Share this page
7 / 7
yace kina son Fridge?nace a'a TV fa?nace a'a,Radio fa?nace a'a yace to me kike so?na dubi hotonshi yana sanye da farin JC mai ratsin ja yayi tsalle zai kama kwallo ina balain son hoton ya dube ni shi kike so?na kada kai alamar eh bayan shi fa?nace ba komai ya mike ya ciro min hoton ya hado da wani shima mai kyau cikin jan JC kan kujera ya zauna sannan ya kama hannuna gabana ya fadi naji wani yarr a jikina ya rike yatsuna da zoben nan yake jiki wanda ya kawo min tsaraba kar ki rabu da wannan zoben komin wuya kinji? kasa magana nayi,yace wannan lallan ya min kyau waya miki?kafin na bashi amsa sai akayi sallama gami da shigowa gaba daya tsoro ya kamani da na juya naga Anty Mimi itama tsoron ne da mamaki a kan fuskarta na dubi yayanmu shi ko namijin duniya ko a jikinshi ya saki hannuna yace Mimi lfy na ganki yanzu?ta juya da gudu tana kuka yace me aka mata oho,yayi tambaya ya ba kansa amsa na mike da hotuna sai nayi gidan su Amira ban koma cikin gida ba ita ko Anty Mimi dakin Haj Yaya ta nufa da kukanta da komai,ta sanar da hajiyan komai haj yaya ta cika tamkar zata fashe ta dubi mimi tace kince yana rike da hannunta?Mimi tace sai kallon juna suke yi,haj yay tace lallai ma yaron nan jiya fa haka su Bilkisu suka ce min sun ga ya shiga mota da ita banyi maganin abun ba bari in kirashi,ta soma daddana waya tana fadin kannanshi bai taba sa su a motarshi ba sai wannan bakar mummunar yarinyar,ta soma magana kazo yanzun nan ta kashe wayar taci gaba da fadin sun asirceshi shima kamar babanshi na shiga uku ni Murja tsakanina da Habiba Allah ya isa ban yafe mata ba,yayanmu yayi sallama ya shiga dakin tana zaune kan kujera sai cika takeyi ya ballama Mimi harara sannan ya shiga ya zauna,duban wulakanci ta mishi sannnan tace yanzu kai saboda Allah me ke tsakaninka da yarinyar nan Iman yar karama da ita shine ta ke juyaka ta shanye ka nan gaba ma kila kace aurenta ma zakayi ko?ya sunkuyar da kai kasa bai amsa mata ba tace jiya ina kukaje?yace Haj waya kawo maki wadannan kananan surutan ne?nifa mutunci ne tsakanina da yarinyar nan tana hidima dani sosai don Allah haj ki daina jin zancan mutane yarinyar nan ita da uwarta suna da kirki kum....ta katse shi an baka kaci a cikin abinci ba dole kace haka ba na gaya ma ka koyaya ni zan mummunan saba maka ta nuna Mimi wannan ita menene laifinta?da zaka sasu a kasuwa sai kowa ya riga zabar Mimi kuma zanyi maganin agola a gidan nan wayarta tayi kara ta dauka ta duba ka dai ji na gaya maka ga babanku nan ma ya dawo shi ne yake kira bari naje,ta dube shi sai ka bata hakuri ai,tana fita ya galla ma Mimi harara sannan yace ke ma zan yi maganinki bakina hada ni da uwata ba ya mike ya zo kusa da ita wllh wllh in kika kuma hada ni da ita sai na fasa auran nan ke ko an daura sai na sakeki akan Iman, Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 Yayi waje ya barta cikin mamaki da tsoro koda haj yaya ta dawo bata sanar da ita yanda suka yi ba ta dai ce ya bata hakuri ya tafi haj yaya tace ai nasan zai rabu da yarinyar nan sai ma kin shiga gidanshi Mimi tace haj ce min yayi fa in anyi bikinmu da sati biyu zai tafi england ya barni dama yaje dani don akwai masu mata a can,haj yaya tace gsky haka za'ayi sai dai za'a yi fama kafin ya yarda na ma huta hankalina ma ya kwanta baya kusa bare in ta fargaba kar yace yana son yar iskar 'yar can shima Kabiru zuwa zanyi na matsa mishi yayi auran tunda yana aikinshi dama jira nake yayanshi yayi tukunna cikin farin ciki Mimi ta fita ta san da haj yaya ta mishi magana shi kenan zai yarda su tafi tare. Da yamma na dawo daga gidansu Amira in da ta nuna min gwaggwaro ba tace don Allah kisa yammata kowa zai sa mu uku iri daya ?ami ta sai mana kalar namu daban ne ma nace to in ya shiga da kayana zansa danni ba anko zan sa ba tace me zaki sa?nace kayan gun yayanmu,a falonmu su hajiyar maska ce da sauran dangin alhj wadanda suka zo biki na rusuna na gaishe su sannan na shiga dakinmu sai da naci abinci sama sama sannan nayi wanka ina gaban madubi ina shafe shafe waya tayi kara na dauka ga mamakina sai naga lambar yayanmu ina da lambar amma bai taba kirana ba nima ko da wasa ban kirashi ba nasa kunnena ban ce komai ba inaji yace hello?sannan yace kina jina?a kasalance nace umm da wani abu nake ji yana fita daga wayar zuwa cikin kunnena yana raba ma jikina qani sako ne mai wuyar fassara yace me kike yi yanzun?na samu kaina da rike murya nace mashi ina shafa mai ne yace to kiyi kwaliya da kyau amma kar ki kula ko wanne saurayi kinjini?nace eh dukkanmu muka yi shiru bai kashe wayar ba nima haka can yace to sai mun hadu a can ya kashe na rungume wayar a kirjina ina jin tamkar shi na rungume,soyayya kenan ban taba tunanin akwai ranar da zata zo na shiga irin wannan halin ba sai gashi yanzu ina ta nutso cikin kogin son wanda bai ma san inayi ba,Allah kenan shi ne mai iya sanya fari ya koma baki.Kwaliya sosai nayi tamkar ni ce amarya nasa lesa din da ya umarceni nasa ya shiga da gwagwaron sai takalmi da jaka su ma kalan gwagwaron ne ni kaina dana dubi madubi sai da naji tsoro don kyan da nayi wayar Mami na kira tace min tana can hotel din na kira Amira tace min tana mota ne taga an gama kwashe mutane shine taga kabir ta tambayeshi ni shine yace kamar ya ganni a can ace mata ina gida ko fitowa banyi ba na mike na cire gwagwaron na rike na fito falo dankwalin na rufa kaina nayiwa mama sallama tace kai kin ko yi kyau,iman yau dai ba zancan hijabi kenan?nayi murmushi na fita ina isa harabar ajiye motoci duk an gama kwashe mutane sai kawayen amarya na nufi waje da nufin in hau mashin sai ga yaynmu shi da Nasir da wani abokinshi ya dubeni yana daga cikin yayi min alamar in tsaya da ido na ko tsaya ya fito ya kirani gefe yace kin ganki kuwa?kinyi kyau fa nace nagode yace to ya baki tafi ba?nace ai yanzun na fito shine naga an watse sai kawayen Amarya yace kina da kudin liki ne?nace ina dasu amma ba sababbi bane yace ok bari mu shiga ki amsa na bishi abokanshi na zaune a falonshi ya shige uwar dakinshi jim kadan yace Iman na ce na'am yace zo na shiga da sallam ya amsa sannan yace shigo mana kin tsaya nan kudi na gani a kan katifarshi ga yan ashirin ga yan hamsin har zuwa dari biyar,ya dubeni dauka wanda kikeso na sa hannu zan dauki ashirin ya dafe hannuna sannan yace ki dau wannan yan dari biyu ne,ya samin a tafin hannuna na gode na fada ina kallon idonshi,Man din akwai sirrin kyau mai birgewa muka fito falo ismail ya dubeni yace kai maska wannnan yarinyar ko dai kai kake ma kanka farauta ne? Sai naga yayi kicin kicin da fuska ya harari Ismail yace ku kun cika yarda girma ban da yarda girma menene na cewa inayi ma kaina farauta? bani son haka,jikina yayi sanyi zan fita yayanmu ki jirani zan sa akaiki Ina tsaye a bakin gate yazo ya dubeni menene kike bata ranki?na dubeshi ba komai ya juya ya kira musa musa direba yazo yace ina zaka na ganka da key a hannu?yace haj ce ta aikeni gidan haj laure,yace to ka kai Iman gurin party nan hotel yace to can na sami su Mami da kowa yana ta hidimominsa inata neman Amira sai can ita ce ma taganni muka zauna kujerun gaba na ce uwar sauri shine kika wani taho Amira tace kar kiga laifina yayanku Kabir shi yace min kina nan,nace don ni ce zan shirya gun ba?dole na riga kowa zuwa yana sani don dai ya dauke ki ne ta ce anji ki min shiru mu bar zancan.Biyar saura ango da amarya suka zo less dina na gida irinshi amarya tasa nace gara da na sa wannan din na dubi ango sanye yake da wata dakakiyar shadda ruwan sararin samaniya tamkar less din jikina ina cikin mamaki Amira tace kunyi anko ke da ango sanya gwagwaron ki nasa na gyara cikin raina nace kila ma don muyi anko ne yasa yace nasa,mai gabatarwa ya fito yana kiran kawayen Amarya bayan bude taro da addua suma abokan ango an kirasu yawanci duk turawa ne,sai kadan,Nasir da Mami aka hadashi tako sha harara gurin ango can aka kira sunana Iman idris zata ba amarya shawara ba don na iya turanci ba da nasha kunya Amarya ta cika don haushi niko duk na tsargu Amira tace don Allah tashi kije mana nace Amira bansan me zance ba dadai tun a gida ne aka sanar dani da na rubuta ana ta kiran suna na na dubi yayanmu yamin kar da ido fuskarshi ba walwala na mike daidai lokacinda mai gabatarwa yace ko bata nan ne?Iman Idris a hankali nake tafiya har naje kan abinda aka tanada don hawan mai magana da sallama na soma sannan nayi wa Annabi salati kafin na soma bata shawara akan zaman aure na kawo ayoyi da hadisai wadanda sukayi magana akan zaman auren da hakkokin auran kansu. Dana gama na sha tafi gun mutane na koma na zauna haka akayi ta gabatar da komai har zuwa sanda zasu ciyar da juna don kar in gani na dauko wayata ina ta danne danne zuciyata kuwa sai zugi takeyi,can na mike zan fita Amira tace ina zaki je gashi shalele na ta waka yanxun za a soma rawa dole na tsaya suna shiga yayanmu a tsaye yake baya rawa amma Amarya har da juyi nace wawiya ba kunya ba jan aji nice na fara liki ina ta zuba musu kudi cikin dauriya yayanmu ya juyo ya fara zuba min na juya zan fita ya rike min riga amma ba wanda zai kula don ta gefe ya rike ya dan matso kusa da kunnena kar ki fita yanzun ki min rawa din dan ban iya rawa ba nima ai ban iyaba Amarya ranta ya baci ta dubeni ashe ita ta kula da abin da mukeyi guri ya kaure liki wasu sun sha nice amaryar ne?ko ra'ayi ne?oho sai ni suke ma liki gudun rikici yasa na fita abina na koma na zauna,Amira tace yar gori a ina kika sami kudi kike bari dasu?nace shi ya bani dubu ashirin kuma na like musu abinsu Amira tace duka?nace a'a Mami ta iso gunmu taja hannuna zo muje ki dan taka nace bana rawa fa ta dubi Amira tace duk yanda suke da yayanmu wai bazata yi rawa a bakinshi ba Amira tace ai ta basu shawara yanda zasu zauna da juna,Mami tace yauwa na tuna dazun me yace miki da naga ya wani karkato dai da kunnank?nace ba zan fada ba Amira tace ashe kin lura kema?sunyi kyau tamkar itace amaryar nace kun cika sharri Mami tace to zamuje kiga hitunanku da masu hoto sukayi suna ta saidawa a waje mu uku muka fita wajen hall din gsky mami ga hotunanmu nan nida yayanmu wani tare mukayi wani ni kadai wani shi kadai an barbaza wanda yafi birgeni wanda mukayi da yayanmu ya dan karkato yana min magana fuskarshi a sake ni kuma ina murmushi fuskata tayi fayau idanuwana sunyi haske kitsona ya zuba a kafaduna Duk masu daukar hoton nan sai da na bisu na saye hotunanmu sannan muka koma ciki nace kije kunnan gidado tace a ina zaki ganshi ta fita kiran,ni kadai na zauna can ji an min sallama cikin hausa da bata goge ba yace na zauna?nace zauna mana ya zauna nadan dube ahi kamar na so na gane fuskarshi yace baki ganeni ba?nace ban ganeka ba yace abokin Maska da muka zo daga England nace ok na ganeka,yaci gaba da cewa ina sonki amma Maska yace krt zakiyi? nace haka ne yace toh zan jiraki mana nace kayi hakuri dan zan dade ban gama ba,koyaushe zan jiraki,muna cikin hirar ne can idona ya kai Ango da Amarya harara ya sakar min na dauke kaina daga duban gunshi a raina nace kai gara kai ka kama taka naci gaba da hirata jim kadan wayata tayi kara na duba sai naga lambar yayanmu da sauri na dubi gurin da yake bashi nan sai na dauka nace hello ya katseni ki sameni a wajen hall din nan gurin wayoyin nan ta kofar baya na fita da sauri can bayan wasu furanni na ganshi na isa cikin fargaba ya dubeni fuskarahi ba annuri yace me gayen nan yace miki?nayi shiru ba zaki gaya min ba?ya daka min tsawa jikina yana rawa nace yace ne yana sona,da sauri ya dubeni sonki?.Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 Na gyada kai alamar eh yace oh my God bana sanar dashi krt zakiyi ba?to naji me ke kikace mishi?nace nima haka nace mishi ya dunkule hannunshi ya naushi dayan hannun sannan ya dinga kai kawo a filin gun mamakin shiga damuwar dayayi na tsaya yi a raina nace ya bar amaryarshi yana yin abin da bai dameahi ba,kamar ya san tunanin da nakeyi sai naji ya dawo gabana daf dani yasa hannuwanshi ya rike kafaduna yace kar kiga na shiga wannan halin kiyi tunanin inayin shishigi ne a cikin abinda bai shafeni ba,no yin karatunki shine kwanciyar hankalina kuma muddin na yarda wannan dan iskan ya soma cusa maki ra'ayin sonshi to zai min illa domin nasan Adam ba sanin yau ba yana da sa'a a rayuwarshi zai yi wuya ya nemi abu bai samu ba tamkar ni yake,so bazan yarda da huldarku ba,nayi shiru ina tunanin wannan iko na yayanmu tunda yace tamkar shi yake sai ma naji ya burgeni na dubi yayanmu nace to in dai zai bari na gama karatuna why not na aureshi in kasan yana da hali mai.....kafin na karasa sai saukar mari naji cikin firgici na dube shi shima ni yake kallo ranshi a bace,hawaye ya zubo min a kan fuskata yace kina hauka ne?kike kiran wani ya aureki?sai kuma naga yayi shiru ya juya min baya,Aminatu yaja sunan kafin na amsa sai ya juyo da sauri ya zo guna ba zato sai gani nayi ya rungume ni tsam tsam a jikinshi gabana yana faduwa jikina na kyarma amma na kasa kwacewa ,nama kasa kokarin kwacewar gwaggwarona kaina ya fadi gashina ya bayyana a waje kitsona ya sauka a kan kafaduna ni kam tamkar an jona ni a lantarki haka nake jina,cikin sanyin murya yake magana,Amina bana son ki saurari Adams zaiyi ma rayuwata illah nafi son sai kin gama karatu ne kafin ayi maganar auranki,ki fahimceni ba ina nufin hanaki aure bane a'a ina son kiyi krt ne,wani haushi naji ya kamani domin a lokacin nayi zaton zai ce min yana sona ne,yanda naga yayi mugun shiga damuwa sannan ya kamani ya wani rungume yana faman ajiyar zuciya tamkar jinjirin daya kwana uku ba tare da ya sha nonon uwarshi ba ina fama da sonshi tamkar na mutu shi kuma ya nan yayi aurenshi sannan ya zo ya wani rungumeni yana min maganar banza nasoma kici kicin kwacewa ya girgiza ni yace come on my sister ki.....kafin ya karasa maganar da zaiyi sai jin salati mukayi akanmu,cikin tsananin tsoro na juya su dayawa daga cikinsu akwai kannanshi da Amarya da Haj Laure uwar Amarya da wasu daga cikin danginsu,duk tsoro ya kamani,Amarya tasa kuka na dubeshi shi kuma ko ajikinshi duban su ma yake yi na tattare zani zan gudu sai naji ya sa hannu ya riko ni.......Masha Allahu Alhamdulillah, mun Kammala littafi na daya Mu hadu a littafi na biyu jinjina agareki HALIMA ABDULLAHI K/MASHI Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 Share DOCUMENT CREATED BY ZAHARADEEN SHOMAR WHATSAPP ,,08168575100 An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 7 of 7