Share this page
5 / 5
shikafa na dafa, a daddafe na idasa girkin dan jiri nike ji, babu ɓata lokaci na gabatarwa da Faruk na shi, nima na zuba nawa daban ina jin du wani saboda ban saba raba mana kwano ba, ko rabi banci ba abincin ya fita a kaina, hakanan na haƙura na aje na sha ruwa sannan na koma na kwanta wani dabon barci yayi gaba da ni. Can cikin barcina na dinga jin muryar Faruk a ɗan kausashe yana magana, da alama waya ya ke ji, ban nuna na farka ba nai shiru tare da sauraren abin da yake faɗi. "Ai har mun tsaida magana da mahaifinta, so nike ayi komi a gama cikin wata uku, ina so lokacin ya kama lokaci ɗaya da taron bikin buɗe plaza." Banji mi aka ce a wancan ɓangare ba sai ji na yi ya sake faɗin. "Kudai Mama ku sanya albarka kawai dan gaskiya banajin zan iya haƙura da wannan auren tunda na kwallafa raina akan yarinyar ina son ta sosai wallahi." Daga can Mama ta ce ranta a mugun ɓace. "To Faruƙu ka je kayi aure lafiya, amma dai sam baka kyautawa Zainabu ba, yarinya me nutsuwa da hankali, ace aure ko shekara bai rufa ba har ka ƙara ƙirƙirar ƙarin aure, imbanda abinka ai ka bari ta haihu ko ɗaya ne, to shikenan ka je Allah yayi albarka ka gaisar da Zainabun." ta na gama faɗin hakan ta kashe kiran ba tare da ta jira cewarshi ba, sai ta soma mitar irin baƙin nacin Faruk idan ya so abu. "Wallahi Mama tausayin yaya Faruk ni ke ji, so yake ya je ya aurowa kanshi masifa, na rantse babu abin da Anty Sabrah ta rageshi da shi, bakiga yanda ta ke kulawa da shi ba, gata bata da wa ta damuwa baiwar Allah." Farida ta yi maganar fuskarta aɗan shagwaɓe. "To ya zanyi da shi Farida, kin san halinshi idan ya saka abu gaba baya ji baya gani, kin mance yanda mukasha daga da shi lokacin aurenshi na farko, nidai babu ruwana ya je yayi aurenshi tunda shi baya ɗaukar shawarata." " To Allah ya kyauta amma yaya sam baida hali wallahi, sai zafin kan tsiya. ⭐⭐⭐ Zaune ta ke acikin mawuyacin hali, duk jikinta shadin duka ne, ga wani irin haske me kashe ido da ke fita daga jikinta, wasu manyan ƙarfafan igiyoyi masu tsananin ƙwarine zagaye da ita, wanda su suka hana shi isa inda take durƙushe ta na kuka, yana ji yana gani ya kasa taɓuka komi illa zuba ma ta idanuwa da yayi. A firkice ya farka tare da kwalla kiran " SABRAHHHHH." du ya haɗa gumi kamar wanda yai tseren gudu, da sauri Mommy da Daddy suka inda ya ke su na tambayarshi ko lafiya, amma ina baya iya magana saboda kukan da ya kubce ma shi, a cikin kukan ya ke faɗin. "Na shiga ukuna mi na aikata haka da alhakin baiwar Allah ya hanani sukunni, Mommy Daddy wallahi ita ce, ita ce wallahi Sabrah ce nike gani a cikin barci cikin ƙunci da damuwa, please Mommy kuyi wani abu akai gab nike da haukacewa idan ban sadu da ita na goge laifina a wajenta ba, na tsani kaina Daddy." Muneeb yai maganar yana kuka kamar ƙaramin yaro, kallon kallo Mommy da Daddy suka tsaya yi, yayinda zukatansu sukai babu daɗi da jin abin da yaronsu mafi soyuwa a garesu ke faɗi, cikin muryar rarrashi Mommy ta ce. "Ka yi haƙuri Muneeb ka cire tunaninta daga ranka, ta tafi ba kuma zata sake dawowa ba kamar yanda ta faɗa, ya kamata ka aje komi ka fuskanci rayuwarka ka manta da jiyanka ka fuskanci gobenka, na san Sabrah macece me afuwa da yafiya ta daɗe da yafe maka laifin da ka yi ma ta, ya isa hakanan ka nutsu dan Allah." "Mommy bazan iya nutsuwa ba alhalin ban san halin da na jefa ƴar mutane a ciki ba, ina ji na tsani kaina Mommy na tsani kaina da nayi amfani da SIRRIN SO na cutar da baiwar Allah bata ji ba bata gani ba, bazan samu nutsuwa ba har sai na dangana da ita na ji ta furta kalmar yafiya da bakinta agare ni, Mommy lokaci yayi da zan fuskanci gaskiya in daina ƙaryata zuciyata, na shirya tsaf wajen gyaran kuskurena saboda haka zan shirya tafiya gobe zuwa KATSINA." MEENAL "Kin yi nasara Mommy Kubrah, kin yi nasara wajen buga game ɗinki akaina, yanzu lokacine da nima zan buga nawa wasan, Muneeb ya sake ni a yau kuma a yanzu ba jimawa, ki jira amsar naki sakin kema zuwa gobe, zan je in tone sirrin da kika binne tsawon lokaci, zan bankaɗo dukkanin abubuwan da kike aikatawa a ɓoye kina lulluɓe su da yaudarar SIRRIN SO, a yanzu ta ki ta riga da ta ƙare ki fara ƙidayar sauran awannin da suka rage ma ki, ki zama bazawa ma'ana tsohuwar maya ga Alhaji Sa'id gobe zanyiwa KATSINA tsinke, zan fara tonon komi daga tushe." Wa ta iriyar dokawa zuciyar Mommy Kubrah ta yi, lokaci ɗaya zufa ta baibaye ilahirin sassan jikinta, tashin hankali ya rifto ma ta nan take, cikin kyarmar murya ta ce. "Mi...mii....miiii kike nufi Meenal ban gane ba ki warware min please kaina ya ɗaure." "Hummmm kina wasa Kubrah, kina wasa da kaidin Meenal, karki tsaya ɓatawa kanki lokaci dan banda lokacin biyewa shirmenki, kamar yanda kika ji na faɗa MUHAMMAD SA'ID NAIRA wa to Muneeb ya sake ni a yanzu, kema ki jira naki sakin zuwa gobe kafin faɗuwar rana." Tana gama faɗin hakan ta juya ta fice ranta a mugun ɓace. LUWAI "Zainabu ƴar halak, wato shigowarki cikin rayuwata ya zama alkairi dan haka ki shirya babu ɓata lokaci zuwa gobe mu dira a KATSINA ki kirawo shi wannan yaro ɗan arziƙi Faruƙu ya iske mu can sai ayi maganar auren ki da a can wajen danginki, ai nafi kowa murna da farin cikin samun wannan yaro da kika yi a matsayin wanda zai aure ki, dan wallagi yanda kika yi wannan lalacewar banyi tunani zaki auru ba, amma dai shikenan ko ba komi mun rage yawa idan kika tafi, yanzu dai kowa ya haɗa kayansa zuwa safiya zan samo mana shatar mota har nan ƙofar gidan dan Faruƙu bawan Allah ya cika min lalita ta taf da canji." YANZU ASALIN LABARIN SIRRIN SO ZAI FARA. WAI SHIN MU ABBA, MUNNEB, MEENAL ZASU JE YI A KATSINA, KUMA WACECE SABRAH, MICECE MAKOMAR ZAINAB A GIDAN FARUK, SHIN FARUK ZAI AURI LUWAI❓❓❓ KU KASANCE TARE DA NI. MARYAM STAR ⭐ ƳAR BAIWAR JAJIRTATTU DAN JIN YANDA ZATA KAYA. END OF BOOK ONE SAI MUN GAƊU A BOOK TWO KARKU MANTA WANNAN LITTAFIN NA KUƊINE AKAN NAIRA 300 KACAL ZA KI MALLAKI NAKI 09112636748 ONLY WATSAPP BISSALAM🙏🏻👋👌🏻💗🌹 An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 5 of 5