Share this page
5 / 7
hakuri Yaya zan maido maki da dukkan abinda Abdulrahim ya sai ma Iman sannan kuma sai kiyi mashi magana ya daina sata aiki a zauna lfy,na dubi Mama hankalinta a kwance tayi maganar sabanin Haj Yaya wadda ke cika tana batsewa. Dakin yayi shiru sai can a Alhj ya soma magana yace Murja! Haj Yaya tace na'am da karfi tana karkada kafa yace ina son kisan cewa 'ya'yan nan nawa ne kuma wancan ma tawa ce don ni da kaina na daukota ko uwarta bata san zan kawo ta sai dai ta ganmu Allah yasan wannan don haka ba zaki raba min kan 'ya'ya ba kinyi kadan,Habiba yarinya ce a kanki amma tafiki hankali da tunani saboda haka kar ki yarda ki amshi duk wani abu da yayi mata kuma aiki duk wanda yayi niyyar sata kar ya fasa don haka na gama wannan maganar sannan ki gargadi laure ta kiyayeni da wasa naji ta taba Habiba ko Iman sai nasa an daureta gara ma ta tabaki zaifi mata sauki,Haj Maska tace yayi daidai hakan,Murja in ka girma to kasan ka girma don haka sai ta soma kuka tana cewa dama namiji ba dan goyo bane nan na dauki kudina na baka ko basu ne silar arzikin naka ba?daban haka ai da har yanxu kana a fakirin ka dole ka min sakamako da mun wulakanci ta nuna ni tace ke kuma zakiga hukuncin da zan yanke a kanki muddin kika kuma ko kallon min 'ya'yane na durkusa da sauri(don har ta mike)nace don son Annabi(SAW) kiyi hakuri bankade ni tayi waje sauran kishiyoyinta suka take mata baya,Alhj ya bisu kallo sannan yace Allah sarki to Allah ya sa ku gane,ya dubi yayanmu yace kaima kayi hakurin dai zan baka cikin sanyin murya yace Alhj kaimin izinin na koma england jibi,yace na maka amma yaushe zaka dawo?kar kaje ka kuma zama yace nan da wata shida ne yace to Allah ya kaimu ya fita na bishi da kallo. Karya ne gane halin da fuskarshi take ciki wato laifinmu yake gani ko na uwarshi,ban taba ganinshi cikin dogayen kaya ba tunda yazo sai yau boyel ne baki amma kanshi ba hula Alhaji ya dubeni yace Allah yayi maki albarka Iman kiyi koyi da halin mahaifiyarki kinji?na daga kai ya cigaba da cewa muddin kikayi halin uwarki to kin dace,sannan mijin da zaki aura ma yadace,su Abdulrahim da Kabir duk yayyanki ne duk abinda suka saki kiyi,sannan in sun maki kyauta ki amsa kice kin gode nace to Alhj na gode,na mike na fita dakinmu na wuce kai tsaye kan gado na fada raina a cunkushe na rasa me ke daga min hankali son da Kabir yace yana min ko matakin da Haj Yay tace zata dauka a kaina ne?wata zuciyar tace duk ba wannan bane tafy yayanku ce wannan amsar da zuciya ta bani itace sanadiyar tashina zaune saboda tashin hankali da naji ni a ciki na mike ina safa da marwa nace a fili ban so akayi wannan rikicin ba ba zanji dadi ba muddin yayanmu ya tafi kai zanje na bashi hakuri in ya tafi na mutu,da sauri na dauki hijabina na fita falo nan nayi turus ganin mama a falon tace ina kuma zaki?karon farko da na soma yi mata karya nace gidansu Amira tace me xakiyi?nace takalmina da gyalena dauko tace ko bari zata aiko maki ko ki aika Jamila kar ki fita ko ina ynxu zo nan kiji,na isa gunta na zauna tace kin dai ga abinda ya faru ko?nace eh tace to ina son kiyi taka tsan tsan da kowa a gidan nan banda yawan shigewa duk wanda ya saki aiki to kiyi masa kamar yadda kikaji Alhaji yace maki,nace to ta kuma duba na tace yanaga kinyi wani sukuku dake?nace bani son tashin hankali ne mama shiyasa tace kar ki damu aikin shedan ne kuma ki cigaba da addua sannan daga ynxu zan na tashin ki duk dare in tashi yin nafila sannan zaki dinga yin azumin litinin da alhamis,sai mu dinga tare in kuma an gama bikin nan zanje wurin kawunki na samo mana addu'o'i na tsari mu dukufa,Allah ya ja mana gaba,sauran maganganun da mama takeyi duk banji su ba ina ta tunanin yanda zan ga yayanmu don nasan nice na jawo wannan tashin hankalin gaisuwar da naji mama ta na amsawa shine yasa na juyo Mami ce ta dubeni tace ya dai?na mike muka shiga dakinmu kan gado muka zube na dube ta nace ya dai tace ina gidan walima muna shirya guri sai ga Sa'a wai ana fada da mamanku da su Haj Laure har sunce sai sun zane ku?nayi tsaki nace kan fa kaya ne kin gansu nan jikina yayanmu ya bani ashe irin na Anty mimi ne shi kenan sai tashin hankali gashi yanzu ma yace zai koma jibi,Mami tace ai dama bayan biki da kwana biyu yace zai koma nace to ai gashi ba'a gama bikin ba ni gani nake ma duk laifina ne hawaye suka zubo mani akan kumatu Mami ta tsaya kallona baki bude shi ne harda kuka?kuma ma ina wani laifinki anan? nace nasa kayan tace to baya baki don kisa bane?shi yayanmu in zai ma mutum kyauta ba ruwanshi da wani nuna bambanci nace rakani na bashi hakuri,Mami tace tab ai sai dai kije ke kadai yayanmu ba ya son ai ta faman bashi hakuri musamman in yana cikin tashin hankali gara makin zauna,ke menene naki na damuwa? kina ganin zaki iya hana shi ya tafi ne?nace bani na ja komai ba,tace sannunki da kai ta mike zo muje gidan walima nace ni kaina ma ciwo yake bazan sami zuwa ba ta tafi na koma na kwanta na cigaba da kuka rurus,saidai za'a a tsira ni ko da bindigane ba zan ce ga abinda nake ma kuka ba sai da nayi ya ishe ni sannan ciwon kai ya yomin sallama kafin wayewar gari nayi rigif ko sallar asuba kasa yi nayi sai wurin bakwai na safe yinin ranar nan haka nayi shi, misalin karfe uku Alhj ya shirya da Yaya Abdulrahim yace Habiba danku zai wuce fa,kan Mama tayi magana shima Yayan namu ya shigo ban san lokacin da na mike ba ya zauna a kan kujera yana gaida mama bayan ta amsa sannan ta ce ikon Allah tafiyar ta tashi ne Abdulrahim?na dauka gobe ne?yace eh gobe ne zanje lagos ne na kwana shida na safe jirginmu zai tashi yanzu ma jirgin karfe biyar zanbi zuwa lagos din yana magana niko bakinshi nake kallo da sauraron muryarshi mai dadi tamkar ba namiji ba ne yake magana ba Mama da Alhj suka shiga dakinta ya bisu da kallo sannan ya juyo ya dubeni na dukar da kai gabana sai faduwa yake yi,ga mamakina naji yace Amina nayi sauri na dago kai baki bude ina dubanahi shima ya kafa min idanu na sunkuyar da kai don ba zan iya cigaba da kallon kwayar idonshi ba sai ina ganin wani abu yana fitowa daga idon shi,yana shigowa nawa,murya kasa kasa yace zan tafi kiyi mani addua kaina a kasa nace adawo lfy Allah ya bada sa'a,a lebanshi naga ya amsa,Alhj ne ya fara fitowa yana cewa Abdul walarka nace Mam zata baka?yace no Maman Sagir kar ki damu ba sai kin bani komai ba Mama ta fito da dambun nama dayawa tace to ka tafi da dambun naman nan Iman tayishi shekaran jiya ya dubeni sannan yace to zan amshi wannan sai naji wani sanyi a raina suka fita nima na daga labulen dakinmu ina kallo ga yan biki nan sai a dawo lfy suke mashi harda su Haj Yaya dasu mama aka fita harabar gidan wajen ajiye motoci nima na fito ina daga can baya ina kallonsa har aka shigar mashi da jakunkunan shi cikin boot din motarshi yaya Kabir ne zai jashi,ga wasu abokanshi suma zasu shiga wata motar ya fito daga dakinshi har ya sauya kayansa da jc jajaye masu ratsin fari dogon wando da riga mai dogon hannu sai takalmin kwallo Anty Mimi ma ta fito sai kuka takeyi haushinta ya kamani a ganina nice yafi dacewa inyi kuka ba ita ba ko mai yasa oho zai shiga mota kenan ya hango ni sai naga ya tsaya yana kallona har Anty Mimi ma ta juyo taga wa yake kallo?sai taga ni yake kallo sai naga ta kawar da kai niko sai na kwantar da kaina a jikin bango sannan na daga mashi hannu alamr bye bye sai ya shige mota suka tafi Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 Tun daga wannan rana ban kuma wani sukuni ko walwala ba har mamakin kaina nakeyi kullum cikin damuwa bana wani cin abincin kirki gashi kowa ya gane halin da nake ciki a gida da makaranta sai dai kowa ya tambayeni sai nace bani da lfy ne.Azumi da nafilflii kullum cikinsu nake ,ranar da yayanmu yayi kwana biyar da tafy Mama taga abin ya isheta bani magana sosai koda yaushe a kwance ga jarabawa ta matso amma bana wani krt sati da lahdi suka zo suka wuce amma banje islamiya ba wato (sanawiyya),Ranar monday mama tace kar naje makaranta na shirya muje Asibiti nace lfy ta kalau tace na dai shirya muje kawai rimi clinic mukaje mama tayi ma likita bayanin yanda nakeyi,likita ta barshi dani bayan fitar mama sai likita ya dubeni yace sanar dani yadda kikeji sai nace kasala nikeji sai kirjina da ke min nauyi kuma bani son yawan surutu yadan gwaggwadani sannan yace kina yawan tunani ko?nace eh yace to tunanin me kikeyi?nace ba komai yace karya ne da na rasa ta cewa sai na ce jarabawa ce nake tunani ba dan ya yarda ba yace to shi kenan ki daina yawan tunani kisa Allah a gaba ya rubuta mana magunguna muka tafi,haka nayi ta shan magunguna amma tamkar ana zugani Mama ta koma na gargajiya ni dai nawa shane a haka jarabawa ta same ni mukayi ta nidai ban sa rai da zanci ba ranar da muka gama ne a nata murna masu hoto nayi,niko sai kallon mutane nake,Mami ta dafa ni tace ga wata yar ajinku can tana nemanki nace ina take?ta nuna min ita ashe Hauwa'u Aminu ce nan tamin korafin rashin sanin gidanmu ita kuma ta bani no wayarta ni kuma nace mata in na fara anfani da tawa sai taga tawa lambar,sai da zamu bar harabar makarantar ne sannan naji duk kewar makarantar ta ka mani.Abdulrahim zaune a kan kujera a cikin falon Hotel din da yayi masauki, ko nace nan ne dama club dinsu suka kama mashi tun farko,kanshi yana jingine a bayan kujera, tebur ne dan karami cike da kayan ciye ciye da shaye shaye amma sam ya kasa cin komai tunanin yakeyi wayarshi tayi kara ya juyo ya dube ta kamar kar ya dauka sai kuma ya dauka Mimi ce ta kirashi bai san dalili ba sai yaji wani kunci a ranshi amma sai ya daure ya dauka,tace yayanmu kana lfy?yace lfy kalau,yake dinfa?tace ina nan lfy dama naga tunda ka tafi baka kira ba ne,yau kwana shida kenan?yace ban sami dama bane,tace to ina jiran kiranka,yace to kawai ya kashe wayar juyawa yayi ya dubi abincinshi kusan minti arbain kenan da kawo abincin amma ya kasa ci ya kai hannu ya bude plate din abincin da yafi so yayi order amma sam sai yaji kamshin abincin ma baya mishi dadi kokadan a fili yayi magana yace yarinyar nan ta bata ni da kalolin abincinta masu dadi,yayi shiru yana tunani tun zuwan shi kasar nan bai wani ci abinci ba daga ruwan lipton sai dambun naman nan,kwankwasa kofar akayi ya bada izinin a shigo ne abokinshi ne shima dan kwallo ne amma shi bature ne ya dubi Abdulrahim sannan yace cikin turanci Maska naga baka shirya ba ne,wannan karon baka so dawowa ba ne tunda ka dawo sam baka da kuzari,me yasa?Abdulrahim ya mike yana fadin tunanin gida nakeyi ya shige dakin barcinsa shima ya shiryo cikin JC na training suka fita.A daran daya cika kwana bakwai da zuwa yana zaune a harabar Hotel din haske ne ya kewaye gurin kamar rana gabanshi gwangwanin coke ne da dan karamin plate cike da dambun nama sannan ya kai hannu ya dauki wayarshi ya soma sana'ar wato danne danne wayarshi can yayi tsaki ya kashe wayar ya mike,da ya kamata ya nufi gurin abokanshi ne tunda ba dare ne yayi sosai ba kuma yasan zasu sa ran zuwansa, amma sam sai yaji ba zai iya ba saboda wani abu da ya taba zuciyasa sama ya nufa dakinshi ya zauna a bakin gado sannan ya aje tarkaccen hannunsa a kasa wayarshi ya rike sannan ya soma sarrafata cikin kwarewa, Babanshi ya kira bayan ya dauka sai yace Alhj ina yini?bayan sun gaisa sai yake cema Alhj dama ya kira ne dan ya amshi lambar wayan Maman sagir domin yana da lambar kowa a gidan itace bai da ita,Alhj yace gata nan ma Habibar ku gaisa,bayan sun gaisa ne sannan ya bukaci lambarta ba tare da wani tunani ba ta bashi,ya jima yana tunanin dalilin karbar no kafin daga karshe ya gane sai dai wani tunaninshi abin zai zamar mashi abin kunya da nunawa cikin abokai,muddin suka san halin da yake ciki,nan a dalilin wata kankanuwar yarinya wacce da yayi auren wuri tabbas zai haifi kamarta.Kwance yake akan gadonshi amma sai sautin daddadar muryar yarinyar yake dawo mashi ya tuno ranar da bashi da lfy duk gidan ba wanda ya kula dashi tamkar ita muryarta ya tuna sannu yayanmu za ai maka wani abu ne?ya sake tuno yanda ya kara tsorata ta ranar da ta daukan mashi kujera tabbas in tana cikin tsoro tana matukar burgeshi yayi magana a fili inda yace nayi missing din ganin tsoranki. (Lallai Iman kinga takanki, mudai daganan sai muce! Allah yakyauta) Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 Ya cigaba da juyi a kan gado ba komai ke dawainiya dashi ba sai begen yarinyar da yake gani abin kunya ne ace ya sota ya tuna da mimi yarinya mai kyau jinin larabawa sai dai shi baya jinta a ranshi yanda yake jin wannan yar mitsilar yarinyar zai auri Mimi ne kawai don bin umarnin mahaifiyarshi kuma ya san duk inda suka shiga ba zai ji kunyar nunata ba a matsayin matarshi shekarunta ashirin da biyar shi kanshi shekara biyar ya bata bugu da kari gashi ta soma zurfi a karatunta,amma in yace wannan yarinyar zai aurà shima yasan rigima zai jawo,yanda mahaifiyarshi ta tsane su wata zuciyar ta ce mashi ga yaran nan da rashin kunya tana jin kace kana sonta to raini ya shiga tsakaninku gara ma Mimi hadaku akayi kuma kasan ta mutu kanka don haka baza ta maka wani rawar kai ba,"A dawo lfy Allah ya bada sa'a" ya kuma tuno muryata da yaji na karshe sannan lokacin da ta rakube a jikin bango tana mashi bye bye ya dawo mishi tausayinta yaji lokacin kuma jikinshi na bashi kamar itama tana jin yanda yake ji a ranta,zaune ya mike yana magana shi kadai tamkar wanda ya tabu yana fadin Amina kiyi hakuri bani da shà'awar auran mata biyu ki bari in runtsa ya kuma fadawa kan gado.Niko yanzu na zama kurma bana magana sosai ban kuma cika son magana ba sai dai maganar su Amira ce ke damuna da suka ce wai ina ciki mayen soyayya na dai ki sanar dasu wanda nake so,inko har zancensu gsky ne to na debo da zafi don ko in har yanda zuciyata ke mani game da yayanmu so ne to ko shakka babu gara na rufa ma kaina asiri nayi shiru da bakina don nasan ko yaji ubana zaici don nasan ni ba ajinshi bace,me kamar Anty Mimi? Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 kammala karatuna shi ya ba samari damar damuna tamakar anbi su an gaya musu musamman ma yaya Kabir shine yasani wannan ya sani wancan,su yaya ma suna zuwa,ban manta wata rana yaya Kabir ya aiko Sagir dinmu ya kirani na fito na sameshi a daki kan kujera na zauna fuskata na kallon wani katon hoton yayanmu sanye yake da JC kore da fari irin na yan wasan Nigeria hannunshi a kan kirjinshi daga gani lokacin suna taken Nigeria ne aka dauke shi,muka gaisa da yaya Kabir ya soma yi min zancen soyayya niko hankalina ba ya tare dashi, yayanmu kawai nake kallo da kyaun da Allah yayi mashi ba abinda ya birgeni irin shedar sallah daya fito mishi a saman goshinshi yayi baki tamkar ya diga ina cikin wannan tunanin ne naji yaya Kabir na min magana da karfi nayi ajiyar zuciya sannan na dube shi nace ka gama?zan shiga gida yace na tambayeki baki bani amsa ba nace ni ban wani jika ba na mike nayi waje yana kirana na fito kirana naji anyi daga bakin gate ko ban juya ba nasan yaya Abubakr ne dogon tsaki naja sannan naje ina zuwa na hau shi da masifa shima kallona naga ya tsaya yi,ina cewa nace ni ba aure zanyi ba amma kun dameni don Allah ku rabu dani ko dole ne?na juyo abina wani abin haushi ina shiga falonmu sai ga yaya Suleiman zaune suna hira da Mama...(hhhhhhhhha.yarinya taki tasameki.) dakin kwananmu na wuce nayi kwanciyata naki fitowa ban fi minti goma ba mama ta shigo ta dubeni tace Sulaiman ya dade yana jiranki wai me kika tsaya yi wurin Kabir din?nace ya aike nine bayan na dawo kuma sai na gamu da da yaya Abubkr na cigaba da cewa gsky ni dai mama ki samu su yaya Abubkr kiyi musu magana nifa ba aure zanyi ba su rabu dani mana,mama tace aike ma yan uwanki ne kuma nasan in ki sanar dasu zasu kyaleki sannan suna ganin girmana sosai bazan iya tunkararsu da wannan zancen ba, nace haka fa shekaran jiya yaya Ibrahim yazo wai har yana takama zaije ya samu babana kuma ko ina so ko bani so shi zai bashi ni mama tace to bisimilla ai ga kinan taci gaba da cewa don haka ma ni koda auren ne cikinsu gara Abubakr din nace ni dai dukkansu har yaya Sulaiman din hakuri zaiyi dani dan bana son auren zumuncin nan mama ta fita tana cewa dai gashi can ku gaisa,na dauki hijabina na fito falo fuskata a daure muka gaisa yace to Iman gani dai na kuma dawowa duk da kin sanar dani krt zakiyi shine na yanke shawara ki yarda a daura mana aure ni kuma zan yarje maki kiyi krt har kiga karshen biro nace mu bar zancen nan, ina Nana?yace Nana tana nan jiya aka sa ranarta goron ne ma na kawo ma Mama nace lallai Nana yanxu itama auren zatayi?yace shine mutuncin duk wata 'ya mace nace to Allah yasa alkhair ni zan shiga na kwanta ka gaida min da su baba uwa kace da Nana inna jiran zuwanta, yace amsata fa? ko zaki yi min waya don Mama tace kin soma amfani da wayarki nace jiya na soma sai dai ni bata dameni ba don haka ko lambar ban rike ba in Nana tazo taje maka da lambar yace ai bazaki min ko flashn bane tunda kinsan tawa nace to na maka na shige daki ina jinshi yana fadin barakiya? Sannu a hankali zuciya da gangar jiki suka tsananta da so kauna da kuma begen wanda bazasu samu ba sannan ni naki yarda da cewa sonshi nake ban yarda da nayi nutso a kogin sayayya ba sai da na samu kaina da rashin barci,sannan na kama karatun littatafai na soyayya,kallace kallace da basu dameni ba yanzun nakan zauna nayi duk saurayin da aka nuno sai naga bai kai yayanmu komai ba ni fa gani nake ba wani namiji wanda ya amsa sunan namiji in ba yayanmu ba,yauma kwance nake akan gado yar karamar Rediyon da nike yin karatu ce na manna a kunnena kaset na wakar fim din kugiya na sa wakar na ratsani Idona a lumshe sai nakejin kamar nice nakeyin wakar, duka naji an dada min da sauri na tashi ganin Amira da Mami shine yasa nayi ajiyar zuciya nace kin dau alhakina Amira ta cire wayar kunnena sai ta dauke Radion ta sa a kunnenta dajin wakar sai naga ta cire da sauri tace Mami ji wannan kaset din Mami ta sa taji sai naga sun dubi juna sukayi dariya nace wai menene?suka zauna suna cewa zancenmu gasky ne nace kamar yaya zancenku gsky ne?Amira ta dauke fuska tace Iman mun gamsu nace me na muku?Mami tace akwai abinda yake damunki amma kin kasa sanar damu,Amira ta amshe damu ne da munhau gaya maki nayi shiru ina tunanin me zan ce masu can dai nace Amira,Mami kunsan yayyena Abubkr,Ibrahim da Sulaiman?suka ce sosai ma kuwa nace dukansu sunce suna sona ni kuma bani son ko daya sannan yaya Kabir shima yace wai sona yake na mike tsaye don girmama maganar da zanyi na cigaba da cewa ni kuma zuciyata da gangar jikina sun nutse a son wanda bai san inayi ba kuma koda ya sani ba zai soni ba don yana da wacce ta fini kyau da ilimi da kuma shekaru,hawaye suka soma zubo min na juyo da sauri na rike kafadun Mami da karfiina cewa ku bani shawara kawayena ku taimaka min da maganin da zan daina sonshi don kukan ku da zaku san ko wanene da kunce lallai zuciyata tayi wauta,suka kamani suka zaunar dani tsakiyarsu suka yi shiru dakin ya yi tsit daga ajiyar zuciata da nakeyi sai karan fanka can Amira tace a ina yake?kuma yaya sunanshi?nace kuyi hakuri wata rana zan gaya muku don ba anan yake ba Mami tace dakin gaya mana ai da mun san yanda zamu bullowa abin nace no ko zan mutu bazan taba tunkarar wani da namiji da sunansa ba yanzu ku bani shawara yaya zanyi na daina tunaninshi suka yi shiru can Mami tace rokon Allah zakiyi muma zamu taya ki nace sai dai mukara don kullum yi nake amma ba sauki sai dai abinda ya karu nan dai suka lallashe ni gami da bani shawarwari. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 Haka naci gaba da rayuwa cikin kunci,wata safiya misalin karfe takwas Mama tana dakin Alhaji ta kai masa abin kari ni kuma ina ta faman gyaran dakinmu na gama na koma dakin Mama ina cikin aiki naji wayar Mama tana ringin na dauka sai ga lambobin rakwacam na dauka nace Assalamu alaikum sai naji ance Wa'alaikummussalam,jin muryar da ta amsa nan da nan na gane yayanmu ne farin ciki da na ji baya misaltuwa ina wannan tunanin ne naji yace Naman Sagir ina yini? nace ba ita bace ni ce Mama tana dakin Alhaji yace ok! nace ina kwana?yace lafiya amma mu nan rana ce kuna lfy?nace lfy lau yace to kice da Maman Sagir ina gaishe ta dama don mu gaisa ne na kira kafin nace to har ya kashe ranar nayi walwala har yamma don jin muryar abin sona. Share DOCUMENT CREATED BY ZAHARADDEEN SHOMAR WHATSAPP 08168575100 Tawa Tasameni1-04 Posted by ANaM Dorayi on 10:13 PM, 30-Dec-15 __________ NA HALIMA ABDULLAHI K/MASHI__ Lokacin da zai tfy nan ko ince da zaya koma ina cikin wannan tunani sai naji yace kin gama?dama na gama sai nace e yace to gashi na isa na dan rage tsawo yace wannan ya turo mani akwati naki ne sannan daya kuma zaki kaima Mimi nata nace to nagode Allah ya kara daukaka duk da bai amsa ba nasan yaji dadin adduar,na dau akwatin nayi cikin gida Allah yasa ba kowa a tsakar gidan ni da mama muka bude muna ganin kaya nayi mamakin kayan domin suna da yawa bayan haka kuma zasuyi tsada english ne kala bakwai sai jakunkuna da takalma sai rigunan barci masu kyau sai wani zobe cikin akwatinsa mai kyallin gaske,na dauka ina dubawa zobe ne na zinari mai nauyi akwai stone mai kalar ruwa gargar tamkar kankara in ka kura ma stone din ido zaka ga an rubuta A guda biyu daya kan daya nace la mama duba ki gani harda farkon sunana tace kin gode sai dai fa in har irin na 'yan uwanshi ne to ba zaki sa su ba na dan bata rai sannan nace bama iri daya bane na tashi na soma gwadawa duk wanda nasa sai su zauna min tamkar a jikina aka kerasu,da yamma ina zaune a daki ni dai bani son zuwa aiken yayanmu domin na tsani ganin Mimi nasan ma wulankanci zasu min Sagir ne yace yayanmu na kirana dama a shirye nake ina son inga ko ya manta ne in share in ya tambayeni daga baya sai nace na manta ne nima haka na tashi na tafi dakin mama na sanar da ita tace sai na dawo,su hudu na samu na gaishesu suka amsa dayan cikinsu yace Maska wannan ma sister ka ce?yace ban sani ba ya wani daka min tsawa yace shiga ciki ki dauko jaka adidas kizo ki wuce kin wani tsaya kina kallon mutane na shige dakinbarcinshi da sauri ya juya gun abokanshi yana ce mishi dj bana son aboida kuke min baku san yaran nan da raini ba sai taga kamar sa'aninta ne mu wani yace to Nasir fa da zai auri Mami kanwarka?yayanmu yace ai yaga zai iya ne sannan nace mishi kar ya yarda ya kawo min karanta raina shi ga manyan babys a gari yazo zai nace gun wadannan yaran,jikina yayi sanyi na sabi jaka na fito ya dubeni yace kikai mata saura ki dade na fito ba tare da ya bani kudin mashin ba, gidansu Amira na shiga bayan mun gaisa da mamansu tace min tana cikin dakinta na shiga tace daga ina haka?nace ina zani zaki ce ta ce to sai ina?na zauna bakin gado na ajiye jakar a kasa na dubeta na nace don Allah zaki raka ni?tace ina? nace malali gidansu Anty Mimi tace to jeki ki gaya ma mamanmu sai na shirya kafin ki dawo nace to amma fa kece zaki biya mana kudin mashin tace wane irin ni zan biya nace to bai bani kudin mashin ba gashi har yana cewa inyi sauri ni kuma ban fito da ko sisi ba na fito gun mamansu na sanar da ita tace sai mun dawo muka fito muka hau mashin sai malali Yanda na zata hakan ce ta faru domin da Mamnsu wato Haj Laure ta ganmu haka ta hau zaginmu wai mu juya da kayan ba'a so inshi ba zai kawo ba to ya bari,Anty Mimin itace ta hana tace mu kawo Amira tace ki barshi mana sai mu maida Anty Mimi

Chapter 5 of 7