu abinda kukan nawa ke sakashi sai ƙarin ƙaimi.
Bai sararamin ba sai da ya samh cikakkiyar gamsuwa, yayinda ni kuma na azabtu matuƙa, aiko kamar jira nike ya dawo daidai nan na dasa da tawa rigimar wacce ta nemi ɗimautashi, nan ya zage yanata aikin rarrashi da ban baki, daga ƙarshe dai bayan ya taimaka min mun tsabtace jikunanmu harda labari aka fara bani, ni kuma nai biris na dinga shagwaɓe ma shi, da ƙyar ya lallaɓani mukai barci, barcin da bamu daɗe da yiba ƙarar alam ya tada mu, ido a rurrufe mukai sallar sannan muka koma mukaci gaba da aikin barci, bamu muka farka ba sai ƙarfe tara na safiya, shima ƙarar kiran wayarsa ne ya tashemu, inda na samu sauƙi nemanshi ake cikin gaugawa, hakan ya saka na taimaka mashi ya shirya a gurguje, ruwan tea kaɗai ya saka a cikinshi ya fice badon yaso ba.
Sai bayan da ya tafi sannan na samh damar ƙarewa kumburarru yatsun ƙafata kallo.
Da hanzari na miƙe tuna banyi koda shara ba, sai de mi ina fitowa tsakar gida naganshi fes alamar anyi shara, duda dama ba wani dattin kirki ke akwaiba, naji daɗi sosai gami da sakawa su Farida albarka, sai na nufi sauran ɗakunan da niyar gyarawa nanma naga sun gyara, hatta kewayen waje du sun wanke, sosai na ji daɗi, a hankali na ɗingisa zuwa ɗakinsu na ɗaga labule da sallama.....✍🏻
DAGA ALƘALAMIN MARYAM STAR⭐⭐⭐ƳAR BAIWAR JAJIRTATTU....✍🏻💪
PAID BOOK NE BOOK ONE FREE.
BISSALAM
Follow the 🌹MARYAM STAR⭐⭐⭐ HAUSA NOVELS AND MORE 𝐶𝐻𝐴𝑁𝑁𝐸𝐿✍️📚📙✏️ channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb5xdoy2975BcTM5m133
💗𝙎𝙄𝙍𝙍𝙄𝙉 𝙎𝙊💗
𝙎𝙩𝙤𝙧𝙮 & 𝙬𝙧𝙞𝙩𝙩𝙞𝙣𝙜 𝙗𝙮
𝙈𝘼𝙍𝙔𝘼𝙈 𝙎𝙏𝘼𝙍⭐ 𝙔𝘼𝙍 𝘽𝘼𝙄𝙒𝘼𝙍 𝙅𝘼𝙅𝙄𝙍𝙏𝘼𝙏𝙏𝙐💪✍🏻
𝙈𝙮 whatsapp 𝙜𝙧𝙤𝙪𝙥 𝙡𝙞𝙣𝙠
https://chat.whatsapp.com/JQlwOnhVAxnFwt1EU6AqU2?mode=gi_t
𝙏𝙞𝙠𝙏𝙤𝙠 𝙖𝙘𝙘𝙤𝙪𝙣𝙩
https://tiktok.com/@maryamumar8361
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
PAID BOOK
FREE FAGE
BOOK ONE.
3 & 4.
"Allah sarki yaran albarka, sannun ku da ƙoƙari na tashi naga kusha aiki, Allah ya yi albarka."
Farida ce ta dubeni cike da kulawa sannan ta ce.
"Yauwa Anty kema dannunki, ya ƙafar ta ki dasauƙi ko?."
Tai maganar tana kallon yanda babbar yatsar ta kumbura tai jajur.
"Anty sannu da jiki, gaskiya ya kamata ki je a duba ƙafar, naga harta soma ɗurar ruwa karta zame maki ɗan banza."
"Nima na yi wannan tunani wallahi, amma bari mugani zuwa anjima idan ba ta yi sauƙi ba sai in faɗawa Yayanku." ina kallon yanda suka haɗa ido alamar gulma, ni dai nai ficewa ta nabarsu ina sake jaddada godiya a garesu.
"Anya kuwa Faruk baka cutar yarinyar mutane da wannan halin naka, wallahi ina tausaya ma ta da take iya jurar zama tare da kai, kai ɗinan zama da kai babu sauƙi wallahi."
Da alamun damuwa a fuskar Faruk ya ce.
"Bama wannan ba, shin ko kasa𝙣 baza𝙣 iya koda kwatanta rabuwa da yarinyar nan ba, tana da kyawawan ɗabi'u ga hankali da sanin ya kamata, sannan uwa uba yarinyar tasan SIRRIN SO, ban taɓa tunanin zan sake komawa soyayya kodawasa ba sai akan yarinyarnan, banyi ƙarya ba idan na ce ban taɓa zama da mutum wanda naji daɗin mu'amala da shi irin ita ba, tana da sauƙin kai sosai."
Nisawa abokin firar ya yi, cikin samo mafita ya ce.
"Yanzu dai muje a fara samun maganin wannan matsalar saura na ji da shi daga baya."
Babu musu Faruk ya miƙe tare da ta da mashin ɗinshi, nan abokin nashi yahau baya suka ɗauki hanya su na taɓa ƴar hira.
A wani babban islamic cemist suka tsaya, bayan sun gaida da kemis ɗin abokin Faruk ya ɗaura da faɗin.
"Malam munzo ne akan matsalar wannan abokin nawa, yana neman shawarwari game da matsalar da ke damunshi."
A nutse ya tambayi Faruk abin da ke damunshi, nan Faruk ya daure ya yi mashi bayani akan irin zafin fushin da yake da shi, sannan kuma baya iya sarrafa kanshi agaban matarshi idai yai fushi, shi yasan yana ƙwararta sosai kawai de tana da haƙuri da juriya ne, sannan kuma idan akwai maganin da zai rage ma shi ƙarfi yana so.
Sosai malamin ya bashi shawarwari harma da magunguna, suka yi godiya sosai tare da sallamar malamin kiɗin magungunanshi suka ta fi.
ABUJA NIGERIA
Haɗaɗɗen ƙayataccen gida ne wanda ya amsa sunan shi, ginine irinna turawa me kyau da tsari gwanin burgewa, Wa ta shahararriyar C. class ce fara ƙar ta doshi makeken get ɗin gidan tana doka uban horn, da hanzari masu gadin gida da suka kasance sojoji suka wangale makeken get ɗin, nan take matuƙin motar ya harbata dantsananin gudu zuwa cikin haɗaɗɗen gida, ko parking bai yi da kyau ba ya ɓalle murfin gami da fitowa a fusashe, kyakkyawan matashi ne wanda bazai wuce shekaru ashirin da tara zuwa talatin ba, farar kyakkyawar fuskarshi a burkice, lallausan gashin kanshi a barbaje babu wani gyara, farar t.shet ɗin jikinshi boturan gabanta a buɗe, yayinda faffaɗan ƙirjinshi wanda ya ƙawatu da kwantaciyar suma ya bayyana.
Da wani irin sauri ya ke tafiya yana furta.
"Mom! Mom!! Mom where are you?."
Ya faɗa lokacin da ya sadu da babban falon gidan, in da mutane a ƙalla shida ke zazzaune a kan dining su na breakfast a gayunce.
Wata fara tas ɗin yar gayun mata ce wacce taci ado cikin tsadaden material ta tashi da sauri fuskarta da alamun damuwa.
"Mom, kinga wannan bagidajiyar yarinyar ko? kinganta ko Mom." Yai maganar a rarrabe cikin fushi yana nuni da waje, kafin wacce aka kira da Mom ta ce wani abu, sai jin saukar muryar mace tayi tana faɗin.
"Wallahi Mom na yi danasanin auren wannan shashashan ragon ɗan naki wanda bai dan komi ba sai fushi da zafin zuciya, bai iya komi bs sai...."
Kafin ta ƙarasa faɗa Mom tai saurin takawa zuwa gabanta ta rufe bakinta da hannunta tare da girgiza ma ta kai alamar tai shiru.
Cike da fitsara ta janye hanun Mom ɗin daga bakinta sannan ta ci gaba da faɗin.
"Gaskiya nidai abarni in yi magana, tayaya za'a dinga tauye mutum a hanashi magana, dama can saida Mommy ta ce da ni kar....."
"Meenal miye haka kike yi, rashin kunya za ki yiwa Mommyn taku, miyasa kike haka dan Allah." ɗayar matar da ke zaune a dinning ta yi maganar cikin sauri, jin Meenal na ƙoƙarin yin ɓaranɓarama.
Cuno baki irin na shagwaɓaɓɓu sangartattun yara Meenal ta yi, sannan ta juya akalarta zuwa wajen dinning ɗin tana sakin huci, ko zama bata gama yi ba ta ɗora da faɗin.
"Wallahi Mommy na gaji da wannan jarababben auren, ni kawai ya sake ni inyi rayuwata ni kaɗai, da ace tun farko kin faɗa min haka auren ya ke da bazan yarda inyishi ba, koda zanyi ba da mutum irin Muneeb ba, wallahi bazan sake koda kwana ɗaya da igar banzan aurenshi akaina ba sai ya sake...."
" Muƙut" ta haɗiye yawu bayan ta yi tozali da kamulalliyar fusarshi a lokacin da ta ɗago kai, mummunar faɗuwa gabanta ya yi a dabirce tana kyarmar baki ta furta.
"Dah,,,, Dad,,,, Daddy barka da safiya." sai kuma ta kama susar kumatunta cike da kunya.
Baƙar harara Mommy ta dinka aika ma ta ƙasa-ƙasa ranta na suya da abin da Meenal ɗin ta aika, shikenan ta ida rushe sauran yardar da Daddyn ya yi da ita, dama ƙaƙa lafiyar giwa bare ta yi hauka, cike da borin kunyar abin da ba ita ta aikata ba ta cewa Daddy.
"Dear ana gaida kai fa."
Sake ɗaure fuskarshi ya yi tamau tare da yin biris da su kamar bai san su na wajen ba ya cigaba da aikawa cikinsa.
Ƙasa-ƙasa Mommy ke zungurar Meenal tana ma ta signal akan ta tashi daga wajen, amma ta gagara ganewa saima ɗaukar cup ɗin da Mom ta aje babu shiri lokacin da suka shigo.
Ƙaƙƙarfan tsaki Daddy ya saki "Mtswwww" gani da ya yi Meenal ta ɗauki cup ɗin Mom, ranshi a ɓace ya miƙe tsaye tare da aikawa Mommy kallon zamu haɗu.
"Na shiga uku ni Kubrah, dan ubanki baki da hankali ne??? kamar dai kin mance tsari da dokar Daddyn na ku da za ki shigo gabanshi kina wannan haukar, abin naki bai tsaya nan ba sai da kika haɗa da taɓa ƴar gold ɗin tashi, wayace maki ana taɓa wannan matar a gabanshi a zauna lafiya, yau ni Kubra na ɗebo ruwan dafa kaina, tsinanniyar yarinya kawai shashasha."
Mommy ta faɗa bayan wucewar Daddy.
"Oh mah god! acan ban huta ba, anan ma na zo ban huta ba, wai mi kuke nufi da ni ne, to wallahi bazan zauna a ƙasarnan ba London zan koma a yau ba sai gobe ba."
Tana gama faɗin hakan ta dire cup ɗin hannunta tare da miƙewa fuuu ta bar wajen, da sauri