danna waya, kyakkyawar tarba ta yi min ta hanyar tungume ni tsaf tana shafa bayana da alamar rarrashi.
Cikin sanyin sauti ta ce da ni.
"Sorry Sabrah, dama ba nace da ke karkuyi fitarnan ba kika biyewa Yayanki kuka fita, kina ganin hadari ya haɗe gabas da yamma ke ga uwar kwaɗayi ko, hummm ai gashinan kin janyowa kanki dan haka ba za ki ɗaga min hankaliba cikin dare, salin alin ki ɗauki ƙafarki ki bishi ku ƙarata can ke da shi."🌹
Ina zuwa nan a tunani wani ƙaƙƙarfan kuka ya kubce min.
Tinowa da zuwan damuna nan kusa na sakani tsananin tashin hankali gami da zullimi, har wa ta rama na yi saboda tsabar tunani da zullumin da ke raina, tsorona bai wuce yanda yanzu Faruk ke yawan yin dare ba, yanzu idan ya fita bayan azahar baya sake dawowa sai bayan isha'i wani lokacin har sai barcin rashin aikin yi ya ɗauke ni yake dawowa, koda wasa ban sake yi mashi maganar zuwa gidanmu ba, dan ban mance zafafan maganganun da ya watsa min ba waɗanda daidai da second basu taɓa barin zuciyata ba.
FARUK
"Ina so ki tsaida hankalinki waje ɗaya ki nutsu, ki watsar da komi dan ina so ayi maganar aurenmu nan kusa, ina so in tare a sabon gidanmu tare da ke, bazan iya barinki ba na gane kece mahaɗin rayuwata, zuciya da gangar jikina ke take muradi, kece kika san SIRRIN SO na, yanzu ya kike gani zamu yi."
Faruk ya yi maganar a miskile, da wani irin mamaki Luwai ta kalleshi da shanyayun idanuwanta irinna marasa kunya, ranta ƙal ta ja da baya ta dage ƙugu dannan takai hannunya saman hancinta ta tangaɗa wa ta irin rangaɗeɗiyar guɗa, sannan ta guya ta karkaɗawa Faruk mazaunai ta kuma juyowa takaiwa fuskarshi sumbata daga bisani cike da bariki ta ce.
"Oh my sugar, najo daɗin wannan bati naka, zanyi alfahari idan na mallakeka a matsayin mijin aurena, wayyo daɗi, ni da Sugar a duniya ɗaya." Ta yi maganar tana haɗe yatsun hannunya waje ɗaya, sam ta kasa nutsuwa .
Wani sanyin daɗi ne ua baibaye zuciyar Faruk yayin da yake sake tabbatarwa zuciyarshi tabbas Zee Luwai ita ce ta dace da shi ba Zainab ba, wacce sam bata jure ɗaukar buƙatunsa hasalina yana kallonta a ƙasa da shi sosai, sai daga baya idan ya kalleta ya ga yanayinta yake tunanin yanda aka yi idonshi ya rufe ya zaɓota a matsayin mata, na ɗaya dai sam baya son mace saliha kamarta, yana tsananin son mace marar kunya kamar dai Luwai wacce zata biya mashi dukkanin buƙatunshi ba tare da taji nauyi ko kunyarshi ba, sannan gana son mace me zafin nama kamar dai shi, bayason sanyin jiki da rashin kazar-kazar. sau dayawa idan ya kalli Luwai yakanganta a matsayin macen da ta dace da ra'ayinsa, yana soyayya sosai, amma ya raina wacce Zainab ke bashi saboda batada zafin nama kuma tsoronta yayi yawa.
Ire-iren waɗannan tunanukan zuciyarshi taci gaba da ingizashi akan lallainya jajirce wajen mallakar Luwai domin ya morewa ƙuruciyarsa.
Da ace Faruk yasan bom ɗin da ke baibaye da rayuwarshi da Luwai da koda wasa ba zai yadda ya kalleta ba bare zaren ƙaddara ya ja shi zuwa gareta......✍🏻
AIKI YAYI MIN YAWA WALLAHI BAN SAMU DAMAR YIN TYPING SOSAI BA, AMMA IN SHA ALLAH ZUWA GOBE ZAN YI ƘOƘARI INYI TWO PAGES🙏🏻🙏🏻🙏🏻
MARYAM STAR
Wa---me only
09112636748
💗𝙎𝙄𝙍𝙍𝙄𝙉 𝙎𝙊💗
𝘽𝙔
𝙈𝘼𝙍𝙔A𝙈 𝙎𝙏𝘼𝙍⭐
𝙅𝘼𝙅𝙄𝙍𝙏𝘼𝙏𝙏𝙐 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎𝙊𝘾𝙄𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉💪.
𝙋𝘼𝙄𝘿 𝘽𝙊𝙊𝙆
BOON ONE
17 & 18------------- Yauma kamar kullum ina zaune zugun ni kaɗai a gida bayan na gama ƙananun aikace-aikace na, nice harda firfito da kayan kitchen na wanke su, bayan na wanke na gyara musu zama, haka kawai nike jin ina son fita, dan zaman shiru ya isheni hakanan, gashi babu wutar nefa bare ko kallo inyi dan in rage zafi, hakanan na ɗauki ƙaramar wayata na danna lambar Sadaukinah, harta ƙarashi ringin ba'a ɗauka ba, hakan ya saka na tura mashi ƙaramin saƙo akan ina so zan leƙa gidan Maman Afnan maƙociyarmu, ban jira ya dawo min da reply ba na saka hijabi tare da zira takalma na ɗauki mukullai na fice.
Unguwar cike da ta ke da matasa da kuma ƙananan yara kasancewar ranar juma'a, sai hada-hada mutane ke yi ga hayani wacce baka raba lungunmu da ita, kaina a ƙasa na zagaya zuwa baya gidan Maman Afnan.
"Assalamu alaikum."
Ma faɗa lokacin da na zura ƙafata cikin gidan."
"Ah, ahh ahh, wata sabon gani lalle da zuwa marabanki."
Maman Afnan ta faɗa ranta fes fa ganina.
Zama na yi akan tabarma da ta shimfiɗa min, nan muka shiga gaisawa.
"Amma dai Zainab ɓatan hanya kika yi ko?."
Ta faɗa da alamun tsokana.
Da fara'a a fuskata na ce.
"Wallahi ko a'aah nazo miki marice ne dan mu gaisa kwana biyu ban shigo ba."
"Allah sarki Zainab ina so muyi mutunci amma da dukkan alamu mijinki baya son mutane, dan kuwa a satin da ya gabata na aiki Afnan ta kai maki wasu riguna da nayi ina so kiyi min beat amma da taje ta kwankwasa sai shi me gidan naki na buɗe, ya tambayi mi tazo yi nan ta faɗa ma shi komi abinki da yarinta madadin ta ce aikota aka yi, aiko ya zazzare ma ta ido ya korota bayan ya tsoratata akan karya sake ganinta."
Murmushin yaƙe kawai na yi, dan nasan indai Sadauki ne zai yi abin da yafi haka ma, ina son mu'amala da Maman Afnan amma ƙiri-ƙiri ya hanina, bama da ita kaɗai ba kaf matan unguwar baya bari in shiga sabgarsu kullum ina gida ni kaɗai kamar mayya.
Sosai muka sha fira ni da ita, tana ɗinki ni kuma ina kama ma ya sanya stons, ban sannlokaci ya jah ba sai da naga mijinta da bansan yana gidan ba ya fito yana alwala, ba shiri na miƙe a hanzarce tare da yi ma ta sallama na fito gabana na faɗuwa, ashe na mance key ban ɗauko ba sai bayanda na fita ta lura da key ɗin sai ta roƙi mijinta akan yabawa yaro a waje ya miƙomin.
Ina shawo kwana gabana ya yanke ya faɗi, wani irin gumi ya shiga tsatstsafomin daga ƙofofin gashin jikina, sai kawai na ja tunga na tsaya ina haɗiyar yawu ganin Faruƙ tsaye fuskarshi a tamke babu alamun fara'a, a daidai lokacin da idanuwa suka sarƙafe cikin na shi, nan take cikina ya murɗa, kafin inyi wani yunƙuri mijin Maman Afnan ya shawo kwana tare da tsayawa kusa da ni fuskarshi a sake ya miƙo min mukullin yana faɗin mance shi na yi acan, da kyar na ƙaƙalo murmushi sannan na yi ma shi godiya na fara takawa sannu a hankali ina tunkarar Faruk tashin hankali na sake baibaye ni.
Bai tsaya komi ba ya warci mukullan daga hannuna lokacin da na isa wajen, a zafafe ya buɗe gidan sannan ya shiga da mashin ɗinsa, a sanyaye nabi bayanshi ina faɗin.
" Sannu da dawowa Sadauki, nahhhh."
Maganata ta tsaya cak sakamakon wani dalellen mari me gigita kwanya da ya sauke min, ban gama dawowa daidai ba ya sake dauke ni da wani marin ta ɗayan ɓangaren, nan take gani da jina suka tsaya, duniyar ta yi min ɗif kamar babu kowa, ƙuafta idanuwa na fara yi ko zan samu su dawo daidai amma abin yaci tura, can sama-sama na dinga jiyo bala'in da Faruk ke yi, ba tare da nasan na ƙure shida kallo ba a zahiri ya kuma sauke min wani azababben marin, nan take na yi ƙasa tare da kwalla ihu dan wallahi na maru bakin gwargwado, kafin in rufe bakina kawai sai naji saukar duka daga ta ko ina a jikina, nan na shiga ihu ina neman ceto tare da magiya, amma Faruk sam bai sauraramin ba sai da ya gaji dan kanshi, izuwa lokacin na gaji da ihun dan muryata da take siririya ta disashe, haka ya tsallakeni yai ficewarshi yabarni da zubda wahayen azaba.
Tun da uwata ta kawoni duniya ban taɓa jin azaba makamanciyar wacce nike ji a yanzu ba, ko ina na jikina raɗaɗi kawai ya ke yimin, ƙarin azana du inda na taɓa sai inji wani abu kamar ruwa, ashe dai jikinane ya farfashe yana zubda jini, da rarrafe na shiga ɗaki, kai tsaye na nufi gaban miro, ƙafafuwana na ƙyarma haka na tsaya ina ƙarewa halittar jikina kallo, cikin abin da bai gaza minti goma ba Faruk ya canza min kammani, idona ɗaya ya kumbura, bakina ya fashe ga shatin duka nan ɓaro-ɓaro, lokacin da na cire rigata sai da na rintse ido, jikina yayi burɗin-burɗin wasu wajajen du jini, sabon kuka na fashe da shi, na ɗauki lokaci ina yin kuka, kafin daga bisani na rarrashi zuciyata na lallaɓa na shiga bayi nai wanka, wankanda ina yinshi ina kuka saboda azabar da nike ji idan ruwa ya taɓa jikin, a daddafe na gabatar da sallah itama a zaue na yi ta, wani irin azababben zazzaɓi da ciwon kai ne yai min dirar mikiya, a inda nai sallah na kwanta hawaye na bin kuncina, nan take wani tunani ya faɗo min, tunanin da abaya idan wani yace zanyi shi tsaf zan ƙaryata hakan, tunani akan rayuwata ta baya abune da sam bana lissafi da shi a halin yanzu, acewata na rigada na rufe wannan shafin na buɗa na gaba, ba tare da sanin mi gobe ta tanadar min ba na yanke hukunci akan abin da zuciyata ke kokonto akanshi.
ABUJA.
Fuskokinsu ɗauke da murmushi kowa ke aika lomar dadaɗɗan girkin da Mom Hajara ta ɓata lokacinta wajen shiryawa domin su, idan ka cire Mom Kubra da Meenal waɗanda ke yawan haɗa ido suyiwa juna signal idan su Daddy suka yi wani abu, koda wasa Muneeb bai kalli sashen da Meenal ta ke zaune ba, duda yanda ta ke yin tsagal ta tsoma musu baki a cikin firarsu, abin da bata saniba su duba bata ita suke ba, hasalima Mom mugun haushinta take ji, dan bata mance yanayin da suka zo gidan ba.
Bayan sun gama ne suka koma farlo suka ci gaba da firarsu gwanin burgewa Mommy Kubra da Meenal sai ido kawai suka saka musu kwanin takaici, da farko Mommy Kubra ta so ayi firar da ita, sai de idan ta haɗa ido da Daddy tana shan jinin jikinta kasancewar dallareriyar harara me cike da gargaɗi yake aika ma ta, daga baya ganin abin bana ƙare bane ya saka ta yafitar Meenal sannan ta tashi tare da yi musu bankwana, a maimakon Meenal itama tabi bayanta sai ta tsaya ƙerere tare da faɗin.
"Sweet ka taso mu koma gidanmu na gaji da nan, ni gida nike son zuwa." ta yi maganr tana wani narkewa gami da shagwaɓewa ta shafe idanuwanta da toka tai kamar bataga su Daddy ba.
Fuska ɗauke da murmushi Muneeb ya ɗago ya kalleta sai kuma ya tashi tsaye tare da kama hannunta duka biyu ya riƙe murya a tausashe ya furta.
"Oh Meenal wane gidan kuma kike magana, bayan kin tabbatar min da bakya son can gidan, zan sauƙaƙa maki zama a cikinsa tunda bakya sonshi kije na sawaƙe maki aurena na sake ki saki ɗaya, idan kin samu miji kiyi aure, ina yi maki fatan alkairi."
Yana gama faɗin hakan ya koma ya zauna yanajin yanda zuciyarshi ke tsananin suya du lokacin da yai ido huɗu da Meenal, ayanzu da ya sawaƙe ma ta aurenshi sai yake ji shi sakayau wannan dabaibayin ya sake shi.
Mommy da Daddy ƙuri suka yiwa Muneen wanda ya maze kamar bai yi komi ba.
Da baya-baya Meenal ta dinga tafiya yana girgiza kai, kafin ta juya a guje ta haye bene tana sakin kuka.
Daddy ne ya buɗe baki zai yiwa Muneeb faɗa akan abin da ya aikata, sai yayi saurin taryeshi ta hanyar faɗin.
"Please Daddy iya yau kaɗai ku barni in rage nauyin zuciyata, yarinyar nan sam bata sona, hasalima a gabanku take faɗin ba zata zauna da ni ba, ni kuma shine na sawaƙe ma ta aurena dan gudun matsalar da kanje ta dawo."......✍🏻
PLEASE SHARE, LIKE AND COMMEND
MARYAM STAR⭐
ƳAR BAIWAR JAJIRTATTU......✍🏻
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DCWTxqKWEXeAryfnr4FVE0?mode=gi_t
💗𝙎𝙄𝙍𝙍𝙄𝙉 𝙎𝙊💗
𝘽𝙔
𝙈𝘼𝙍𝙔A𝙈 𝙎𝙏𝘼𝙍⭐
𝙅𝘼𝙅𝙄𝙍𝙏𝘼𝙏𝙏𝙐 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎𝙊𝘾𝙄𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉💪.
𝙋𝘼𝙄𝘿 𝘽𝙊𝙊𝙆
BOON ONE
19 & 20--------------- "Sakin aure halal ne, amma halal wacce ke girgiza al,ashin ubangiji, Allah shi ya halasta saki amma baya son shi, da haka ina tausar zuciyarka Muneeb ka dinga haƙuri da rayuwa kar ka sake maimaita irin kuskuren da ka yi a baya."
Daddy yayi maganar da tausasawa, jikin Muneeb a sanyaye yake kallon mahaifin na shi, yayinda wani yanayi me wuyar fassara ya lulluɓe fuskarshi.
Dafa kanshi Mommy ta yi tare da faɗin.
"Tabbas ka yi sauri wajen yanke hukunci, amma babu komi Allah yasa hakan shi yafi alkairi, amma please ka rage gaugawa cikin lamurranka ka ji ɗan albarka, Allah ya albarkaci rayuwarka."
Ta yi maganar fuskarta ɗauke da murmushi, yayinda ƙasan zuciyarta ke cike fal da jin daɗin hukuncin da Muneeb ɗin ya yanke, dan kuwa ta dawo daga rakiyar baƙin hali irinna Meenal.
Barci ne me cike da azaba gami da raɗaɗi yayi min dirar mikiya, ga zazzaɓi da ya sake saukomin me zafin, cikin ƙanƙanin lokaci na fita a hayyacina, har zuwa lokacin Faruk bai dawo ba, ni kaɗaice a gidan kamar mayya, a wannan daren na ɗanɗana azaba me radaɗi, zuciyata ta yi kwanan ƙunci, gangar jikina tayi kwanan jinya da ciwo, kwanyata ta yi zurfi wajen tunanin can baya, rayuwa me daɗi wacce na guda da ƙafafuwanah, rayuwarda na juyawa baya badan wani dalili ba, rayuwar da na kira da marar amfani a gareni, sai yanzu dana samu irin rayuwar da nike buri zuciyata ta nutsu, sai kuma ƙullin matsaloli ya kwance min, ban san a wane yanayi nike jin Faruk ba a halin yanzu, sai de ina ji kamar na gama yi ma shi uziri, bazai canza ba kamar yanda nike fata, sam SIRRIN SO bazaiyi a iki a kanshi ba, baudaɗɗen halinshi yayi yawa, shi mutum ne me wahalar sha'ani da mu'amala musamman ga mutane irina, tabbas Faruk bai face da ni ba sam...
FARUK
Ranshi a mugun ɓace ya baro gidan bayan ya rufe ta waje harda saka kwaɗo, a maimakon ya nufi madallaci ya gabatar da Sallah sai kawai ya ja mashin ɗinshi yabar unguwar a mugun fusace.
Bayan isarshi inda zuciyarshi ke marari ya daɗe akan mashin ɗin yana tunani kafin daga bisani ya bi umarnin zuciyarshi, wayarshi ya lalibo a aljihu ya dannawa lambar da ya yi saving da LUWAI kira, sai da ta kusa yankewa sannan akan ɗauka, murya a yangance ta ce.
"Hello Zumanahhh."
Sai da ya rumtse ido jin yanda sautinta ya yi ma shi dirar mikiya a ƙoƙon kanshi, sassauta muryarshi ya yi sannan a hankali ya furta.
"Ina ƙofar gida kiyimin sallama da Abba idan yana nan ina so zamuyi magana." bai jira cewarta ba ya yanke kiran tare da furzar da huci daga bakinsa.
Tun daga nesa ya fara jiyo sautin muryar Abba ya na faɗin.
"Ko wane ɗan ta kazar ubanne ke nemana da mangariba sakaliya, kai mutame anyi ƴan jakar uba." ya na yin tozali da Faruk zaune akan mashin ya fara sakin fara'a tare da ƙarasawa da sauri kamar zai duƙa ƙasa ya ce.
"Ah Faruk na Manzon Allah, yau kaine tafe, ikon Allah ikon gaske, kamar kasan nemanka nike yi ido rufe wallahi." nan ya fara zuba kamar ƴaƴan kanya ba tare da ya bari ko gaisawa sunyi ba.
"Abba barka da wuni."
Faruk ya katseshi daga surutun da ya ke ta faman yi ba kama hannun yaro.
"Lafiyau ɗannan ya kake ya kwana biyu bamu gana ba tun watan shekaran jiya, da yake na je Legas kwadago, kaganninan babu abin da na damo sai kayan takaici dana taras a gida, yara du sun ida kangarewa sun zama karuwai masu lasisi, aiko na naɗe hannun rigata na koma gefe na zauna nace su ɗauki nauyin gidan dan ni bazan iya cida waɗanannan kitika-kitikan ƴaƴanba wallahi."
Haka Abba yai ta surutai maras kan gado daga baya da surutun ya ishe Faruk a taƙaice ya ce.
"Abba dama na zo ne akan zancen aurena da Zainab ina so zan turo magabatana a tsaida lokaci bana so aja lokaci me tsawo ina so a haɗe bikin da bikin buɗe sabuwar plaza ta, watanni uku nike so a saka sai kuyi ƙoƙarin zaunar da ita gida tayi istibra'i daga zarar ta gama sai kawai a ɗaura auren.
Aifa abin nema ya samu, nan Abba ya ja da baya ya rangaɗa rangaɗeɗiyar buɗa kamar wani ɗan TikTok wai shi Abba Bakaji.
Faruk bai bi takanshi ba ya fito kuɗi masu ɗan kauri ya damƙawa Abba, nan take Abba ya yi hucking ya shiga zare idanuwa gami da washe baki, zai fara jero godiya kenan Faruk ya dakatar da shi da faɗin ba komi ya je kawai.
Waya ya ɗauka ya kira Luwai, a taƙaice ya ce da ita " Ki fito mu ɗan je gidana zamuyi magana, sauri nike yi ba lokacin ɓatawa." yana gama faɗin hakan ya kashe wayar gami da kunna mashin sannan yai juya yana jiran zuwanta, wani malolon takaici ne ya tokare zuciyarshi ganin yanda Abba ya ɗakawa mazaunan Luwai duka da suka haɗu a ƙofar gida, saurin juyar da kanshi ya yi tare da tabbatarwa kanshi dolene ya aureta ya killaceta ta zama tashi shi kaɗai.
Bai yi wata-wata ba ya ja mashin ɗin da tsananin gudu bai tsaya a ko ina ba sai a wani ƙaramin hotel, kai tsaye ya biya kuɗin ɗaki ɗaya na kwana biyu, ya ja hannun Luwai suka shiga daga ciki.
Tun da suka je ɗakin ya ke ta morar albarkar jikinta yana rage zafin zuciyarshi, ba shi ya rabu da ita ba sai tsakiyar dare, ahaka suka kwanta barci babu sallah bare salati ko tsoron mutuwa ta riskesu a wannan yanayin basa yi.
Kwana biyu cir suka kwashe a Hotel ɗin sannan Faruk ya mayarda Luwai gida bayan ya kora ma ta jawabi akan plan ɗinshi na aurenta, da kuma tabbatar ma ta da yayi akan zai saka matakan tsaro a unguwar saboda ita.
Bai tuna da wa ta aba ba wai ita Zainab sai bayan da ya tunkari hanyar gida, a maimakon yaji bai kyautaba a zuciyarshi, sai ma haushinta daya dawo sabo fil a zuciyarshi, hoton yanda ta sakarwa maƙocinsu Baban Afnan murmushi tare da amsar wani abu a hannunsa ya tsaya raɗau a kwanyarsa, nan take ya koma ainahin Faruk ɗinshi me zafin rai, wannan shauƙi da farin cikin du suka gushe daga kan fuskarshi.
Fuskarshi kamar wanda aka turowa saƙon mutuwa haka ya haɗe gabas da yamma lokacin da ya lalubi key ya buɗe kwaɗon da ya rufe gidan da shi, shiga yayi tare da kullewa ta ciki sannan ya ajiye mashin ɗinshi a zaure.
Wa ta iriyar mummunar dokawa gabana yayi, lokacin da na hangi shigowar Faruk gidan, nan da nan jikina ya soma rawar mazari wani irin tsoro da razani ya baibaye ni, da kyar na tattaro kalmar.
"Sannu da zuwa Sadauki." wasu marayun hawaye na gangarowa daga kuncina, kwana biyu cur na share a kwance banda lafiya ga kumburi da jijina yayi musamman inda ya dakeni, gashi babu ƙwayar magani ko ɗaya a gidan bare insha, a yaune na lallaɓa da niyar inleƙa in samo koda yaro ne ya amso min maganin amma mi ina zuwa na ji ƙofar gam a kulle ta baya, hakanan na janyo marayun ƙafafuwa na dawo ɗaki, ga yunwa da ke saƙalar ƴan hanjin cikina, da kyar nike iya shan ruwan zafi, cikin kwanaki biyu rak na zabge na jeme du na fice daga hayyacina, a lissafina bai kyautu ace du irin tattalin so dakulawar da nike yiwa Faruk zai iya saka min da haka ba, nayi tunanin zai kasance a sahun farko cikin mutanen da zasu bada shaida akaina, abin da yayi ya matuƙar karya min zuciya nan take da sare da lamarinsa, duka abune wanda sam ba saba da shi ba, duda kasancewa abaya nayi rayuwar tozarci da wulaƙanci, duka abune da tun tale-tale nike tsananin tsoro, ko a makaranta bana laifin da za'a dake ni, ban hango abin da zai saka Faruk ɗaga hannu ya dake ni ba, dan kuwa bakin ƙoƙari ina yin abin da ya dace.
Dogon tsaki ya ja tare da wuce ni ya shiga bed room bai amda sannu da zuwan da na yi mashi ba, a sanyaye na saka siririn hannuna na sharce hawayen idona sannan na rakuɓe kamar wa ta baƙuwa, ya ɗauki lokaci me tsawo bai fito ba, ni kuma hakanan na ji ina mugun shakkarshi, sai na kasa tashi imbi bayanshi, ashe gogan zama ya yi yana jiran shigowata, ganin ban shiga ba kuma kamar ma bani da alamar shigar ya saka ya kwallamin kira a harzuƙe.
"So kike inzo nan in datta ke?."
Jikina ya ɗauki ƙyarma da hanzari na miƙe na shiga tare da gurfana a gabanshi kamar me neman gafara wasu sababbin hawayen na kwaranya daga fuskata.
"Uban mi aka yi ma ki da zaki zo kina yimin kuka, bana son munafurci fa😡." yayi maganar a zafafe kamar zai kawo min duka.
Da sauri na ja da baya sannan na ce.
"Dan Allah ka yi haƙuri wallahi bani da lafiya." ina aje zancen wani sabon kukan ya sake kubce min du yanda na so tsaida shi amma abin ya ci tura.
Kallona yayi na ƴan mintuna kafin ya tashi ya shiga toilet, ban tashi daga wajen ba har ya fito a same ni, anan zaune, baice da ni komi ba ya saka kaya maras nauyi sannan ya dube ni bayan ya feshe jikinshi da turare.
"Idan kinyi girki zubomin yunwa nike ji."
Cikin disashiyar murya na ce.
"Yau kwanana biyu banci komi ba tea kaɗai nike sha, babu cefane a gidan kuma dama na gaya maka tun ranan mai ya ƙare."
Dafe kanshi kawai ya yi, dan kwana biyun da yayi bayanan sosai yai missing girkina hakanan ya ke daurewa ya ɗan cakala.
Tashi yayi ya fita a ƙafa, bai jima ba sai gashi ya dawo da cefane a hannunshi da galan ɗin mai, bai ce da ni komi ba ya aje min sannan ya nemi waje ya zauna, jiki na rawa na tashi nakai kayan kitchen na soma kiciniyar ɗora girki, duda rashin ƙarfin da bani da shi, hakanan nike yi ina hutawa, dan nima ina buƙatar abincin ina jin yanda nauyin jikina ya ƙara raguwa.
KUYI JOININD GROUP DOMIN TATTAUNAWA AKAN WANNAN NOVEL ƊIN, ƘOFA A BUƊE TA KE
👇👇👇👇👇👇
https://chat.whatsapp.com/DCWTxqKWEXeAryfnr4FVE0?mode=gi_t
MARYAM STAR⭐
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DCWTxqKWEXeAryfnr4FVE0?mode=gi_t
Follow the 🌹MARYAM STAR 𝐶𝐻𝐴𝑁𝑁𝐸𝐿✍️📚📙✏️ channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb5xdoy2975BcTM5m133
💗𝙎𝙄𝙍𝙍𝙄𝙉 𝙎𝙊💗
𝘽𝙔
𝙈𝘼𝙍𝙔A𝙈 𝙎𝙏𝘼𝙍⭐
𝙅𝘼𝙅𝙄𝙍𝙏𝘼𝙏𝙏𝙐 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎𝙊𝘾𝙄𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉💪.
𝙋𝘼𝙄𝘿 𝘽𝙊𝙊𝙆
BOON ONE
LAST FREE PAGE
Jolof ɗin