Share this page
1 / 7
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels Tawa Tasameni 1-01 Posted by ANaM Dorayi on 12:09 PM, 03-Dec-15 ________________NA _________________ __________ HALIMA ABDULLAHI K/MASHI_______ Na mike a hankali ina ninke sallaya ban kai ga ajiyewa ba naji ana sallama,na juya cikin don san in dauki muryar mai sallamar har kin shigo kenan?nace bayan na amsa sallamar ta shigo sanye da kayan makarantar islamiya masu launin farare kar,riga da wando da hijabi. Tace kina kallona ba zaki yi sauri ba sai munyi latti ko?nace ko munyi latti ai yau akwai layi na nufi daki dama nayi wanka sai kawai na dauki kayan makarantana dake goge kan gado nasa,Amira tace su mama basa nanne?nace eh basa nan gashi har jamila ta tafi a lokacin islamiya yayi amma basu dawo ba,na rungume takarduna da Alkurani na na fito falo muka fita na mika ma amira ta rike min littattafaina don zan kulle kofar,natura key din inda muke sawa in mama zata unguwa ni kuma ban dawo daga makaranta ba sai ta aje min a gun in kuma zan fita tace in aje mata.Amira ta dube ni ta dubi dakin su mami tace yau su mami ba zasu bane?nace da kyar ne don yau ko makarantar boko bataje ba bata jin dadi in mun dawo kin gaida ita.isarmu islamiya kenan muka tarar da an tare yan latti ana yi masu bulala,Amira ta soma dariya don ta sanni da tsoron bulala na dafe kirji ina fadin yau na shiga ukku zamu sha bulala ni iman,Amira tace don Allah mu karasa ba kece kika jamanaba?nace Amira ina jin tsoro ta ja hanuna na bita muna isa gun muka tadda harda Ahmed yayan Amira don shine Amir dinmu yace don Allah ku zo inyimuku ku wuce don yan kwanakin nan kun kware gurin yin latti.Nace don Allah yaya Ahmed kayi hakuri yace wllh sai nayi maku kun fi sauran ne?da zan kyaleku ya ci gaba da cewa kuna bata mani lokaci in har kuka bari kowa ya gama shiga sai na zane ku tas,wani kusa dashi yace to kai Ahmed ka bar su su wuce mana,yace Allah Aliyu bazasu shiga ba sai na dakesu wanda yaya Ahmed ya kira da Aliyu yace to bari ni in dake su to,yy Ahmed yace sai dae kai na dake ka a madadinsu,in ko ba haka ba sai dai suzo ni in dakesu da kaina,Amira na da zuciya don haka sai taje ta mika hannun shi ko bai bugi hannunba ya zuzzuba mata a jiki,ganin haka ya sani na kuma rudewa ina faman magiya don ni kowa ya sanni da shegen tsoro sannan bani son abinda zai taba mani lfyata don haka ma dawuya ka ga nayi laifi nakan yi kokari ganin nabi dukkan dokar da aka shimfida a gida ko a makaranta.Amira ganin zan bata mana lokaci taje gaban yy Ahmed tace ka bige ni a madadinta shiko da gayya ya ringa tsala mata har sai da Aliyun nan suka ce ya isa mana Ahmed niko hawaye na somayi na kama Amira muka wuce ina fadin me yasa kika je ya buge ki?ta soma share mani hawaye muka wuce ajinmu,Shidda na yamma daidai muka tashi dama mu yan aji biyar Ajinmu a sama yake,don haka titin kan layinmu naji an kwala mani kira cikin fada na juyo sai naga anty mariya gabana yayi faduwa don na san ganin ta ba alkhairi bane hakan ce ta kasance domin kuwa tana isowa gun mu sai ta hauni da zagi wai na taho makaranta ban jira su kamal ba don naga ba kannena bane shiyasa ta cigaba da zagina gami dayi mani gorin gida wai shegiya agola yar kara nazo zan fare,Amira tace mani don Allah iman zo muwuce taja hannuna cikin fushi tayi maganar,anty mariya ta koma kanta tace ke kar kiyi mani rashin kunya don zanci ubanki a nan,Amira tace ba dai ubana ba kuma har kika yarda kika buge ni zakiyi da kin sani,cikin rawar jiki na rufe ma amira baki muna cikin wannan hali sai ga anty hadiza da bilkisu da saade dukkansu sai zaginmu suke yi,Sa'a har da dungurina,nan amira ta kai mata duka nayi saurin rike amira don kar suyi mana taron dangi su bugi banza don nasan kadan suke jira anty mariya tace wai ke amira nan da dukan Sa'a zakiyi?amira tace yo da sai in barta ta duke mu,don kunga bata ramawa ne,lman din shi yasa ku ka raina ta, taci gaba da cewa,ai Sa'ar ba girman lman din tayi ba,bilki tace to ta koma gidan ubanta mana in kuma bata dashi bane mu sani,naja hannun Amira muka wuce Amira ta cigaba da lallashina sannan tace min,don Allah lman in tambayeki mana?na share hawayen fuskata da gefen hijabina nace ina jinki tace babanki ya rasu ne ko yana nan? In ya na nan ina yake?na dan yi shiru sannan nace Amira baba na yana nan bai rasu ba wasu hawayen suka kuma zubo mani ban damu da in goge ba na cigaba da cewa yana tudun wada ta nan kaduna,Amira ta ce to ki koma mana don zaifi maki kwanciyar hankali komin talaucin ubanka ya fi zaman agolanci y not ki koma can?nace uhhm Amira mubar zancen nan wata rana zan sanar dake dalili mai karfi da ya hanani in bar gidan nan sannan kisan mahaifina ki kuma daina zargin ko kwadayi ne ya zaunar dani a nan,Amira tayi sauri ta rike ni gami da tsaidani wuri guda tace wllh ni ba nufi na kenan ba naga wulakancin da su Sa'a ke maki yayi yawa ne shi yasa,nayi mirmushin karfin hali nace no a Amira karki damu na fahimceki sannan muka wuce gidan su Amira,kamar minti goma na dauka gidan su Amira sannan ta rakoni kofar gidansu tace min a cikin satin nan ba zata shiga gidanmu ba,ina shiga naga su Anty mariya sun rigani dawowa kuma sun fadi karya da gasky sai faman fada suke su da iyayensu suna ganina ai dawa Allah ya hada su ba dani ba suka hauni da masifa,Haj Kulu mahaifiyar mami harda aibantani gami dayi min gori sannan tace zata ga Amiran don ubanta sai ta gaya mata dalilin da yasa ta zagi su anty mariya don ba sa'anin yinta bane,ni dai sum sum na wuce daki Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 Mama na gani a falo ta zuba tagumi da alama taji duk abinda suke cewa(kishiyoyin nata)ta dubeni fuskanta cike da tausayina tace Iman menene dalilin da yasa kika tsokanin mutanan nan bayan kinsan halinsu sarai nace mama wllh ban san me nayi masu ba na dai ga anty mariya sun zo da su Sa'a suna ta faman zagina wai ko na taho makaranta ban jira su Kamal ba ko mene oho mama tace to naji suna cewa kuna ta zaginsu keda Amira nace Allah mama ni sam ban ma yi magana ba Amira dai ce kinsan ta da zuciya shine fa ta tanka masu amma sam bata zagesu ba,mama tace to don Allah ki dai na kulasu sam musamman a kan titi in ma sun zo maki da irin wannan ki dinaga basu hakuri kiyi wucewarki kinji ko?nace to mama muka mike don yin sallar magariba. Misalin sha biyu da rabi muka taso daga harda yau ma yan dakinmu ne kadai ni da jamila da sagir muka je,dama sauran yan gidan zuwa islamiya bai damesu bane bare ma hadda,gara ma mami takan je to amma tun fridy bata jin dadi,muka tadda mama a kicin tana girki na shige kicin din bayan na ba jamila Alkurani na da hijab ta wuce daki nayi ma mama sannu gami da amsar albasar da take yankawa,nace yau me kike dafa mana ne,tace dan wake nayi in kin gama yanka albasar ga mai can sai ki soya shi bari in dauko kular baban ku nasa mishi,don yace zaya aiko a dauka nace dan waken za'a kai mashi kasuwa mama?tace nima haka na ce mashi sai yace yasan komi na dafa ba zaiyi shakkar kaishi cikin jamaa ba,nayi murmushin jin dadin an yabi mamana ai kin iya girki ne mama,ta fita tana dariya ina jin dadin yanda mama take sakar mani fuska duk da kasancewa ta yar fari a gunta sannan mama uwa ce mai wahalar samu takan ki nata don duniya ta soshi bata fada da zagin yayanta sai dai nasiha gami da lallashi.bani manta lokacin da nake karama mama ta kan zaunar dani ta nuna mani girman Allah gami da cusa mani tsoronshi tana nuna mani abinda zanyi da tsira daga azabarshi a wancan zamanin ta kance kar na zagi kowa ko an zage ni kar na rama sannan kar na yarda sallah ta ringa wuceni don haka ma tun ina karama nasan sunnoni da farillai gami da mustahaban sallah da alwala sannan bani zagi in ma wani yayi naji sai na gudu ince kar na sami zunubi saboda jin da nayi shiyasa ban iya zagi ba,sannan mama ta na da hakuri na ban mamaki zata iya zama da kowa ga ladabi don ban taba ganin tana musu da maigidanta ba komai yace tana yi sannan ga tsafta komi namu daban yake duk inda muka shiga ni da kannena mukan zama abin sha'awa gashi mama ta iya girki sosai na zamani da na gargajiya shi yasa maigidanta ya kanyi alfahari da ita baya shayin kawo baki ko shi akai mashi kasuwa haka nan duk da cewar basu shiri da abokan zamanta suma suna farin ciki da ranar girkinta don sunci mai dadi sannan yayansu kanyi rigima a duk lokacin da suka zo cin abincin kai ko ruwan tea ta dafa daban yake don zaka iya shanshi ba sai kasa madara ba.nayi zurfi a tunani bansan har mama ta dawo ba sai dai naji tace haba iman har yanzu kina kan yankan albasar nan baki tashi ba?nayi firgigit na juyo tace ai kina tunanin menene haka?bata saba mana da karya ba don haka na sanar da ita tunanin da nake na kara da cewa mama ina matukar jin dadin zama dake kuma ina alfaharin kasancewarki uwa a gareni tayi murmushi tace sai ki dinga koyi da hakan kuma kiyi watsi da duk wani kuskure da kika ga nayi sai da na zuba albasa a cikin man sannan nace wllh mama ni ba taba ganin wani kuskurenki ba tace kar ki kuma cewa haka babu mutumin da baya kuskure dan adam ai ajizi ne nace to,sai da muka gama cin abinci sannan na nufi dakin su mami don in gaisheta ina son inje amma ina tsoron haj kulu mahaifiyarta ynxu ma ganin ta shiga wanka shine dalilin da yasa xan je duk da dai bayin a dakin yake amma nasan ta shiga wanka ne a bakin kamal inda na tambayeshi ta na nan yace man ta shiga wanka na samu mami zaune a falonsu tana cin kifi nace yan jinya an samu lfy kenan tace kar kice man komi komi tunda baki zo gaisheni ba nace wlh ina son in xo gaisheki ina jin tsoro ynxu ma kamal na tambaya yace mani mominku ta shiga wanka,um kina jin tsoro ne?nace baki yarda bane tace na yarda nace Amira ta na gaisheki tace tana amsawa tace ai naji sauki kwarai don naci dan waken mama sosai kafin inyi magana sai muka ji maganar haj kulu fuskarta a daure ta nuna ni tace wannan yarinyar baki da zuciya in banda rashin zuciya har yaushe zamuce ki bar shigo mana daki amma kin kasa to yi nan ta nuna min hanyar waje.ta cigaba da cewa kekasashiya marar zuciya anyi halin uwa mami tace kai mama don Allah ta kaima mami duka a gadon baya yi min shiru yar iska duk ba kece kika jawota ba in na kuma ganinta anan sai naci ubanki ni dai nayi waje cike da takaicin zagin da nasha. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 washegari monday ga aladar gidanmu duk mai girki itace zata tashi tunda asuba dafa ruwan tea ko wane daki suna zuwa su dibi nasu a cikin flask su kai daki suje su hada,yau haj kulu ce da aiki don haka sai da na bari ta fita sannan naje diba bansan cewa madara ta kare ta kicinba sai da nazo hadawa da sauri na nufi daki na iske mama tana sa ma jamila safa nace mama babu da madara ko kadan ta dubeni tace kash jiya.... amma ga dari biyar can kan mirror dauki ki siyo yanda zata isa in yaso kafin ya wuce sai in sanar dashi nace to na dau kudin na fita,a tsakar gida na iske mami sanye da uniform hannunta rike da safa tace har kun gama karyawa?nace aah ya jiki tace da sauki yau dai zanje makaranta nace da kyau kam ki leka ta dubeni ynxu ina zaki?nace shagon sanita aje safar akan window din dakinsu taje muje in rakaki nace kardai a nemeki tace kedai muje,dashi ke shagon ba nisa nan da nan muka dawo shigowar mu kenan haj kulu ta fito daga daki ganinmu tare da mami ya yi matukar bata mata rai ta hau mami da zagi gami da daukar alkawarin dukan mami,haj yaya uwargida sarautar mata itace ta fito daga dakinta tace ke kulu kina bani mamaki ga yar iskar da zaki jibga nan ta nunoni sai ki hau yarki da zagi kinsan fa ita da uwarta in mutum ya sarkafe masu baya ji baya gani sai Allah da malaman gari indai zakiyi mata addua to kawai kiyi mata,niko uwar tsoro jin ance zaa bige ni sai nayi daki da gudu ko mama ban bari taji xancen ba don bata son tashin hankali kuma Allah ya taimaka ta kunna rediyo inda tasa kaset na kr2n Alkurani kira ar sudes,a gurguje muka karya don kar muyi latti muna cikin sallama da mama kamal ya shigo wai kuyi sauri ko muwuce inji anty mariya mama ta miko mani naira hamsin tace gashi sa jikka nace barta mama gafa ta jiya nan ban kasheba sagir yace meyasa mu ba'a bamu kudin mama tace ku ai ga kwandonku nan cike da kayan abinci amma in kun girma zan dinga baku kuma,jamila tace kai sagir mama tace babu kyau a ba kananan yara kudi yace wai haka mama? Mama tace e mana nace kai muje kar ayi ta jiranmu mama sai mun dawo tace to.. haka rayuwa ta cigaba da kasancewa kuma kusan ko yaushe inada abunyi ban cika zaman banxa ba in bani makaranta to ina kicin in ranar girkin mama ne don haka nima babu girkin da ban iyaba na gargajiya ko na zamani haka nan kuma na kan gyara dakin mama da namu da falo sannan na kware gun wankin bayi nasa turaren wuta shiyasa dakinmu kullum yana cikin kamshi da sanyayar iska mai ddi na kan zauna nida yan kannena in koya masu kr2 Alkurani da sauran littatafai haka ina taimaka masu da homework dinsu shiyasa mun fita daban a gidanmu komi namu tsaf tsaf,a ranar wata sundy lokacin muna hutun islamiya, hadda ma don muna kusa da fara azumin watan ramadan da safe misalin karfe goma da rabi na gama duk wani yan gyare gyare nace da mama bari na shiga gidansu amira dama nan ne gurin zuwana tace to ki gaida mmn faruq nace to,na samu Amira tana faman krtun littafin hausa a falonsu ko sallama ta bata ji ba sai da na zabga mata uban duka sannan na fizge littafin na duba sunan shi naga Allura cikin ruwa,nace kedai kullum kina cikin krtu maman su ta fito na gaisheta tace mani yasu mama nace tama ce a gaisheki tace ina amsawa na dube ta nace mama wai baki hana Amira krtun nan ne?maman su Amira tace nayi nayi taki bari ynxu ma boyewa take don tasan in na gani yaga shi nakenace in tana son tayi karance karancenta ta bari sai ta kai ss sannan ta kijiba sai tayi tayi ba,maman tayi shiru cikin bacin rai na harari Amira nace kinji ddi mama ta bata rai saboda ke?mama tace ai ke kina da hankali ba kamar ita ba ta shige daki Amira ta dubeni tace kinji ddi kin hada ni da mama nace no Amira in iyayenmu sunce mu bar abu muyi kokarin bari don gsky zan gaya maki da ki kijin mgnr iyayenki gara ki bar duniya a guna kenan tace to naji taja hannuna tace zo muje dakina nace ke dai Amira baki son fadin gsky muna shiga na zauna bakin gadon nace mata don Allah Amira kiyi kokari ki barin krtn nan tun da mama ta baki damar yin krtn in kinje ss.Amira tace nayi kokarin na bari na kasa ne,nace ni ko kingani nan ko me mama tace na bari ko da zan rasa raina ne ba zan bari don bani da tamkarta nai shiru ina tunani hawaye ya zubo min na dubi Amira nace don dai iyayenku duka biyun suna nan raye ko ince a tare shi yasa baki san zaman agolanci ba cikin hawaye ban san sanda nace......... Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 sunana na gsky shine Amina kuma naci sunan kakata ce mahaifiyar babana ,babana da mamana yan asalin wudil ne a wani kauye da ake kira indabo a jihar kano,babana gidansu sun gaji sarauta don babanshi ne dagacin kauyen,yanxu haka itako mama yar malamai ce don babanta shine limamin garin sunan mahaifina idris kuma shine da na hudu a gurin mahaifinsu yana da yayye yaya samaila sai yaya musa sai babana idi kamar yadda suke kiranshi sannan sai kannanshi biyu bala da sani su shidda ne a dakinsu matan dagaci biyu ne uwargida Amina mahaifiyarsu babana kenan wadda naci sunanta sai abokiyar zamanta basira wacce aka bashi sadaqarta ita kuma yayanta ukku Auwal,salisu sai hindu,suna matukar zaman lafy ba wani bambanci wannan shiyasa yayansu hadin kai da son junansu gashi suna ma mahaifinsu dagaci umar biyayya kuma dukkansu gidan liman suke daukar krt mama ko a lokacin tana kaduna gidan yayanta mai suna mal bashir ya dauko ta ne tunda mahaifiyarsu ta rasu shi babban malami ne a tudun wada daga yawan almajiranci Allah ya zaunar dashi a inda yayi auren shi da baba uwa itama dai yar can din ce da yaje ya auro ta,yana almajiranci a wani zuwa da yayi gida shine ya tafi da wasu almajirai a cikinsu harda idi babana kenan domin yayi sauka tuni,zai dora ne su ko su mama su hudu ne a wurin liman kawu bashiru shine babba sai kawu Aminu sai kawu kabiru sai mama ita kadai ce mace tana da shekara tara mahaifiyarsu Allah yayi mata rasuwa kasancewar ita kadai liman ke aure sai kawu bashir ya dauko mama dama baba uwa bata taba haihuwa ba ko ince har ynxu Allah bai bata haihuwa ba sai ko ta rike mama,shi ko liman isuhu aka bashi sadaqar mata guda biyu da taimakon baba uwa mama mai suna habiba ta samu shiga firamare shi ko baba yana nan yana hadda gidan sai Allah ya hada shi da makocinsu Alh adamu a dalilin dan gwanjo ne a kasuwar bacci yasa baba yana rubutu yana kai masa daga nan yace yana yayi sanaa irin ta gwanjo alh adamu shima dai dan kn ne ana ce mashi adamu garko duk girinsu daya sai dai shi a garko yake bayan nemi izinin malaminsa wato kawu bashir kawu yace tunda kayi sauka hadda kakeyi ba bu komai ko da rana za ka iya haddar ka Allah ya bada saa wannan sanaar itace hanyar arzikin mahaifina tun yana kasawa a bakin titin kasuwar bacci in an kwance dila a bashi ya kasa har ya koma kwance dilar shima kafin shekara ukku har ya sayi rumfa kuma yana sayan diloli a wannan lokacin ne Allah ya ba baba uwa ciki ta haifu da namiji kuma mama a lokacin ta kammala primary shiko babana duk da ba a gidan yake ba yanzu yana zuwa da daddare haddar shi ya sanar da malam kamar yadda suke kiranshi kawu shi dai habiba yake so mutumcin da baba yake dashi a idon malam shi yasa har ya amince koda kauye suka ji wannan zance sunyi murna don akwai zumunci mai karfi tsakanin gidan dagaci da gidan liman,kauye aka koma akayi biki sannan su mama da baba suka dawo shekara biu da aurensu baba yayi kudi sosai da gwanjo tuni ya gina gidanshi a unguwar sanusi ga motocin hawa da na haya da ya sai ma mama sannan ya tallafi yan uwa na kauye hakika yana da halin kanawa na asali don akwai taimakon na kusa dashi haka ya debo yayan yan uwa sa daga kauye ya sasu a makaranta dan yana da haushin rashin bokon da baiyi ba danma cudanya da mutane yasa ya fara jin dan turancin sa na yan kasuwa matsalar baba da mama daya shine rashin haihuwa har wannan lokacin mama ta fishi damuwa shi ko ko a jikinshi yace Allah baya barci a gefen mama ita ma tana taimakawa yan uwanta dama tuni daga dagaci har liman sun keta hazo sannan angyra gidansu tsohuwa Amina(kakata) sun kaita ita da abokiyar zamanta harda yayyan babana,su mama dai kowa a kauyen ya gama zuwa a cikin iyaye da yayye sannan suma suka je ita da babana.kowa yaje sai ya roka masu Allah ya basu haihuwa har cikin dangi sun fara korafi gami da nuna masa ya kara aure ita ko tsohuwa Amina macece mai nagarta da ibada da yarda da kaddara don haka itace mai tsawatarwa sauran yan uwanta da kannen alh idi (wato babana)takan mika lamarinta ga Allah don haka kullum ma tana yi masu adduar Allah ya basu yaya na gari masu albarka,shekaru goma da aurensu Mama na da babana sun dawo ummara ta dawo da jinya mai tsanani bayan jin jiki da jinyar asibiti sakamako ya fito cewa tana da ciki fadar farin ciki ma bata baki ne,anan da kanshi baba yake mata rubutu take sha..... Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 Wata tara da 'yan kwanaki ta haifo ni sankaceciyar kowa ya zo barka sai ya yaba girma da gashina sai dai ni baka ce tamkar mahaifina tun ina yar jaririyata har yau ban canzaba, dangin babana na dauko domin gaba dayan yan uwanmi dangin baba kamar mu daya muna da dan kyau daidai namu sai anan na dubi Amina nace kin dai ganni har yau ban canza ba na cigaba da cewa dangi sun kwararo daga kauye da birni anan naci sunan tsohuwa Amina, kawar mama kuma makociyarta itace ta ba da shawarar a kirani da iman,na taso cikin gata da tsantsar so gun iyayena da yan aikinmu da yayyena wadanda babanmu yake riko,shekara takwas na halarci makaranta nursery mai suna salmat intl dake kasuwar santara market makarantar yayan masu kudi ce don haka krt ba wasa duk lokacin hutu babana ya kansa a kaini kauye don yace asali mafari wannan yasa na saba da kakata Amina da yan uwana 'ya'yan baba lami mata sa'anina Hassana da Ussaina muna wasa dasu kuma sune suke kaini ganin dangi a sauran kauyukan,ina matukar son kauye musamman yanayin damina tayi min a garin domin muna zuwa gona kakata tana ji dani don haka nima ina sonta suma dangi kowa na sona kawunnaina da liman suma ina zuwa in yi masu kwana biyu yau ina nan gobe ina can gata dai gani nan cikin sai in hutu ya kare zamu dawo wani sain da kuka nake dawowa a hado mani tsarabar kauye mai yawa dangin uwa da na uba sannan mu dawo tare da su yaya Ibrahim da yaya Abubakar,yaya Abubakar dan baba lami

Chapter 1 of 7