Share this page
4 / 7
yaya kenan?yace yau dai na gaji ina son in fadi maki cewar ina sonki kuma da aure ba da wasa ba,nayi shiru don banyi wani mamaki ba don na kula da hakan shima yaya Ibrahim kwana hudu kenan da yazo min da irin wannan maganar,yace sister naji kin yi shiru,nace to me zance?gasky yaya ni bazan boye maka ba karatu zanyi har sai naga karshen biro,ya tsura min ido sannan yace in har zaki yarda ki aureni to ni kuma na miki alkawarin zan jira ki,na dan bata fuska nace gsky kar katsaya jirana don ni sai nan da shekara ashirin zanyi kai kuma kila a lokacin kace na tsufa ko ni naga tsufanka,yace inda so ai tsufa ba matsala bane nayi shiru ina tunani shi ma fa haka mukayi dashi (wato yaya Ibrahim)sam wai jirana zaiyi,yaya abubkr yaci gaba da matsa min nace yaya mubar maganar nan in lokaci yayi sai ayi na sako mashi wani zancen muna cikin hira yayanmu ya dawo a motarshi na raya a raina cewa daga gidansu Mimi yake sai kawai naji banji dadi ba kuma wancan abin dake samani nauyin kirji ya taso,sau daya ya dubi inda muke ya shige dakinshi sai naji ma duk hirar ta gunsheni nace da yaya Abubkr zan shiga gida yayanmu ya dawo kuma fada yake mana ya dubeni yayi shiru sannan yace har yanzu bakida waya a hannunki ko?nace eh amma mama tace ina gama secondary zata sai mani ya juya gefenshi ya dauko wata leda yace min gashi wannan ni na sai maki ba Baba bane bare mama tace ki maida,nace to bari sai na fara fadi mata in ta yarda sai na amsa yace dole sai na amsa ko ya kwana a gidan nan,dole na amsa yana tfy na dauki kujerun yayannu na nufi kofar dakinshi cikin sanda na ajiye zan tafi naji yace wanene a nan?nace nice yace me kike nema?nayi shiru sai gashi yazo bakin kofa fuskarshi a murtuke yake magana wayace ki daukar min kujera? nayi tsuru tsuru yace wannan shine na farko kuma inason ya zama na karshe kar ki yarda ki kuma daukar min kujera ko ni sa'anki ne?nace a'a na durkusa nace yi hakuri bai min magana ba ya wuce daki ni kaina dari dari nake bansan yanda zanyi da waya ba. Washe gari nayi kuru da safe na nuna mata tace ke bakya jin magana ko?nace miki sai kin kammala karatunki sannan zaki ci gaba sai na sai maki waya amma kinje kinsa Abubakr ya sai maki ko?to shi kenan,na soma hawaye ina cewa wllh mama bani na sashi ba tace ki maida mishi in yazo nace to har tara na safe ban daina kukan wannan magana ba ni ba wai wayar da Mama tace kar inyi amfani da ita bane ya dameni a'a sai dai ganin da tayi tamkar na roka,tafe nake ina share kwalla zanje gun mamansu Amira in amso ma mama kanunfari zata yi ma su sagir kulin kamu yaya Kabir naci karo dashi zai shigo gidan yace Iman me ya sameki?na cigaba da kuka yana ta magana nayi shiru,yace nasan su hajiyarmu ne ko?nan nayi magana nace basu bane ni da mamanmu ne,yace duk yanda akayi kece kika tabo ta nace wani ne ya saya mani waya shine take ganin kamar na rokeshi ne,yace to ta kwace wayar ne? nace nifa ba kwace wayar ne ya bani haushi ba,yace na fahimceki kafin ya kara wata maganar sai ga yayanmu sun nufo cikin gidan shi da Anty Mimi shima ya ja birki yana ce ma yaya Kabir brother me ya sameta?kabir ya soma yi mashi bayanin cewa bafa wani abu bane wai yayanta ya bata waya shine maman Sagir tace wai ta rokeshi ne,ya dan dubeni sannan ya dubi yaya Kabir yace to yanzun ta kawo karanta ne? yaya Kabir yace no na dai tambayeta ne shine take min bayani,ya dubeni yace wannan marar kunya da ya zauna mani a kujera shine yayanki?daka mani tsawa yayi nace shine yace good gara da ta kwace wannaki bashi da kunya bai iya gaida mutane ba sai aikin kallon mutane don haka in ya kuma zuwa kice mishi ya tsaya daga bakin gate sannan ki san kin maida mishi wayar nan,a fusace ya yi cikin gida daga ni har yaya Kabir da kallo muka bishi Kabir yace ki tafi inda aka aikeki,na tafi ina mamakin wannan karfin hali wai (barawo da sallam) Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 Ashe yana shiga gida dakinmu ya shiga dama shima duk safiya yakan shiga falonmu ya gaida mama tamkar yanda yake gaida mama tamkar yanda yake gaida sauran matan babansa,bayan sun gaisa ne sai yake ce mata maman Sagir mai ya sami yarinyar dakin nan na ganta tana kuka? Sai mama tayi mishi bayani ta kara da cewa nasan ba zata rokeshi ba na dai mata haka ne don kar ta kuma karbar wani abu gunsa,yace hakan na da kyau ta maida mashi zan sai mata waya bansan bata da waya ba kuma sanda na dawo ban san tana nan ba,mama tace ka barshi kawai yayansu nima zan sai mata nafi son sai sun kammala krt don yan satittuka ne suka rage masu su soma jarabawa yace haka ne in ta gama ko ba na nan zan aiko mata da waya,mama tayi godiya sannan ta kara da cewa ga kuma dawainiyar kayan da ka sai mata jiya an gode,na dawo na samu zai fita daga dakinmu na dan dube shi harara ya watsa mani nayi sauri na dukar da kai,na shige daki. Sam ya manta da cewa tare da Mimi suke sai da ya shiga dakin Haj yaya sannan ya ganta zaune tana cika tana batsewa ya zauna a kan kafet din dakin kasancewar mahaifiyarshi tana kan kujera ya gaisheta ta amsa a ciki ciki sannan tace kai wai ba zakaji magana ba ko?ya dubeta yace haj me ya faru?tace ai kafi kowa sanin abinda ya faru don tsabar iskanci ku taho da mimi amma ku taho amma sai ka bar ta anan tana ta faman jiranka kuma kasan makaranta zata je tace tun tara take da lectures yanxu goma da rabi a ina kasa gaba?kafin yayi magana mimi tayi saurin cewa wurin fa bakar yarinyar nan ya tsaya wai sun ganta tana kuka suka firgice shida Kabir sai tambayarta sukeyi ban.......tsawa ya daka mata ke shiga hankalinki ni sa'anki ne?uban wa yace da zaki makaranta ki biyo ta nan?me zan miki?karki sa ma bakinki kwado zaki sha mamaki duk sanda ana min magana kika tsoma baki ya nuna kofa da hannunsa yace see your way,fita a nan ta mike jiki na rawa mama ki daina min fada a gabanta kin manta ita ce matar da kika zaba mani na aura?zata raina ni ne hajiya in kina min haka a gabanta har tana sa baki dan raini,wllh taci albarkacinki ne da sai na mata dukan tsiya,ya cigaba da cewa bata san cewa ni saboda ke ni zan aure ta ba ba wai don tayi mani ba?haj yaya tace tsaya tsaya ba na son cin fuska ka manta ni da uwarta nono daya muka sha?bayan haka ma mimi bata da makusa ubanta balarabe ne ka kuma sani inma ilimi ne akan nema take gashi tana sonka sosai amma kai sai faman goce goce kake yi shi yasa na canza shawara kafin ka tafi sai an sa ranar aurenku,ya dubi haj yace ki dai yi hakiri na dawo don kar aje ana dagawa tace sam ban yarda ba yace to shi kenan ta juya zancen dake cewa wacece take kuka ku ka tsaya kai da Kabiru?yace waccan yarinyar da nake aike ce,nan ta hau bala'i da masifa tace dama in banyi da gaske ba sai Habiba ta shanye min yara yanda ta shanye babanku kallonka kawai nake yi wannan mummunar yarinyar yanzun itace abincinka gyaran dakinka,aike yanzu itace tunda haka kafi so ai sai kayi sauran ka ka soma kai shawara gun Habiba haka tayi ta sababi yana bata hakuri har dai ta sauka,Niko tuni nakai dinkinmu gun yaya Sulaiman nan da nan kuwa sai ga kaya ya kawo,na rakoshi zai hau mashin nan mukayi kicibis da yaya Kabir suka gaisa da yaya Sulaiman ga mamakina sai naga yaya Kabir ya daure fuska ya dubeni yace na lura baki jin magana ko Iman?me yaya Abdulrahim yace maki?na dibe yaya kabir nace ai to wannan ba yayan da ya bani waya bane wannan wani ne bai saurareni ba yayi cikin gida muka fita ina ta mamakin wannan abu da yaya Kabir yayi na dubi yaya sulaiman da nufin nayi magana sai kawai shima naga yayi fuskar shanu(wato ya hada rai)yace wannan kuma wanene?nace yayanmu ne yace ni ba wani yayanku na kula ke sam baki ma san halin da nike ciki ba ko? gabana ya fadi nace me kake nufi?yace ina cikin mayen sonki,na dade da yin nutso cikin kogin sonki don Allh ki taimaka min da ganin wannan da ya wuce sonki shima yake yi,nan take hankalina ya tashi na gudu nayi cikin gida dakinmu na fada na kwanta a kan gado rigingine nayi fuskata na kallon silin na soma tunani, yaya Abubakar sona yake,yaya Ibrahim sona yake,yau ga yaya sulaiman da wannan zancan har kuma yana tunanin wai shima yaya Kabir sona yake, ban ganeba? na mike zumbur tamkar an tsunguleni nace da na shiga uku ni Iman muddin Haj Yaya taji wannan lbr na ciji yatsana na soma sintiri a tsakar dakin tabbas da zan so yaya kabir ko ba komai yana dan yanayi da yayanmu wata zuciyar tace min in yana yanayi da yayanmu shi kenan sai ki soshi a matsayin da yayan naku ya taka a zuciyarki?shin kina neman ma kanki rigima da mahaifiyarki?menene laifin Abubakar da ba zaki soshi ba?ya jima yana maki dawainiya dake in ba ki son shi ga Ibrahim nan shima dan uwanki ne sannan in dama za kuyu adalci to da Sulaiman kika zaba ki tuna shine yake maki hidima ta fannin dinki tun kina karama har yau dinnan shi ke maki dinki, ****hhh! Lallai yariya taki tasameki,duk cikin wayit blood ne***** ban san shigowar mama ba sai dai naji an girgiza ni sannan nayi sauri na jiyo cikin tsoro naga tana kallona tace iman me kike tunani haka?na shiga uku ni Habiba na soma in ina,ina cewa ba komai ta girgiza kafaduna da karfi cikin daga murya murya tace kinsan tsawon lokacin dana dauka ina maki magana nan kuwa baki sani ba,na jima a nan ina kallonki kina safa da marwa tamkar wadda abin duniya ya dama,ta ja hannuna muka zauna a bakin gado ta sanyaya murya tace Iman sanar dani matsalarki don baki da wanda ya fini kuma na jaki a jikina don irin wannan ranar wato don neman shawara kar kiji komai sanar dani ta fada tana kallona nayi shiru ina tunanin mama gaskiya dole ne ma na sanar da ita sai dai ba zan gaya mata maganar kabir ba, na dubi mama nace yayyena duka uku sune suka sani shiga wannan tunani,tace kamar yaya?na dukar da kaina kasa sannan nace yaya Abubakar da yaya Ibrahim da kuma yaya Sulaiman kowanne yazo wai yace yana sona,Mama tayi shiru kamar ruwa ya cita tace ke me kika gani?ta cigaba da cewa Abubakar da ne ga yayar mahaifinki cikinsu daya,Ibrahim kuma dan kanin mahaifinki ne da suke uba daya shi ko Sulaiman dan wana ne nima cikinmu daya sai ki fadi min wanda kika zaba?nayi shiru tunani ya dawo sabo mama tace ba tunani zakiyi ba sanar dani abinda kikace masu ke kin amsa musu dukansu ne?nace aa duk hakuri na basu,nace ni karatu zanyi amma tamkar sun hada baki kowa sai yace zai jirani yaya Sulaiman ne ma ban tsaya yi mishi magana ba,mama ta dafa ni sannan tace yanzu gaya mani a cikinsu wa kikafi so?sai na baki shawara nace gsky mama ni cikinsu bana son kowa,ta mike tana fadin alhamdll gara hakan don dama ko da dole sai na zabi daya ne,to nace gara Sulaiman yaron na da mutunci,kuma naji ma ina fuskantarshi game da ke ma na dade da gane cewa sonki yake nayi kwadayin dama shi kadai ne yace yana sonki taci gaba da cewa yanzu in naceki amince dashi sai ace don yaron danuwana ne shi yasa don haka ki kwantar da hankalinki kinga jarabawa na matsowa kar ki yarda na kuma samunki kina wannan tunani ba yarda za ai ki auri wanda bakiso ba mai matsa maki don karatu ma zakiyi,haka mama tayi ta lallashina har dai na saki jiki sai dai a raina maganar yaya Kabir itace a raina. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 Tun ana saura kwana uku bikinsu anty mariya dangi suka cika gidan,fannin Haj Shuwa da yanuwa Haj Yaya,sai yan uwan Alh Mukhtar wato yan maska Aunty Mimi ma a ranar tazo don ranar ne za'ayi dayis,yayanmu ranar bai wuni gida ba sai yamma dama ni banje masu wurin da suke yin lalle ba nida Amira mukaje mukayi kitso sannan mukayo namu lallen a can don dama mu ba ma saka mai a kanmu. Misalin karfe biyar na yamma yayanmu ya aiko Kamal ya kira ni nazo yace na kawo masa wani abu tabawa in akwai dan yinwa yakeji na koma ba wani abin kirki sai na rana kuma ya huce nasan ba zai ci ba,don haka sai na dafa mashi indomie da kwai na kawo mishi natarar da Aunty Mimi a dakin sai naji raina ya baci na ajiye zan juya yace ke kizo ki zuba mani mana na dawo sai tace ka barta sai na zuba maka ,bai dubeta ba yace min samin mana kina kallona baki sanni bane?nayi kasa da kaina sannan na zuba mishi na dauko mishi coke da ruwa sannan na juya zan fita sai naji yace shiga bedroom ki dauko wayarki tana nan a kan katifa,na dauko sannan nayi mashi godiya,washe gari a command quest za'ayi kowa ya shirya cikin anko nima na sanya nawa ankon nayi kyau sosai na fito harabar gidanmu a nan ne ake daukan yan matan tuni kowa ya tafi sai Amarya da kawayenta wadannan kuma bana tunkare su ba itako mami tuni dama tana can don sune masu shirya gurin dasu bilkisu da sauran kawaye,ina tsaye na jingina da bangon dakin yayanmu ina kallon kawayen amarya suna ta kai da kawowa kowacce na rike da waya tamkar masu gasarta nan na tuno da tawa mama tace na aje sai mun gama zana jarabawa ina wannan tunanin naga anty mimi sun fito itada yayanmu itama anko ne a jikinta irin nawa tayi matukar kyau dama anty mimi ba dai kyau ba gata fara yanda mami ke gaya mani mahaifinta balarabe ne zamanin da Haj Laure mahaifiyarta suke zuwa kano to jidda a can Allah ya hadata da wani balarabe ta aura shekarunsu ko goma ne da aure ya rasu lokacin Anty Mimi na shekara shidda shine ta gudo da ita ba tare da sanin dangin babanta ba,sannan ta sake aure shine ta haifi yaya uku sanda naji wannan lbr a raina nace ashe jirgi daya ya debomu ni da ita.....Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 DOCUMENT CREATED BY ZAHARADDEEN SHOMAR WHATSAPP 08168575100 Tawa Tasameni 1-03 Posted by ANaM Dorayi on 02:31 AM, 29-Dec-15 Under: TAWA TASAMENI __________NA HALIMA ABDULLAHI K/MASHI Garama ni ubana yana nan, haka danginshi, nayi nisa cikin tunani na ji horn ba karewa na juya can wajen da ake horn din bakin gate sai naga ashe su yayanmu ne zasu tafi ban fahimci wai ni suke ma horn ba sai da anty Mimi ta bude gaban mota tace ke na dubeta na dafa kirjina nace ni?eh da Allah zo nan ana maki horn kinyi banza da mutane, na nufi gunsu ina zuwa naga yayanmu ya sako hannu ya bude baya yace shiga,gabana na faduwa na shiga motar don nasan ba wanda ya taba shigarta a yan gidanmu sai yaya Kabir na zauna sannan na rufe sanyi da kamshi sune suka ziyarceni tamkar wata munafuka haka na zauna a motar kaina a kasa, suko suna ta labari bana jin dai muryar yayanmu sai ta anty .Mun yi nisa sannan na dago idona sai kawai muka hada ido da yayanmu ta madubi nayi sauri na sunkuyar da kaina kasa har mukaje ban tanka ba,ban kuma daga idona ba,sai da naji an tsaya sannan na dubi gurin yan mata ne cike na buda zan fita sai naji yayanmu yace karba,na juyo sai naga yana bani kudi ne sababbi yan naira hamsin na amsa nace Allah ya saka da alkhairi,anty Mimi ta shaka sosai da na kalli fuskarta ni dai nayi ciki ko zan ga Mami, ana cikin hidima shalele suka kira don haka gun ya cika da karan kidan police band Sa'a tazo tace kije ana kira gabana yana faduwa nace inji wa?ta harareni dole sai kinji? ki zo mana na bita can baya mukaje ganin Anty Mimi da Amare da kuma kawayensu yasa wata faduwar gaba ta sameni na dai daure na isa wurin,Anty Mimi ta kai mani rankwashi akai tace ina jakarki?nace tana gun Mami tace nawa yayanmu ya baki?nace ban kirga ba nan ta shiga zayyane masu wai wannan wace irin yarinyace,Anty Hadiza tace ai wannan daga ita har uwarta annoba ce,Anty Mimi ta cigaba da cewa kunga jiya a gabana ya bata waya irin tawa ce sak koda ganin kwalin sannan yau zamu taho nan ta zo ta rabe ya dauko mu tare kunji biyu,cikon na uku kuma sai gashi ya raba mana kudi kilan ma daidai ya raba tamkar wasu kishiyoy,nan suka taru a kaina wannan ya kai mani bugu kowa dai na fadin albarkacin bakinshi, Mami ta iso daidai lokacin da wasu kawayen Anty Mimi suke cewa asiri tayi mishi daga gani,in ba haka ba me zaiyi da wannan mummunar yarinyar gara ma ki dauki mataki tun da wuri akan abin, Mami tazo tana cewa Anty Mariya kuzo anguna sunzo fa ana ta nemanku,kan suyi magana Anty Mimi tace Mami muga jakar wannan jakar,sai sannan Mami ta ganni ina kuka tace Iman menene?Bilki tace ba'a sani ba ke dai ki bada jaka a kace Mami tace bazan bayar ba nace Mami bata ta mika mata sai da suka kirga kudi daidai da nata dubu ashirin da biyu ne dama ban kirga ba,saura sukace kar ki bata ko sisi Mami tace wllh sai naga ya wa yayanmu in har kika dauki kudin nan,Anty Mimi ta watso kudin da jakar a jikina sannan tace ki jira abinda zai biyo baya ta wuce sauran suka bi bayanta aka bar daga ni sai Mami inata kuka,Mami ta kwashe tana tambayata abinda ke faruwa na zayyane mata komai itama na kula ta dan yi mamakin kudin da ya bani tace Iman yayanmu yana ji dake fa nace Nami ku kula da wani abu daya yayanmu nice nake mashi aiki,shiyasa yake mani alheri amma wai suna zargin wai yana sona ne ni nasan ko mata sun kare yayanmu ba zai taba cewa yan sona ba ke kinsani balle yana da kamar Anty Mimi,Mami tace ai itama anty Mimin ba wani kyau ne da ita ba uban gashi ne kamar jirgi ya daso tasha kuma a tsaye take ba wani diri kirji kamar na bera ba wasu nonuwan kirki nace to shi dai tayi mashi Mami tace ke zo muje ba wani yi mashin da tayi kawai saboda mamansu zai aure ta. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 TAWA TA SAMENI,haka na fada ranar daurin auren anty mariya ba wani abu yasa na fada ba sai ganin munsa less iri daya da Anty Mimi wato wanda yayanmu ya bani nasa daya daga ciki me ruwan lemun tsami takalmi da jaka iri daya itama ni take kallo ta zauna kofar dakin yayanmu a fararen kujerunshi ranta yayi matuka gun baci naga ta yi cikin gida ni kuma sai na nufi gidan su Amira,dama dazun ta aiko Faruq wai ta dawo dama jiya ne ta tafi unguwar dosa gun kanwar mamansu da suka dawo kwanan nan shine taje kwana,ta fito wanka na sameta nan nake zayyane mata abin dake faruwa ta dinga mamakin karfin halin irin na nasu Aunty Mimi dan yayanmu ya min kyauta ta kara da cewa komai ya sai maki ba zai biyaki ba irin dawainiyar da kike mishi ba nace suna zargin fa wai sona yake yi,Amira tace haba dai nasan ma ba zai fara ba domin kin......na katse Amira nace ni ba ajinshi bane nasan da haka kuma ko mata sun kare ba zai so ni ba Amira tace ba nufi na kenan ba ina nufin matsalar dake tsakanin mahaifiyarki da tasa ai yasan da wannan matsalar ba zaima ce yana sonki ba.Nace ato su sai hauka suke yanzun nan na hadu da anty Mimin shine ta ganni da kayan nan har jakar to tayi cikin gida ban san me zai faru ba,dama bikin nan sai yan tsegungumi sukeyi dangin Haj Yaya naci gaba da cewa kinsan abin da ya faru ne da babansu Mami ya tambayi Haj Yaya game da kayan da za'a siya don yayanmu ya riga ya sai masu sai yace to suyi mashi list din kudin sukayi mashi hauka to hauka mana wai fa miliyan daya da rabi suka rubuta shiko ya kira mama tayi mashi lissafin kayan dakin mata mata har da na jere da na kicin duk ta sanar dashi naji ya bata kudi sukaje ita da Anty Yagana suka sawo mashi komi don Mama cewa tayi sai da tayi ciko suka kawo ya dinga sa mata albarka itama ta bashi nata gudummuwar na zannuwan gado to wannan abin shi yayi matukar tada hankalinsu Haj Yaya da har sunce sam kayan nan bai masu ba shine baban yace yayi in baiyi masu ba to su sai nasu da kudinsu kafin Amira tayi magana sai ga Jamila kanwata da kukanta wai ana fada da Mama nace mama da wa tace Mama da mutane yan biki nace yau mun shiga uku ko takalma bansa ba na nufi gida Amira ta biyoni,tun a harabar gidan nake jin hayaniya yaya Kabir na gani ya fito daga cikin gidan ranshi a bace da ganina ya nufoni yace kar ki shiga zo nan,na soma kuka ina cewa ni dai na shiga uku ya ja min hannu zo muje karki shiga,nace ina kuka yaya Kabir barni naje naga Mama yace Mamanki tana dakin Alhajinmu zo muje ya jani dakinshi ya zaunar dani kan kujera sannan ya tsugunna gabana yace kiyi shiru zan tambayeki ne,nayi shiru ina share hawayena yace yaya Abdulrahim yace yana sonki? nace aah yayi ajiyar zuciya sannan yace alhmdll yayi shiru zuwa can yace a gaskiya Iman na dade ina sonki shiyasa ma har yau na kasa kula duk wata ya mace da sunan so na mike tsaye na ce Kabir tun ina ganinka da gashi kar ka yarda na kuma jin wannan zancen kana ganin balain da muke shiga kullum a gidan nan sannan zakace wai kan sona ni dai ba ruwana,ya zaro mani ido gami da tasowa kamar zai bugeni yace sai kin soni kuma ni da ruwana ba abinda ya dameni da fadan iyayenmu,na mike zan fita yace kar ki yarda ki fita su Haj Laure zasu dake ki muddin kika shiga,jin maganar duka ni uwar yan tsoro na dawo na zauna na sanyaya muryata nace sun doki Mama ne?yace suna hauka ne?ita ko kulasu ma batayi ba shine yar Alhajinmu da tazo daga maska tace ta shuga dakin Alhajin tasa na mashi waya yanzun nan yana zuwa shiyasa nace kar kije,na cigaba da kukana yaya Kabir yana lallashina har nayi shiru ya dinga shigar dakan shi a guna yana ce min in na yarda yasan Akhajinsu zai tsaya man kuma zai nemi canjin gun aiki mu bar kaduna haka ya yi ta cusa min raayi har na soma yarda,sai dai ina tunanin mama ba zata amince ba na dai yanke shawarar zan ci gaba da addua. wayar yaya kabir tayi kara yace in dauka don nafi kusa da wayar,na dauka sai naga sunan yayanmu sai na mika masa yace ya baki dauka ba?nace yayanmu ne ban san mai yake ce mazhi ba na dai ji yace gata nan sai na kuma jin yace dakina sai gabana ya fadi,sai naji yace to gata nan zuwa,ya dubeni yace alhaji yazo yana dakinshi an ce kije,nace yayanmu na gurin ne?yace shi ne yayi min waya wai Jamila tace nine na tare ki ina kike yanxu sai shine nace gaki nan ki tafi ko na raka kine?nayi saurin cewa a'a don kar agan mu tare,cikin dar dar na shiga gidan yan biki sai ni suke kallo gashi ko takalmi babu a kafata na shiga ciki nayi sallama a kofar falon Alhaji na shiga Alhaji na kan wata kujera irin ta karfen nan ne dama nan ne gun zamanshi sai Mama akan kujerar gefen damanshi dayan gefen Haj Yayace sai Haj Shuwa kusa da ita Haj Kulu na dakin sai yaya ta maska(wato yayar Alhj)yayanmu na kan kafet kusa da kafar Alhaji nima na shiga na samu guri kusa da Mamana na zauna a kan kafet. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 Alhj na gaisar sannan yayi gyaran murya yace to gara ke Murja(haj yaya)menene sanadin wannan fadan?na tambayeki dazu kince sai an kira Iman gata tazo sai ki fda muji ynxu,ta soma magana cikin sababi ni dai Alhj kawai kayi mani tsakani da Habiba da kuma 'ya'yana in kai ta gama da kai to ni da 'ya'yana li'ilafi,,tashanye min yara basa cin girkin kowa sai na 'yarta sannan yanzu shi wannan miskilin dana gani kamar zai zama namiji amma ba haka bane ya tashi sai kashe mata kudi yakeyi harda yi mata anko da matar da zai aura me hakan yake nufi? na dai san rokonshi sukayi don haka ayi mana iyaka dasu ba 'ya'yanta ba nawa,tun da ta soma bata tsaya ba kuma ba a katse ta ba,jin tayi shiru sai na dago kai na dubi kowa kowa dai ita yake kallo sannan na dubi yayanmu wanda kanshi yake kasa Alhj yace to naji naki ke kuma Habiba ya abin yake?Mama ta soma magana cikin sanyin murya lafuzza masu kyau tace ni dai Alhaji a gefena ba wani matsala yarinyar nan dai itace matsalar, da zaka amince min da sai na dauketa na maidata wajen kawunta don inda bata nan gidan da baza ta ga ma 'ya'yan Haj Yaya ba bare su sata aiki sannan muddin tana nan gidan ba zan hanata aiki ma kowa ba har Hajiya Yaya inda zata sata,amma kiyi

Chapter 4 of 7