Share this page
3 / 7
nan,in har kin kiyaye komai babu abinda zai faru tsakaninku ko ynxu ki tashi muje ki gaishe shi mana,nace a'a mami gaisa wata rana nace to ynxu ya dawo kenan?tace aah bai dawo ba kenan,zai koma wannan zuwan ma in gaya maki haj yaya ce ta matsa yazo don su gana da yar gidan haj laure,anty mimi nace ita zai aura kenan?mami tace kuma abinda baki sani ba yana matukar bin maganar iyayenshi don ko wuta suka ce ya shiga zai iya shiga musamman haj yaya bai hada ta da kowa ba yana matukar jin maganarta,na dube ta cikin tsoro nace kinji ko?tana ce mishi ya koreni zai koreni ko dai ma in tafi ne?mami sai dariya take yi min,Kamal ne ya shigo ya sanar da mami mamansu na kiranta.Bayan kwana biyu ya raba tsaraba har su jamila da sagir ya basu,mama ma ta samu less da shadda da takalmi sagir din ma harda Jc shi da kamal,su mami english wax ya kawo masu ni dai banje ba kuma bai sani dani ba don ban yarda ya gani ba,ran da ya yi kwana ukku da dawowa mama ta amshi girki da rana ina tayata aikin burabisko mami ta same mu a kicin tace yaya yace a kai mishi abinci,nace yana cin birabisko ne?tace oho nace to inbazaki laifi ba kije ki ce mishi burabosko ne don kar a yi mishi laifi,tayi musrmushi sannan ta fita,anty yagana tayi sallama ta shigo na fito daga kicin na amsa,sannan na gaisheta gami da tambsyarta saudat tace tana gida sannan ta wuce ciki tana ce min maman naki na ciki? nace eh,mami ta dawo tace yace akai ma abokanshi shi kuma a dafa mashi indomie amma ke zaki dafa ko? tace eh nace to don kar inyi kuskure mami tayi dariya tace kai ke kam kin cika tsoro,sababin kuloli mama ta bani na zuba masu birabisko da miyar kaji yaji curry sai kamshi yake,na dauka na tafi nayi sallama a kofar dakinshi aka amsa mani cikin faduwar gaba na shiga nace sannunku mutum uku suka amsa kaina a kasa ban kalli kowa ba nace a ina zan ajiye?cikin dauriya nake magana gabana sai faduwa yake wani daga cikinsu yace maska tana magana,da sauri na dan dubi wanda aka kira maska yana ta faman danne danne waya tamkar ba dashi ake magana ba,dayan yace ke ajiye kan wancan table din,na dubi table din sai naga akai yayanmu ya dora kafarshi ,na dubi mai maganar nace ai yasa kafa a kai yayi murmuahi sannan yace ajiye ko ina kinsan halin yayan naku sai hakuri na ajiye a gabansa don mami tace dama su ne zasu ci na juya zan tafi sai naji murya mai sanyi amma cikin fada akace ke haka ake bada abinci a gidanku ko?na juyo da sauri ga mamakina yana danne danne wayarshi kamar yanda na sameshi,sai a lokacin ne ma na dan kalli fuskarshi, kykkyawa ne na ban mamaki don duk gidan yafisu kyau sak kamarshi daya da hajiya yaya,tsawa naji in ba zaki zuba musu ba dauki ki tafi,da sauri na duka jikina na kyarma na zuba musu nan dakin ya bude da kamshin miyar kajin na mika wa kowa sannan na mike dayan yace dan bamu ruwa nace to zan fita dayan kuma yace ga fridge nan na nufi gun fridge ina tunanin yanda zan bude dan ban taba ganin irinshi ba cikin sa'a ina dafa shi sa i naji na latsa wani abu sai ko ya bude kayan shaye shaye ne kala kala na rasa wanda zan dauko musu sai na dauko musu ruwa a babban gora na dauko five alive na aje masu da na duba saman fridge din sai naga kofuna irin na wajen na dauko tiran kofunan gaba daya na aje a gabansu,ina kokarin mikewa ne mami tayi sallama suka amsa har da yayanmu ta shigo dauke da kula da plate da cokali na fita na dan tsaya a kofar dakin ina jiran mami labarin abinda yayanmu yayi mani sai na jiyo itama tana shan nata fadan,muryar yayanmu ne yana ce mata yar iska haka ake dafa abinci?indomie ne din ba za ki iya dafawa ba?ina cewa ganin kin danfi su mariya abin kirki ashe kema useless ce,sam ban ga wani amfani ba gun mace matsawar bata iya abinci ba,ko aure kukayi irin abinda da zakuyi kenan ko?sai naji muryar wani acikin abokan yaya yana cewa to kayi hakuri mana maska,ai yara ne sai naji muryar yayanmu din yana cewa no....... Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 Nasir kar ka goyi bayan wadannan yaran sam basu iya komai na mata basu iya girki ba basu iya gyaran daki ba,sam basu iya komai na mata ba yan iska sai dare yayi ka gasu suna surutu da samari sannan ace masu yara?yaci gaba da cewa bari kiji ba za'a yi asarar wannan abincin ba maza ki dauka kije ki cinye shi ina nan shigowa har dakinku inci ubanki in baki cinye shi ba ina nan yanda kuka sanni ban canza ba fita useless kawai,nan mami ta same ni a kofar daki duk na kara firgicewa na dubi mami wadda ke zubda hawaye nace mami yanzu ya zakiyi da wannan uwar taliyar don Allah?tace zo muje sai da muka isa gun lungun shiga cikin gida sannan ta dubeni tace don Allah iman ci wannanabincin kiji nasa hannu na dandana daidai kam yayi sai dai da ta dam kara wasu abu zai danfi wannan dadi,nace yayi mana tace to kinji shiyasa ni sam bana son ya sani wani aiki ga tozartani a gaban abokanshi nace to ki kai ma masu wanke wanke su tafi dashi gida mana tace wai in kaiwa su lami masu aiki?nace eh tace baki san yayanmu bba kenan kar kiyi fata irin haka ta hada ku kuma duk matar da ta aureshi ta shiga uku,nace anty mimi zatayi fama muka wuce cikin gida bansan yanda mami ta kare ba,sai washegari a school take ce min zubar da rabi tayi ya sameta tana cin rabin.Washe gari gab da magriba na dawo daga islamiya da shike ina zuwa sanawiyya na shigo gida,zaune a kofar dakin yayanmu samari ne su hudu sai shi yayanmu yana tsaye yana daddana waya,nadan yi mamakin yanda baya gajiya da danne danne waya ban taba ganinshi ba waya ba kuma ko da yaushe cikin danna ta yake tun daga nesa nake kallonshi sanye yake da dogon wando da riga daga nesa nake kallonshi sanye yake da dogon wando da riga mai gajeran hannu masu ruwan bula da ratsin fari an rubuta adidas a jikinsu,gsky yafi yan gidanmu kyau,maza da mata dogo ne yana da dan fadin ga kwarjini gashin kanshi a nannade ina tsammanin yana sanya mai ne akan ko kuma haka gashin nashi yake?oho ban san dalili ba duk sanda na ganshi sai gabana yayi wani mugun faduwa bana raba daya biyu don ina jin tsoronshi ne,na iso daf dasu kanshi a duke yana danna waya amma sai naji yace ke in kin shiga kice Sa'a ko Bilki su kawo mana butoci,to ba ma magana dasu Sa'a ko ince basa min magana kuma ban ga mami ba sai naje dakinmu na dauko butoci guda biyu na kai masu shi baya gun ina zaton bayinshi na daki zaiyi sagir na tura sagir ya kwaso mana butocin,wata rana asabar zan tafi islamoya don yanzu bana jiran kowa a yan gidanmu dan ba lokaci daya muke karatu dasu ba sai dai na biya wa Amira mu tafi,sanye nake da hijab har kasa nasa safa da nikab yayanmu na gani yana kulle dakinshi sanye yake da gajeren wando da yar rigar nike kafarshi da safa da takalmi but na kwallo da alama zai motsa jiki ne,nazo zan wuce ya dan dubeni ina jin yana son ya gane kowacece kamar na gaishe ahi sai kuma na fasa ina zaton bai gane ni ba,na gota shi kadan sai ya juyo yace ke gabana ya fadi dama cikin faduwar gaba nike,na dawo kaina a kasa nace gani baiyi magana ba ya gama rufe dakin ya matso gab da ni sannan yasa hannu ya dage nikab din idona ya firfito don tsoro yace ooh na dauka mami ce,ya cigaba da magana fuskarshi a daure ke na lura sam baki gaida mutane ko?na dan saci kallonshi fuskata yake kallo na kali kasa sannan nace ina kwana?yace wuce bani so sai da na roka kenan dubeta ,a raina nace masifaffe kar ka amsa din na tafi abina. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 Zama da Amira yasa yau da gobe nima na soma karanta littafi kuma sai da na tambayi mama tace amma na dinga karanta masu kyau kuma masu amfani sannan in har zan karanta to ya zama bani da aiki ko na makaranta ko na gida shi yasa ma nafi yin karatun da daddare kasancewar bana fita ko ina ko samari sunzo kirana mama bata matsa mani ba don tace in kr2 nake son nayi to na tsayar da hankalina gun karatun.Yau monday muna hutun easter bani da wani aiki duk na gama kwance nake bisa gadona ina karanta wani littafi mai suna auren kisan wuta ina jin dadin lbr banji sallamar mami ba sai dai naji an fisgw littafin daga hannuna cikin sauri na tashi tana dariya tace kai iman,ke dai kina krt nan baki jin komi,nace lbr ya hadu,tace hala na soyayya ne?nace eh tace ai na sani nace kin san me?ai ku ne kuke soyayya ni kin ganni da saurayi ne?naci gaba da cewa wallahi ni banma yarda akwai wata soyayya da kuke cewa ba,mami ta soma dariya tace lallai yarinya da sauranki ke da kike karanta littatafai ai ke zaki ba wani lbr yadda ake soyayya,nace suma duk jinsu nake sai kiji an ce wai tana tuna shi tana mafarkinahi,don Allah da gaske ne?mami tace aa karya ne randa baku iya nutso a cikin soyayya ba ba zan yi magana ta katse ni da cewa ke ni ba wannan ya kawo ni ba an sa ranar su a anty Mariya wannan Alhajin kin ganeahi?nace mai katon cikin nan?tace eh shi ita kuma Hadiza wannan Sanusin mai jar motar nan,nace na ganeahi wanda ya taba cewa na kirata,don ya bata kudi ta bani shine ake cewa kar na kuma gaishe da saurayinta,don mu duk wanda ya dafe mana ya dafe mana kenan mami tayi dariya tace to shi. Yaya a Abubakr yana zuwa gidanmu haka yaya ibrahim dukkansu suna min hidima sannan yaya Sulaiman shima yana zuwa sai dukkansu sun daina shiga wurin mama sai dai su gaishe ta waya,wani abin mamaki kuma yaya Abubakar shi kadai yake zuwa haka ma yaya Ibrahim din duk babu wanda ya taba min maganar soyayya ina ganin take takensu kuma bana jin zan iya amince ma dayansu. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 Yaya Kabir ya gama bautar kasarshi ya dawo gida,to shi dama muna shiri dashi rannan na fita da safe zani shagon mal Sani dan sayan sabulu naga yaya Kabir yana tahowa daga bakin kasuwa na jira ya iso nace kai kam ka cika yawo daga ina? Na duba wani abokin bab can da bashi da lfy nace ko Alhaji isa naji mami tana maganar zuwa duboshi yace yea shi ne,muka jero muna tfy har gida na tsaya daidai kofar dakinshi zai bani kwanukan dana kawo mishi abinci da daddare ya fito dasu kenan yayanmu shima ya fito daga dakinshi cikin sauri na gaisheshi sau daya wato ina kwana yace lafiya dama shi gaisuwarshi bata wuce haka in ma ka kara to ba zai amsa ba na amshi na wuce sai naji yayanmu na cewa kice mami tazo tayi mani shara kan nayi magana sai yaya Kabir ya riga ni yace ai yaya Abdulrahim dama wannan din kasa da kafi ganin daidai dan ta kware yacw to gashi in kin gama ki rufe mani dakin kiba brother key din,nasa hannu biyu na karba gami da cewa a dawo lfy bai amsa ba yayi gaba,na dubi yaya Kabir nace don Allah shi yayanmu baya amsa gaisuwa ne?Kabir yace yayanmu kenan ai shi daban ne duk yanda kika so ki san halinshi ba zaki iya ba mutum ne mai ban alajabi na wuce ina dariya,na sanar da mama aikin da yayanmu ya sani tace to na bar wankan naje na gyara mishi dakin zatayi ma su jamila in na dawo sai nayi nima nace to na shiga dakin yayanmu sai yau na yima dakin kallon tsaf,leather sit ne kujerun shi bakake ne masu girma setinau sai kayan wuta kafet da labulaye jajaye dakin sai kamshi yak nan na soma da bedroom din katuwar katifa irin wadda ba asa ta a gado din nan ce sai hanga na kayan sakawa a saman hangar akwatuna ne saiti biyu na dubi hangar rataye da kaya jibge a kan katifar ma duk kaya ne dai dai ko ina kwashe masu datti nayi a cikin wani dogon kwando irin na zuba kayan na gyara uwar daki tsaf sannan na koma falo shima nayi mishi aiki sosai na goge electronics din komai yayi tsaf sannan na dauko turaren daki na feshe ko ina na kulle dakin,na kaima kabir,wanan shine silar fara sani aikinshi na zama mai gyara mishi daki har ya zama dayan key din dakin ma a hannuna yake kullum da safe sai na gyara nake tafy makaranta wata ranar laraba na isa dakin da sauri dan in gyara na tura naga dakin ya bude a raina nace yau yayanmu bai je training bane?na shiga ban ganshi ba na cire hijabina na ninke na ajiye a saman kujera kaina tsaye na shige uwar dakin kayan barci ne a jikina doguwar riga da wando,sam ban san yana bedroom ba na shige toilet na gyara tsaf na fito bedroom din sai a lokacin na kula da mutum kudundune cikin bargo nayi sauri na duba kan gado dan na tabbatar yayanmu ne a kwance,ya kudundune da sauri na juya zan fita sai naji yace zo nan muryarshi irin ta marassa lfy nazo na dan duko yacw ki dafa mani ruwan lipton nace to na fita zuwa dakinmu mama na samu tacw har kin gama?nace ban ma gyara ba don yana nan ne yace akawo mashi ruwan lipton inaga bashi da lfy ne,mama tace ga wannan dibar mashi a ciki na baban sagir ne da yasa na dafa mashi dan yana fama da mura sai dai nasa kayan kamshi,nace zaisha ai yana shan na gida kuma yana sawa na diba na kaimashi na rusuna na bashi da kyar ya mike ya zauna akan gadon ya amsa duk naji banji dadi ba nace yayanmu baka da lfy ne?yace eh nace sannu,haka na koma naci gaba da gyaran falon har na gama na kara lekowa nace sannu na gama ko za'a kawo maka wani abu ne?yace ki shiga ki sanar da hajiyata sannan in ba zakiyi latti ba to ki dafa min indomie nace to cikin mintuna da basu fi biyar ba na dafa mishi hadaddiyar indomie na kai mishi.... Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 Afalo na sameshi zaune kan doguwar kujera yana sanye da singilet da gajeran wando naja dan karamin table din glass din dake tsakar dakin na dora cooler fin a kai na zuba mishi a cikin plste nasa cokali nace a baka ruwa?ya girgiza kai a raina nace yau dai ba danne dannen waya ba tare da ya dubeni yace kin fada ma hajiyata din ne?nace bata bude kofa ba,yace bani waya a cikin bedroom na shiga na wayar na kan katifarshi na dauko na duba fuskar wayar gabana yayi wani mummunan faduwa sakamakon ganin hoton anty mimi a fuskar wayar na kai mishi sañan nace bari na gyara cikin,na shiga na gyara na fito yana cin abinci yace bani abinsha a fridge na bude coke na gwangwani na dauko mishi dan ina yawan ganin gwangwanayen coke din a cikin bolarshi na hado mishi da ruwan Cway na aje na wuce ban wani karya ba shiryawa nayi kawai nasha ruwan tea kadan don kar mama tayi min magana na fito su mami sun jima da shiryawa shi yasa ma ban tsaya saka safa ba,haj yaya mukayi karo da ita ta dawo daga dakin yayanmu ta dubi bilkisu tace yayanku bashi da lafiya ku shiga ku gaishe ahi keda saa da mami sukace to sun shiga ni kuma na tsaya daga waje ko yaya akayi ya ganni sai ji nayi yace ba zaki shigo bane ke? Na shiga da sallama na ce sannu bai amsa mani ba ya cigaba da cewa in kin dawo makaranta ki dafa mani wani abu ,karfe nawa kuke dawowa?nace biyu yace to zan je na ga likitane sai ki samar mani wani abu nace nace me zaa dafa yace komai ma,muka fito su bilkisu sai wai hararata suke yi ni ko tausayin halin da yake ciki shi ya dameni ko a mota sam na kasa sakewa duk tunanina yana can gunshi sai kuma abin da yafi tsaya mani a rai hoton anty mimi dake cikin wayar yayanmu tana sanye da jar riga kanta ba dankwali tana ta faman murmushi duk sanda na tino sai gabana ya fadi a ranar sukuku na yini ko yan ajinmu sai da suka tambayeni nace banjin dadi haka a mota da muna dawowa na kifa fuskata kan jakata ban da tunanin yanda yayanmu ya yini da jiki bana tunanin komai har naga karfin halina irin wannan daga hankali haka,mami ta dafa bayana tace iman wai yau me yake damunki ne?nace banjin dadi ne tace sannu na amsa muna isowa gida kowa na kokarin leka dakin don naga an karo kofar saa ta harareni tace neman suna shishigi babu kwarjini ban kula ta ba na shige dakin da sallama yana kwance sambal a kan 3sitter barci yake amma fuskarshi a sake tamkar yana murmushi don ko idonshi biyu bai cika faraa ba,wayarshi a ajiye kan kirjinshi ina mamakin irin son da yake ma waya na dubi fuskarshi gsky yana da kyau sosai cikinshi a dame tamkar baya cin abinci na kuma duba sa amma shi dogo ne don kanshi a hannun kujerar yake taga ba ma kafar shi ya dora amma duk da haka kafar sai dai karfinashi ne ya haukan hannun kujerar farin gajeren wando da yar tshirt itama fara sune jikinshi,na juya da niyar in fita sai naji ance me kike so?gabana ya yi mumunan faduwa nasa hannu na dafe kirjina jakata ta fadi kasa na kuma kasa juyowa jikina sai rawa yake yi nayi waje da gudu a firgice na shiga daki Allah yasa mama bata falo don haka sai na shige dakinmu,sai da na nutsu sannan na fito na shiga dakin mama ta dubeni tace ya sauran yan uwanki suka rigaki shigowa?nace yayanmu ne ya kirani yace na dafa mashi abinci kuma yaki fada min wane zan dafa yace wai kowanne na dafa,mama tace tunda bashi da lfy ne to ki dafa mashi wake da alayyahu ki sa kayan ciki akwai a fridge ki mishi hadi sosai yanda zai mishi dadin ci nace to.Da yake tun a makaranta mukayi sallah sai na shiga aiki kawai uku da kwata na kammala aikin sai da na watsa ruwa sannan na aiki sagir ya gani ko kofar dakin yayanmu bude take bayan ya duba ina sanye da riga da siket na farin lesi na shiga da sallama shine ya amsa gaba na na faduwa na shiga abinda na gani shine ya tsorata ni,anty mimi zaune a gabanshi a kan kujera shi kuma yana kwance tana rike da hannunshi bansan dalili ba sai naji duk banji dadin ganin haka ba sannan ga wani abu da ya tokare mani kirji wata tsawa da anty mimi ta dakan ita ce kuma silar rudewa ba zaki ajiye abin da ke hannunki bar nan ba?useless kawai kin wani tsaya akan mutane,na ajiye kan table zan juya sai sannan yayi magana yace baki zuba mani ba zaki tafi,,Najuyo da sauri ban dubesu ba na dauki plate daya da na kawo don haka na zuba mashi cokali ma daya na kawo na sa mashi na tura table din gabanshi dan ya tashi zaune,dakin ya dauki kamshin abinci yace ki kawo wani cokali da plate din tace no ba zan ci ba barshi,na bude fridge na fito mashi da coke da ruwa na ajiye tunda na fito nake mamakin yayanmu iya kwanakin da na dauka ina mishi aiki ban taba jin yace mani sannu ba haka ban taba jin yace abincin nan ko dakin nan baiyi daidai ba sam.Wasa wasa na zama baiwa,gyaran daki nice girki nice aike yanzu duk inda naje sai ya jirani na dawo sannan zai aiken abinda ke ban mamaki bai taba nuna min yana jin dadin abinda nake mashi ba sannan uwarshi da kannanshi sun kara sani a gaba wai mun shanye mata da kabir ma ya kan sani nayi mashi aiki amma ba kullum ba kwana biyu uku hakan ya kan ce a share mashi daki kuma idan na dafa ma yayanmu abinci shima ina zuba mashi to a cikin satin nan ya soma aiki shima aikinshi ya ragu, Kwanaki sun shura ana saura sati ukku bikin su Anty Mariya mami take bani lbr komawar yayanmu in anyi biki da kwana biyu nan duk naji ba dadi nace mata sai ya dade zai dawo?tace a'a yace duk bayan wata shidda zai dinga zuwa saboda zancen bikinshi da mami da zaran ta gama HND dinta nace Allah ya kaimu..... Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 Baba shine yayi mana ankon bikin gaba daya ko da yake kala biyar suka fitar shi kuma biyu yayi mana, ana sauran kwana goma biki da misalin karfe uku na Oiyamma ina tsaye bakin kofar yayanmu ina sanye da atamfa sai karamin hijabina mai less fari takalmina fari yayanmu yace nazo zai aikeni kafin ya fito daga daki sai ga wasu abokanshi suka min sallama na amsa sannan na gaishesu suka amsa min gami da cewa mai dakin yana nan?nace yana ciki suka ja fararen kujerun roba da yayanmu ya zuba a gurin suka zauna,sai gashi ya fito guna ya nufo da leda an rubuta SI super market a jiki,yace ga wannan ki hau mashin ai kinsan gidan su mimi ko?nace e yace to ki kaimata kuma ki yi sauri yanzun nan,ga wannan ya miko mani dari biyar na fita ba wai don nasan gidansu anty mimi ba bana dai iyayi mashi musu ne,bansan dalili ba na dai san malali suke,gidansu Amira na shiga sannan nace don Allah ta kira mani mami da wayarta mami tace gata nan ma zuwa gidansu Amiran dana soma mata bayanin cewa ta min kwatancen gidan su Anty Mimi sai tace min me zan je inyi?nace yayanmu ne ya aikeni,suka rakani su da Amira don na hau mashin tayi ma mai mashin din kwatancen inda zai saukeni muka tafi yanda Mami tayi mani kwatance haka nabi bayan na sauka a mashin nan da nana sai gani a gidansu anty mimi na shiga kannanta na samu suna wasa a harabar gidan sune suka yi min jagora har ciki nan na sami Haj Laura da wata kawarta suna hira na gaishesu da farko bata ganeni ba sai da na gaya mata daga inda nake sannan ta murtuke fuska tace zauna nan na zauna.Ta daga murya ta kwala ma Mimi kira kan Mimi ta fito sai wannan kawar tata take tambayarta wannan yar gidan wacece?maman tace yar gidan kishiyar hajiya ce yar'uwata itama ta yatsuna baki tace ai har ta haifi yar da takai girman haka?ko ba amaryasu ba?tace itama mana amma ai wannan agola ce sai shegen kankanba kan ta kuma cewa wani àbu sai ga Anty Mimi ta fito tace gani Mumy, Hajiya ta dube ta sannan ta nuna mata ni tace ga mai nemanki nan muna hada ido gabana ya fadi tace meye kike nemana?nace yayanmu ne ya aikoni tace yace me?na isa gunta nace gashi yace na baki ta dubi kayan tace duk gidan ba zai aiko kowa ba sai ke ko?shegu mayun asiri ni dai nayi shiru na kasa magana,Haj laure dake zaune can gefe tace to ko bata kayan ta maida mashi mana,tace tabdi ai shi momy daban yake in har na bari aka maida kayan nan ai sai nayi dana sani,ta fincike daga hannuna tace ai zamu hadu ni dashi,a raina nace kamar zata iya mashi wani abu,ina jinsu sai faman masifa suke nace ai sai kuyi a raina,ina fitowa daga gidan na soma raba ido ko zan ga mai mashin amma ban gani ba na soma tafiya sai naji ihu ban juya ba naci gaba da tafy mai motar yaja ya tsaya ya fito ya biyoni yace ke yan mata ina magana,na juyo cikin dardar don ban taba tsayawa da wani ba nace lfy?ya ce kalau in har ba zaki damu ba ina son sanin sunanki nace don Allah mallam kayi hakuri,nacigaba da tfy ganin yana ta bina gashi ban sami mashin ba ko wane yazo sai ka ganshi da mutum akai nace sunana Amira yace to ina ne gidanku nan dai nayi mashi kwatancen gidansu Amira muka rabu dashi lfy,da kyar na samu mai mashin na isa gida in da na bar su yaya nan na samesu na dan rusuna nace na kaimata yana sanarshi(wato danna waya)ba tare da ya dubeni ba yace ki shiga daki ki dauki wata leda ke ma kije kiyi amfani dashi nace to nagode kwarai,bai amsa ba na mika mashi kudin hanuna nace ga canjin kai kawai ya girgiza mani na nufi dakinshi,irin ledar da ya aike ni da ita ce akan kujera don haka nasa hannu na dauka na nufi cikin gida ni da mama muka duba less ne me shegen kyau kala biyu sai wani yadi mai santsi shima kala biyu takalmi da jakka kala biyu mama tace kin gode,nace mama ki bani da na kamu dana su Jamila sai na kaima yaya Sulaiman a tudun wada tace sai dai gobe nace mata dama ai. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 A ranar yaya Abubkr yazo da daddare kofar gida ya tsaya ya aiko Kamal wai nazo,na fita muka gaisa muka shiga hirar duniya can ya ce kanwata yau nazo da alamurra masu girma nace to yace zancen na zama ne na isa kofar dakin yayanmu ganin baya nan sai na dauko kujerun shi na robana aje mana a kofar dakin yaya kabir muka zauna ya dubeni yace lman nace na'am yace ya kamata ace tuntuni kinsan inda nasa gaba,nace kamar

Chapter 3 of 7