Share this page
3 / 5
haka bana son ganin fararen idanuwanki sun koma ja kinji? nace to na dakko mishi sallaya sabuwa na tuno duk juma'a in Allah zai je masallaci ya kan shigo dakin mama ita kuma sai ta dauki turare ta fesa mishi gami da mishi rakiya bakin kofa nan nima na dauki turare na fesa mashi yace nagode na mika mashi sallayar ya amsa na biyo shi har bakin kofa ya juyo me zan roka maki?na juya baya don kunya nace 'ya'ya na gari naji yayi jim bai ce komai ba na juya sai ya kago murmushi yace har da kishiya ko?na daure fuska nace a'a yayi murmushi to sai na dawo. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 Kafin ya dawo na hada mishi salat, nayi salla na sake wata kwalliyar da pakistan irin na India sky blue sun zauna tsam na zuba yan kunne da abin hannu tamkar ba Indiya yan kudancinsu marasa fari sosai ina jin tsayuwar mota na leka ta window dina su uku ne da sauri na daure gashi na tsam da ribo mai kalar kayan gashina ya sauka abaya ina isowa falona shima yana shigowa ya dubeni a ranshi yace yarinyar nan zata kasheni da salon gayunta ya jawoni jikinshi kin fi dazu kyau nace na gode yace zamu samu abincin mutum uku?nace sosai ma yace yauwa 'yar albarka a kawo mana ya fita na kai musu na koma na kawo masu drinks sannan na gaidasu, dayan Bello ne biyun kuma ban sansu ba yace shiga ciki ki kirawo Mimi kice tazo da dady ga bakina nace to na shiga na zata Haj tana nan ashe ta tafi na gaya mata na fito na koma daki,da zasu tafi yai min text wai nazo zasu tafi amma na rufe mishi gashina su daina ganin mashi, nayi murmushi gyalen kayan na warware na rufo muka yi sallama,ya tafi raka su,ya dawo ya sameni inna ma babana waya, ya jawoni jikinshi nace ma babana baba ina son kudi yace nawa?nace ko nawa ne ka bani na gode yace to direbana zai kawo maki ina mijin naki na juya na dubeshi da zan ce ga shi nan sai na ga ya sha mur sai nace baya nan to in ya dawo ki gaishe shi nace to sai anjima na gode cikin fargaba na dube shi ya mike zai fita na ruko shi yaynmu menene?harara ya sakar min da sauri na sakeshi ya fita na koma na zauna nace to mena mishi haka na cigaba da zama sukuku .Karfe hudu ina kicin, tuwon shinkafa da miyar agushi nayi sai kaza dana gasa,kunun aya da dabino da na amfani na sannan na kaima Anty Mimi da mai gadi nasu sauran na kwashe na tafi dashi kicin din dakina sai da na yi wanka sannan na yi sallar magriba ina zaune har akayi Isha'i na idar siket na sa na Jeans da yar riga mai hannun singleti ta dameni sosai na canja salon fakin din gashina na zauna a falona cikin fargaba, takwas da rabi ya shigo da sallama ciki ciki ya zauna na dubeshi har ynxu fuskarshi a daure take na daure nace sanu da zuwa, bai amsa ba na shirya mishi abinci a gabanshi yace in kwashe ya koshi na sa hannu na dafa kirjina na tsura mishi ido a raina nace to wai shi wannan wane irin mutumi ne? ya dubeni kwashe nace,na matsar da kayan gefe naje na durkusa a gabanshi bisa gwiwoyina nace yayanmu don Allah sanar dani abinda nayi maka tun kafin ubangijina ya soma fushi dani wllh ba zan sake ba pls!ya dubeni fuska tamke me yasa kika ce babani ya baki kudi? me yasa ba zaki tambaye ni ba? menene wanda kike so ba zan iya miki ba gaya min? nace ok daman wannan ne? to dan Allah kayi hakuri dama ba wai zanyi wani abu da kudin bane saboda kawayenmu na makaranta da suke zuwa shi yasa ina son na dan ringa basu na mota kuma Babana yace kar na tambaye ka kudi na tambayeshi, to amma kayi hakuri ba zan sake ba kaji?na kawo maka abincin?kaji don Allah um ni ya zuba min ido yana kallona na kifta idona na baka a baki?na fada ina dubanshi ya harareni na runtse idona sai hawaye na tashi zan shige bedroom ya jawoni jikinshi to na hakura yi shiru kinga zaki bata min kwalliya baki bari nace kinyi kyau ba, nayi lamo kan jikinsa yayi mani magana cikin kunne tashi ki bani abinci my Dear tashi,na tashi nayi ina yar shgwaba ta na soma bashi abinci yana ci bayan ya gama ne muka tarkata sai master bedroom kai yaynmu karshene ya iya soyayya mai ban mamaki daran ranar ya min abubuwan da na san yes ni mace ce kauna zalla mai tsayawa a rai. Washe gari sai ga Haj Yaya ta kuma zuwa lokacin ma baya gida tana ta masifa har ya dawo tace su tattara su koma England tunda yace jira yake ta haihu ai ta haihun yace Haj kinga dan bai yi kwari ba don Allah ki bari ko wata yayi tace yayi acan dole suka bari akan sati maizuwa zasu tafi wannan satin dai mun kwashe shi ne cikin soyewa,bana manta ranar lahadi ana gobe zasu tafi ba kowa sai ni kadai yaynmu ya tafi ya kai Anty Mimi gidansu sallama ina zaune a falona abin duk yabi ya dameni yanzu in yaynmu ya tafi shikenan ko sai yaushe zai dawo oho?banji shigowar mutum ba sai ji nayi an kama min gashi ta baya zan yi ihu sai naji yaynmu yace ke sarkin tsoro ni ne tunanin me kikeyi ne ban rufe ba nace tunaninka mana in ka tafi ko sai yaushe oho?ya zauna zanzo da zarar na samu sukuni tunda na dade,nasan zan dan kwana biu dama sun dameni da waya karki damu mun gama magana da Alhj gobe Haj Maska zata zo sai ki gyara mata dakin kusa da kicin ko,nayi shiru duk ya damu na kula so yake yaga na daina damuwa ya jawoni yana min wata magana cikin kunne na mike nace a'a yace ni ko?nace eh ya kai hannu zai kamo ni na ruga ya biyo ni muna ta zagaya kujerun babban falon na gaji inata dariya na fada kan doguwar kujera ya zauna a jikina nace wayyo zaka kasheni yace to kin yarda?nace na yarda pls ya dagani ya dorani a jikinshi hannuwanshi yasa ya balle maballin gaban rigata ya sa baki yana aikin....kungane dai,na kuma kwacewa zan gudu yace pls kinga daga yau bana nan zanyi missing dinshi nace to sai ka goyani yayi dariya yace to zo hau ya duka na dane ya sulmiyoni ya kwantar kan kafet ya cire min rigar gaba daya ya soma sarrafa albarkatun kirjina shi dai yana son wannan abu daran ranar mun raya shi kan gobe zasu tafi.. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 Washe gari sai da hankalinshi ya tashi ganin yanda duk na tada hankalina ynxu iman in kina wannan kukan kike son na tafi?ko ban fada miki ba kinsan kina da matsayi mai girma a gurina karki damu wata rana dake zamu tafi sannan ga waya ko yaushe zakijini ki dai kular min da kanki shi ne nafi so ina share hawaye nace shi kenan,ni na hada mishi kaya suka fito har gurin mota na raka su,Anty Mimi sai wani jin kai takeyi,ta shiga gaban mota zai shiga ma zaunin dryva dama ina kusa dashi sai na rike mai hannu da hannuwana guda biyu hawaye suka sake zubo min ya juyo ya rasa me zai ce yace jeki ki dauko hijabinki mu saukeki a gida in su Haj Maska sun iso sai ku dawo tare nace to,baya na shiga mun isa gida ta gaida su Haj Kulu da Shuwa ta shige dakin Haj Yaya,ina jin Anty Mimi tana ce mata wai ni na tsaya shagwaba yana biye min da yanxu sunyi nisa dan haka da ina gaisheta bata amsa min ba sai na dawo dakin Mama, nan na samu yaynmu yana gayawa Mama wai don Allah ta lallashe ni duk na damu, Mama tace kaima ka daina biye mata kuyi tafiyarku zata warware,yace game da kudin amfanin ko abinci komai na hannun Kabir, nace mama ni fa da jamila zamuje can game da makaranta sai ya ringa zuwa daga cen mama tace badani ba tana min yan aikace aikace na hada rai kamar za sa ihu yaynmu ya dubeni sai kuma ya dubi mama yace maman sagir kiyi hakuri su tafi mama tace ka daina biye mata Abdulrahman akwai abinda nake hangowa wanda ita bata hangoshi ba, yace to ko dan kwana biu ne Mama tayi shiru sannan tace da tayi kwana biyun zan aiko a dakko min yarinyata, ya dan rusuna yace mun gode ya dubeni bari na shiga gun Hajiyata,mama ta nufi kicin, ina nan zaune ina jiran shi muyi sallamar karshe ashe ahi yayi gaba dan kar na mishi kuka, sai dai waya yayi min wai sun wuce nace ni kaima haka ko,yace sorry zan kiraki amma sai mun sauka lfy,nace Allah ya tsare min kai yaynmu yace na gode kanwata sai kin jini,ni ce na fara kashe waya ina gaida su Haj Maska suka amsa sai da muka yi magriba muka ci abinci sannan yaya Kabir yazo daukamu,maimakon ka bari sai bayan ishai sannan kazo yace a'a zanje tadi bayan isha'i, Jamila tace yaya Kabir gidan Anty Zee zakaje yace kwarai can zani Jamila nace kin san tane tace yaya ne ya kaimu ni da Sagir da Kamal,Haj Maska tace ai gara ayi auren,Kabiru yace to Haj kwanan nan ne. Na gyarawa Haj Maska dakinta katifa biyu ne a dakin sai kafet sai gurin aje kaya, babban falo muka zube munyi kallo bayan isha'i sannan muka shige dakin Haj Maska, nan muka kwanta katifa daya ni da Jamila ita ta kwanta dayar,bayan na rufo kofata.cikin dare naji wayata nata ringin na tashi na san yaynmu ne dan na sa mishi ringin din shi daban,cikin yanayin barci nace yaynmu yace iyen ba kice ke barci ma kike?nace to ya zanyi yaynmu yace ban san nayi kewarki ba sai da nazo kwanciya gsky nayi missn dinki a lot nace gara kai ga maman daddy nan, ya juya ya dubi mimi da taki ko kissing dinta yayi wai tana kishi sai ynxu ya san da ita,sai yace min mmn daddy jego takeyi nace to ynxu ga shi gari ba kusa ba bare nazo gareka yace me zan samu ynxu?nace komai ma yace kiss kafin ya karasa fadi na mishi yace Allah ya bar min ke kina cikin aikina haka mukayi ta hira har asuba sannan mukayi sallama dan haka da nayi sallar asuba sai na koma barci.Goma na tashi da zazzabi na sha panadol jamila ta mana Break har ina mata jinjina nace Jamila mama tayi kokari har kin iya girki?ai ko ina cin dankali sai amai,jiki yaki ko da yaynmu yayi waya ban sanr dashi halin da nake ciki ba Jamila ce tayi wa Mama waya, da yake komai namu yana hannun Kabir sai Mama ta mishi waya, sai da yazo ya dauki Mama suka zo gidanmu ko zama ba na iyawa yaya Kabir yace mu je Asibitin da yaynmu yayi Family Card Garkuwa Hosp, nan muka je bayan likita ya dubani sai ya bani gado yayi ma su Mama bayanin ina da shigar ciki sai dai yana bani wahala,sati na daya a hosp amma su Mama sun hana a gayama Yaynmu don sunce bai dade da tfy ba, sai dai duk san da ya kira sai Haj Maska ta dauka tace ina barci,ranar da aka sallameni ya kira ina kwance akan gadona na dauka a wahalce nace yaynmu......ya katseni ke ba wani yaynmu me kike nufi da kin daukar wayata nace bari kaji wlh ya katseni dama na kirane in kin ga dama kin dauka ince maki kin kyauta sai dai dadin abin ba ke kadai gareni ba bare abin ya dameni sai ya kashe wayar,ni ko da yake bani da lfy ban damu sosai ba.tun daga ranar bai sake kirana ba nima ban nemeshi ba,yau lfy gobe ciwo har muka shiga wata na biyu da rashin lfyr rannan da jiki yaki sai da aka kuma mai dani Asibiti na sha ruwa leda uku,Kamar daga sama sai gashi yayi min waya na dauka nace yaynmu ka huce ne?dan Allah kayi hakuri ka saurareni yace ina jinki nace sanda kake nema na a waya bani da lfy ina hosp sati na daya su Akhj sunki a sanar da kai don kar kace zaka dawo gashi baka dade da tfy ba ynxu ma ina gadon asibiti yau kwanana uku kuma yau za'a sallameni,sannan duk tsawon kwanakin da ka dauka kana fushi dani bani da lfy da sauri yace wanne irin ciwo ne?nace nima ban sani ba sai dai ka tambayi yaya Kabir ko Doc din yace to zaki iya jina ko wanne lokaci mukayi sallama, cikin tashin hankali ya yiwa Doc waya bayan sun gaisa Doc ya sanar dashi ciki gareni sai dai yana bani wahala,washe gari na fito wanka kenan sai na samu mutum a bakin gado,yaynmu ne zaune ya zuba tagumi da sauri na isa gareshi nace yaynmu yanxu kazo?ya dubeni hannuwanshi ya bude naje na shiga jikinshi yace Allah sarki babyna duk kin rame sai farin ciwo ko?na sunkuyar da kaina yace ina Haj Maska nace tana dakinta ya su Dady yace suna gaisheki nasan dai ya fada ne nace bari na samo maka wani abun yace a'a gurin likita zamu koma dake shirya na shirya nasa gyale wai nasa hijabi na cire gyalen nasa hijabina. Muna zaune gaban likita yace ma likita yana so ne a cire min wannan cikin da sauri na dube shi ban gane ba ya dubeni ke ba zaki gabe ba ki jirani,suka fita da likitan da yake dama abokinshi ne yace Maska cire ciki ba aikin mu bane sannan kayi kuskure da ka fada a gabanta yaynmu yace Doc Salihu taimakona zakayi mahaifiyata ta gindaya min doka mai tsanani akan yarinyar nan sharadin da ta gindaya min tace na zabi daya na kuma zaba, na farko tace ko in saki yarinyar nan wanda sakin da zan mata yana nufin barin gidanmu da mahaifiyata zatayi (wato mahaifina yace muddin na saki yarinyar mahaifiyata zata bar gidansa)na biyu ko ta tsine min na kuskura nabar yarinyar ta haihu,a son ranta kar na kusanci yarinyar kuma ba zan iya ba tunda ina tsananin sonta na zabi ba zata haihun ba to ynxu tun bamu je ko ina ba gashi ta samu ciki,Dr Salihu yace kaima ka san dole ne tayi cikin tunda ba wani mataki ka dauka ba sannan zaka cutar da ita in har kace ba zata haihu ba akwai nau'in zalinci,yaynmu yace naso a dan dauki lokaci ne sannan na san yanda zanyi na shawo kanta na san bai kamata nabi son rantaba na saba ma Allah, amma ina son na ganar da ita a hankali,Dr ya ce gashi ka soma magana a gabanta yace wannan ba wani abu zan shawo kanta, ni kam lokacin na kifa kaina a tebir din likita sai kuka nake yi, cikin da na kwallafa rai shi ne yaynmu yace a cire min ko da yake ba mamaki tunda dama yaynmu ba wai yana sona ba an dai bashi ne,soyayyar da yayi ta nuna min don ya mori albarkatun kirjina ne,ina wannan tunanin suka shigo yaynmu ya zo gurina ya kamani muka ida komawa kan wata doguwar kujera,Na dubeshi fuskata taf da hawaye nace yaynmu ciremin za'ayi yace kiyi hakuri kinga cikin na baki wahala nace ynxu ai naji sauki ina sonshi dan Allah a bar min yace ba ki isa haihuwa ba ki bari sai nan gaba, nace zan iya dan Allah ku barmin ina sonshi yace nima ina so to amma dole ne a cire ai bana so in rasaki ne Iman,na dube shi ya soma ban haushi nace yaynmu kona mutu in dai gurin haihuwa ne nayi shahada pls kar ku cire min ina son babyna,sai na ga yaynmu ya daure fuska gami da hararata gashi in ya sha mur ko kai wanene dole ka saurara dan haka sai nayi shiru ya kira likitan ta waya da yake fita yayi ya bamu guri yazo yace to kazo ka mata inaji ina gani yaynmu ya kwantar dani a jikinshi dr Saluhu ya danna min Allura har biu sannan yace mu dan zauna dan tana da karfi ,lokacin duniya ya isheni na mike nace ni gida zanje sai jiri duhu ya mamaye min ido na sulale kasa daga nan ban kuma sanin komai ba sai dai na farka naga Mama da Haj Maska,sai Yaynmu dake gefen gadon jina nayi sharkaf da lema ko ban duba ba na san jini ne na soma kuka yaynmu yazo ya rike min hannu ina ne yake miki ciwo?ban kula shi ba mama da Haj Maska suna min sannu nace Mama me yake zuba a jikina?ta dubeni yau me zan gani ni Habiba?wannan ai jini ne haka jini ya tsinke sai zuba kan kace kwabo har na fita hayyacina likitan kanshi ya rude da ganin jinin dake zuba daga jikina ya ma wani likitan waya yazo sun hadu su biyu a kaina suka ce su Mama da Yaynmu su fita,Yaynmu hankalinshi a tashe yama rasa me yake mashi dadi sai safa da marwa yake yi a kofar dakin tunanin shi in na mutu shine sanadi,dana sani da nadama kawai yakeyi dan da ya san hakan zata faru da bai bi san ran Hajiyan shi ba. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 Awa daya,awa biyu,har awa hudu basu fito ba sai da aka kira magriba Mama ta matso gurin shi tace Abdulrahman kaji masallaci ana kiran sallah yace mmn Sagir ba zan iya salla cikin nutsuwa ba gara in sun fito sai nayi tawa,Mama tace ka daure ka je sai kayi addu'a kaji ko? Haka nan ya tafi ,yana dawowa sai yaci karo da Dr Salihi,yace yawwa Maska dama kai na fito nema ynxu mun shawo kan matsalar da kyar sai dai jini muke so leda hudu zamu duba,yaynmu yace a'a gani ka gwada nawa in yayi sai ku diba ko laida nawa kuke so Dr yace biyu zamu diba a naka yaynmu yace Allah duka za'a diba haka kuwa akayi Mama tayi ta yima yaynmu fada wai ya zai kwanta adibi jini har leda hudu?yace mmn sagir mu dai yi fatan samun lafiyarta haka aka sa min jini hannu biyu sai da na kwana biu bansan inda kaina yake ba sai da na farka jinin ya kare sai ruwa.Dishi-dishi nake gani ban san su waye a dakin ba, hasalima dakin shiru sai karar fanka a hankali idona ya soma washewa naga Mama da anty Yagana,sai Babana da Alhj, sai kuma Malam. Nakai dubana kusa da kaina Yayanmu ne daf dani da ganin shi yasa komai ya dawo min sabo a raina nace abin da kake so shi yake wahalar da kai,hawaye suka shiga yimin zarya sannan ne yaynmu ya gane na farka da sauri yace Iman kin tashi ne?ya kamamin hannu su Mama suka zo suna min sannu gami da yiwa Allah godiya,wasa wasa kwana na sha daya,Yau monday na fito wanka ina zaune a kan gado yaynmu ya shigo Mama da Haj Maska suka fita bayan sun gaisa ya dubeni Iman ya jiki?nace da sauki fuskata babu walwala yace iman ki min afuwa na san nine sanadin sakaki cikin wannan halin amma ki min hakuri bana son rasa ki ne shi yasa,ni dai shiru na mashi nasan duk dadin bakine yake min yanxu na gane in mutum yace baya sonka tun farko ba zai taba sonka ba,sai dai wani abu to shima yaynmu na gane albarkatun jikina kawai yake so ba wani ni ba dama nasan ni ba ajinshi bace shishshigi nayi Ya tabani Iman tunanin me kikeyi ne?na zame na kwanta hawaye ya soma min zarya abin da yafi bani haushi yanda har ynxu zuciyata take matukar son shi,har ynxu son na nan ba zan iya fdama wani ainahin abinda ya sameni ba,Likita ya shigo bayan dube dubene aka sallameni sun yanke shawarar Mama ta wuce dani gida don haka gida muka tafi shi kuma yaynmu su babana suka ce ya koma,ranar da zai tafi ya shigo tunda na gaishe shi ban kuma magana ba, ba yanda baiyi ba in yi magana naki daya matsa min sai na sa kuka, ya kifa kanshi akan gwiwoyinshi na dube shi duk ya rame a raina nace duk kai kaja ni ynxu don son da nake maka zanci gaba da zamada kai baya ga haka da sai dai ka sakeni ya mike to Iman na tafi sai kin jini a waya ko motsi banyi ba bare na tashi nace Allah ya kiyaye hanya yadan dubeni sai kuma ya tafii,Tunda ya tafi kullum zai min waya sau uku,amma daga gaisuwa bana kuma magana har mama ta gane sai fada take min tanacewa ai ba shi ne ya dora min ciwon ba in kuma cikine ai Allah ke badawa dan ya zube sai na zargi mijina.Na warke sarai jikina ya dawo nayi kiba mama tace na koma dakina nace nidai tunda Haj Maska ta koma Maska sai su yaynmu sunzo zan koma,watanshi uku da tfy suka dawo saboda zuwan watan Ramadan nan da sati daya, ina falo ina kallo naji ana masu oyoyo duk da son ganin yaynmu da zuciyata takeyi sai naki tashi,dakin Haj Yaya suka yada zango sai daga baya yaynmu ya shigo dakinmu, na dube shi kullum dai yana nan dan gaye dashi jikin nan sumul, yace gimbiya ina gajiya nace kunzo lfy,yace lafiya,ina mmn Sagir?nace tana Sallah mama ta fito suka gaisa da har nace ni ba ranar zan koma ba mama ta bude min wuta dole na bisu, Yaya Kabir yasa an gyara gidan an share shi,na zauna a falona ya shigo kusa dani ya zauna nayi kamar ban ganshi ba yace Iman kin canja min sosai yanzu ba kya kula dani kamar da shiru na mishi ya jawoni jikinshi tashi muje dakina mu kwanta nace kayi hakuri ba zan iya kuma kwana dakinka ba, yace kina hauka ne ko? nace ba hauka yace ya zaki ce ba zaki kwana dakina ba alhalin ina mijinki? nace yaynmu ina ganin girmanka kar kasa na gaya maka magana, yace gara ma ki gaya min dan shiru shirunki ya soma cutar dani ya cigaba ina matukar bukatarki ba zan iya jurewa ba, na soma kuka ina fadin dama nasan jikina kake so hakika iyayenmu sunyi kuskure da suka zata kaine zaka rikeni amana ashe ba haka bane....... Ya tare ni wayace miki ban sonki? fadin son da nake miki kauyanci ne kin gani in za kiyi magana ki daina kawo maganar so....da kana sona da ba kaini an cire min ciki ba ina son abina kila ma shi ne kadai kwaina a duniya tunda baka sona shi yasa baka son hada zuria dani,yace ba zaki gane bane shi yasa amma ynxu na yarda komai kika ce ki min afuwa nayi kuskure,shiru nayi mishi gami da shigewa bedroom. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 Har azumi ya riskemu bamu jituwa da shi,yayi naki,karshe ma ya shareni,ina komai,girki da sauran aikace aikace, girkin ma nawa nakeyi tana na ta, kowa ran girkinta ta sama mijinta,duk da yaynmu yana kokarin ganin kar Mimi ta gane sai da ta gane,don haka take ta shigewa yaynmu gami dayi min kallon banza,yaynmu yayi siyayya irin na neman lada su gero,suga, madara ya aika kowanne gida,wato gidan mu da gidansu Anty Mimi kai harda babana,haka har sallah ta gabato ya mana siyayar kayan sallah ya sai ma yan uwa da abokan arziki sannan ashe ya biya musu ummara shi da Anty Mimi,ko ita ma bai gaya ma ta ba sai da abin ya gabato, murna ta dinga yi tana waya tana gayawa kawayenta da sauran danginsu,ni ko sai nayi kamar banji taba dama ranar nice da girki,yana shan ruwa a falona ni kuma na idar da sallah ya dubeni kiyi hakuri ba zamu je umra dake ba sai wata shekarar in Allah ya kaimu,bace Allah ya sanya alkhairi na tashi,da za su tafi yace komai na dangane da abincin sallah yaya Kabir zai kawo sannan ya bani kudi nace to ka san dai da sallah zani gida da gidan babana har gidan kawu malam ya dubeni ban ce ki fita ko inaba, haushi ya kamani, dama ina ciki gashi sai yayi ta jan Anty Mimi suna wani soyayya a gabana dan naji haushi ni ko sai na tashi na basu guri,na dubeshi gsky zanje yawon sallah tun da nazo gidan nan ban taba fita ba sai sanadin ciwo kusan shekara sai ka ce matar kulle yace tun da ba matar kulle bace ki je ai zan ji lbr na kara fusata nace ba fa siyana kayi ba hasalima ba gori ba ganina kayi kawai an kawo maka shi yasa kake wulakantani,yace Zauna ki gaya min me na miki? kuskure daya na san na miki kuma na baki hakuri ni nan da kika ganni kece mace ta farko bayan uwata da na taba ba hakuri kuma kin ki ki hakura dadin abin ba ke kadai gareni ba,abinda kike rowa ki jika ki sha ga tsinuwar malaiku da kin bari ma cikin da kike fushi kanshi da yanxu kin maida wani,raina ya kuma baci na shige bedroom ina kuka.Tunda suka tafi kullum sai yayi man waya wata rana in dauki wata rana na ki dauka, dama dady wajen Haj Yaya suka kaishi,ko shekara bai yi ba watan shi tara amma yana tfy.Da sallah ina zaune gida dan ma yan yawon sallah sunxo min sosai Jamila muna tare da ita tana tayani aikin sallah,shima yaya Kabir yazo da Zee dinshi,babana ya aiko min da kudi da kaji har da zannuwa ni da Anty Mimi har da Yaynmu ranr baba uwa tazo da yaranta biu sun min wuni, Mami da Amira rana daya suka zo min,mun sha hira har dare,ita bikinta bayan sallah da Gidadonta,Sallah ta wuce da kwana goma sha daya yaynmu suka dawo ko waya bai min ba ranar ina daki ina karanta littattafan da na ba Amira ta siyo min,na fito zani babban kicin ne sai naga mutane baje a falo,na tsaya ina mamaki araina nace lallai yaynmu,ya dubeni yace kin tashi?ko ba barci kike ba,ko tanka mishi banyi ba.Da daddare ya shigo ya kawomin tsaraba na ce ya barshi na gode bana so ga mamakina bai tsaya roko na ba

Chapter 3 of 5